a?” Gyadamai kai yayi alamun eh batare dayayi magana ba, Baffa yace “sannu da zuwa Salim, Ya shirin bikin” anatse yace “Alhamdulillah Baffa” Ammi tace “zokaci abinci” ahankali yace “okay” saiya wuce dinning dasauri Auwal yabisa Dady yadan sauke jaridan kasa yabisa da kallo kafin ya kadakai yasake bude jaridan yana dubawa, Auwal yace “Yaya akwai kanwar wata Abokina Shamsu dazatayi IT a company mu, I know kace no yan IT but please Yaya kaga nariga nacemai yes” dan kallonsa Salim yayi fuskan nan tasa ba walwala, Ammi dake zubamai abinci tace “tundazu yaketa nanata maganan nan Son, I told him daya sanar dakai kafin ya yarda but tunda kanwar Abokinsa ce ka yarda please na san Shamsu yana zuwa gidan nan he’s a nice boy kaji Son” ta shafa kansa, sauke jaridan Dady yayi yajuyo yakallisu yace “kazo company na kayi aiki ka makale ana yayanka gashinan kullum cikin roko kake kaman me bara” dukansu kallon Dady sukayi hatta Ammi bataji dadin maganan ba Baffa zaiyi magana Auwal ya jirasa yace “common Dad sau nawa zan gayamaka company Yaya is my dream, I studied architecture a school, mexanyi in your company when my brother open my dream company and gives me to manage” yayi maganan yana murmushi yana kallon Yayansa dake juya spoon, magana Daddy zaiyi Baffa yace “kafi kowa kewan yaron nan dabaya gari yanzu yadawo zaka fara” shiru Dad yayi bai kara magana ba.
Kansa Ammi ta shafa hakan yasa yadago yakalleta murmushi ya sakan mata kadan yadan lumshe idanu yabude sai yaja bowl of soup din gabansa yasaka spoon ciki yadeba zaikai baki saiya kallesu ganin duk shi suke kallo da Ammi da Auwal yasa yace “is there something in the food”? Kwashewa da dariya Auwal yayi yace “wlh Ya Salim baka iya cracking jokes ba badadi kai sojoji babu abinda kuka iya”, murmushi Ammi tayi tace “ci abincin ka mun dena kallonka” taja kujera ta zauna kusa dashi, kaiwa bakinsa yayi anatse yaci sannan yakalli Auwal yace “she can start” dunkule hannu Auwal yayi cikeda jin dadi yace “yesssss!” Ammi tai murmushi tace “thank you Salim” gyadamata kai yayi cikin muryansa kasa kasa yace “tell him within the week zanzo for supervision idan naga anything ba daidai ba I will fire both him and Paresh and nobody will use you to beg me Ammi! It won’t work” Ammi takalli Auwal dake dariya tace “kadaijiko”? Dasauri yace “I manage everything to perfection bazaka ga komi ba sai alkhairi Yaya, wannan uban salary da kake biyaba how can I joke da wajen cin abinci na” dan hararansa kadan Salim yayi yace “silly boy” shiru yamusu bai kara tankasu ba yacigaba da cin abinci while Ammi da Auwal na hira, Dady da Baffa na nasu a falo, bai wani ci sosai ba yadauki mug na coffee yamike baice musu komiba ya wuce stairs yashiga hawa Ammi tabisa da kallo, anatse yake tafiya kaman yana inspecting ko’ina dakin dake gaban na Ammi yawuce hannunsa yadaga yayi knocking so daya dudda kannensa ne baya taba fadawa dakinsu kai tsaye he respect privacy nasu, bude kofan akayi autansu ce Lubna batai wata wata ba kawai ta rungumesa tana washe baki dan tana bala’in son yayanta tace “Yaya kadawo? Oyoyooo” Ameerah da kanta ke a tsefe gashin kam acinye tazo itama tana murmushi akunyace gabanta na faduwa tayi hugging nasa tace “Yaya sannu dazuwa, Yaya kaga gashina duk yakarene saisa nasaka” Calmly yet strictly yace “is that ur excuse na yin abinda Allah yahana”? Dasauri ta girgizamai kai, anatse yace “Allah ya tsinema mai karin gashi, get ready I will take you to supermarket gobe to get the best hair products that helps with hair growth” gyadamai kai tayi tana murmushi tace “thank you Ya Salim”suna mugun tsoron sa but again kuma suna mugun sonsa, he’s just the best and very sweet but you need to be open minded before ka fahimce sa inba hakaba zaka dauka ya tsaneka ne, kusan 1min suna ahaka yace “ku cikani” dariya dukansu sukayi suka sakeshi wucesu yayi yashigo dakin Lubna ta kulle kofa duk suka biyosa bai zauna kan gadonsu ba saiya wuce gaban dressing mirror nasu ya zauna yayi crossing leg yanashan shayin ahankali yanabin ko’ina da kallo kaman wani invigilator this is just him haka yake, akwai observing environment nasa, he’s very very security conscious, gadaje biyu ne a dakin daya na kallon daya ga bra da pants akan gadon Lubna kallo daya yamusu yadauke kai yace “wat are those underwears doing saman gadonki Lubna?” Dasauri tayi wajen ta kwashe komi tawuce wardrobe nasu tabude tana sawa ciki tace “Yaya sunmin kadan ne Ammi tace nahada nafito dasu” wayansa ne yahau ringing da sauri Ameerah tazo wajen tace “Yaya Anty Nanah ne?” Kallonta yayi saiyasa hannu yaciro wayan ga sunan Nanah a screen din dasauri Ameerah tace “can I talk to her Yaya?” Dasauri itama Lubna tace “Yaya nima I want to talk to her” wayan yaba Ameerah yamike yace “idan kun gama ina wajen Ammi” yawuce yafice daga dakin yashiga dakin Ammi, Ammi na zaune saman gado hannunta rike da wata yar takarda yawuce ya