NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 21 of 69

…..” “Feerah!” Mama takirata cikin kakkausan murya dayasa Safeerah tai shiru bata karasa maganan ba, Mama tadan gyara magana tace “yaran yanzu basu iya magana ba wani shirme kike gaya haka Safeerah”? Kada kafa Momma tayi tana kallon Mama tace “ke Amina nizaki gwadama makirci? Ohhh wato ke kin kasa gayamin a fuskana aiki yamiki yawa sai ki turomin yarki” dasauri Safeerah tace “Momma wlh bahak…….” Hannu Momma tadaga mata sama sannan takalli Mama tace “na ciyar da mijinki na ciyar dake, na ciyar da yarku na ciyar da jikanku, nine tufafinku, abin shanku, kunzgunku, abincin jikanku, nine makarantan diyarku private university, kin dauka ina kashe uban kudin nan zan bar masu aiki agidan nan ne? Menene amfaninku? Shu’aibu kanina ne jini daya kuma, da babuni da ina zaku? Sabida na rufamuku asiri namuku rumfa da sutura eh shine zaki bama yarki sako aiki yamiki yawa?” Ahankali Mama tace “kiyakuri Mama Kubra kuskure ne kawai da shirmen yara yasa Safeera…..” “Shu’ibu! Shu’aibu!” Momma tashiga kiran Baba ranta abace kaman daman jira take daga tsakar gida ya amsa yashigo gidan da gudu hannuwansa duk kumfa yana tsiyaya anan falon Momma tamai wani kallon banza da takaici tace “shashasha bakasan zaka goge hannu kafin kashigo min falo ba” runtse idanu Safeerah tayi zuciyanta namata daci yanda ake zagin mata iyaye agabanta, Baba dasauri yashiga goge hannuwansa ariga yace “yakuri Mama Kubra, gani kin kirani” cikin fushi tace “Matarka Aminatu tayomin aike da yarku yanzu take sanar dani wai aiki yama uwarta yawa” dasauri Baba yace “Subhanallahi wani irin magana ne haka nakeji Aminatu, Safeerah” Mama zatai magana Momma ta dakamata tsawa tace “lemme finish”Mama tai shiru, Momma tace “dan haka ka tattara matarka da yarka da jikanku kubarmin gidana yanzun nan” faduwa gabansu yayi dasauri Safeerah takalleta tace “Momma dan Allah kiyakuri” Mama tace “Mama Kubra dan Allah kiyi hakuri wlh aiki baimin yawa ba” Baba ya zube yana hada hannu yace “Mama Kubra wanake dashi banda ke? Ina kikeso naje? Taya zan fara? Ga makanta? Bara kikeso naje nayi” cikeda rashin mutunci tace “sai me toh akanka aka fara baran, sabida na rufamuku asiri sai ahaumin aike, mara mutunci kawai butulu daku marasa godiyan Allah matsalan talakawa kenan kamusu dare su maka rana” lumshe idanu Safeerah tayi hawaye na zubomata this is the reason why she never talks take hadiye komi, cus everything she says affect parents nata more, they are being humiliated, abune ya tsayamata a kirji ganin yanda suke begging Momma tana duramusu zagi baki tabude zatai magana kawai sai zuciyanta ya karaya ta fashe da kuka sosai tace “Momma dan Allah kiyakuri, wlh wlh Mama bata aikoni komiba, baki fahimci maganata bane dan girman Allah kiyakuri” Ijiyan zuciya Momma ta sauke tana kada kafafu tace “okay zan salllami masu gadina! Shu’aibu ka tattara matarka da yarka ku koma dakin masu gadi dake gate dagayau kaine zaka dinga bude gate tunda na kore ka bawai kanada wajen zuwa bane” dasauri Baba yace “naji na yarda” zuciyan Safeerah ya mugun sosu, bude kofan sama akayi Salma tafito dawani mahaukacin kayan bacci ganin su Mama duke gaban Momma a falo yasa ta harari Safeerah tace “yarinya sai mugun hali kuma saidai aiki ya kashe Uwarki da Ubanki yanzu suka fara, yazama gateman your mother kuma our cook and maid die da bakin ciki, in kinyi zuciya ke nemo naki kudin kawai an dawo gidanmu ana cinye mana kudin gadon da Baban mu ya barmana, kai Baffa dalla tashi kafita” tashi Baba yayi ahankali yajuya yawuce idanun Safeerah suka kada sukai ja. EPISODE 1️⃣1️⃣ Momma itama ta dakama Mama tsawa tashi kibar nan kekuma wuce kije ki shirya kafin nasa Shamsu ya tattakamin ke” da gudu Safeerah tayi kofa Salma tabita da kallo saikuma tazo wajen Momma tazauna tace “Wlh Momma I hate Safeerah, I hate her ta uban Yaya ma tafini kyau”?Dasauri Momma tajawota jikinta Salma ta kankameta ashagwabe, Momma tace “wat are you saying Salma? Yarinya fara kal dake inake ina hada kanki da black skin Safeerah haba haba, ai sama taiwa yaro nisa saidai yadaga fuska ya kalleta” shafa gashinta Salma tayi tace “Momma harda gashi tafini fa” dasauri Momma tace “Kin fita keda kesa relaxer jibi gashinki common stop the comparison kina ragema kanki daraja ne, the kind money kike spending on your body why will you compare kanki damai shafa alayyadi”? Turo baki Salma tayi ta bala’in jin dadin maganan mamarta tai blushing ta gyara zaman kanta a cinyan Momma tace “you’re the world best Momma”. Dakinsu Safeerah tabude kofa ta shiga idanunta sunyi jaa, waje tasamu akujera ta zauna hawaye na saukowa daga idanunta tana gogewa da bayan hannu, ita kadai tasan metakeji azuciyanta, itafa da ace ita suke zagi, suke ciwa mutunci, suka maida jaka wlh bazata damuwa as long as iyayenta nada martabansu da kimansu, mesa Momma da yaranta this small Salma ke zagin mahaifinta da mahaifiyarta? Why? Wlh kawai tausayin s
🏠