im yawuce ciki ya barsa a dinning.
***
Takai kusan awa daya zaune kan kujeran canteen din ita kadai babu komi agabanta banda jakan school normal bag pack black sai wata allo haka na board mai dan girma jingine da jakan, tana sanye da dogon rigan abaya black ta yana kanta da gyalen fuskanta babu komi akai but caramel skin dinta is glowing dazaka dauka tana skincare ne, fatar fuskan sai sheki take asalin defination na glass skin, gashin goshinta akwance sosai yayi wani mahaukacin kyau kaman buzuwa, lips dinta pink din dasukadan taso kaman ta turosu kanta akasa tana wasa da kyawawan fararen kunbanta dan ranta abace yake wlh sosai, sake dago kanta tayi ta kalli wani table da wasu yammata su uku ke kai ga abinci daban daban agabansu da drinks irin na yan gayun nan sunasha suna hira, kuka sosai cikinta yayi na yunwa tun tea datasha da safe da bread gashi this is almost to 5 na yamma, tun 2 suka gama lectures amman har yanzu basu tafiba tana jiran Salma, yadade a Cafeteria dayake aiki yake a system kawai sallan la’asar ne yadagasa yana lurada sanda yarinyar ta tashi taje tayi salla tadawo, akan idanunsa suka shigo sunyi order komi ita basu mata ba, maida laptop nasa yayi cikin jakan sai yaje yasayo jellof rice da chicken da juice da kansa yadauka a tray yashiga tahowa table da take kai, daya daga cikin yammatan dake hiran fara tabisa da kallo, karasowa table nata yayi yasauke tray cike da fara’a yace “Assalam” dago kanta tayi ahankali manyan idanunta suka sauka akansa ganin mutun ya ijiye mata abinci agaba yana mata wani murmushi mai kayatarwa yace “my name is Aziz I bought you lunc……..” “toh Malam bazawara ce harda d’a!” Sukaji muryan mace akansu da sauri suka juyo harda ragowan mutanen dake cafeteria ma saida suka jujjuyo, wannan faran budurwan ne bazata wuce 22yrs ba but kana ganin kalan kayan dake jikinta kasan yar gidan masu kudi ce sosai, sauran yammatan guda biyu suka bushe dawani dariyan keta, ahankali ta maida kanta kasa, cikeda rashin kunya tana kallon fuskan mutumin tace “stop looking at me I’m just saving you ne, just 6month tayi agidan miji ya korota da ciki tanada yaro dan 3yrs u know looks can be deceptive! I’m sure a young guy like you won’t settle for yar mai wankin motan gidanmu” sauran yammatan suka kara kwashewa da dariya, wani kunya ne yakamata idanunta suka cicciko da hawaye sosai dawani irin sauri ta tashi tadauki jakanta da board nata da gudu tai kofa duk aka bita da kallo hartasaka hannu zata bude kofa yarinyar tace “wa kika barma jakana ya daukarmin?” Daidai lokacin hawaye yasake sauka a idanunta bayan hannu takai ta share saita dawo anatse kanta akasa tazo inda suke tsaye takai hannunta ta karbi jakanta, ita mai maganan tama guy din daketa kallonta fari cikin iyayi tace “My name is Salma my friends call me…..” atare yammatan sukace “Sams” Salma cikin iyayi tace “and you’re welcome cus I just saved you from a disaster let’s go girls” tawuce abinta tayi gaba yammatan na binta anatse itama tashiga binsu ko ajikinsu is Nile idan da sabo an saba ganin all this Ajeboter kids, this is Abuja fa, wajen parking sukayi kawayenta suka wuce nasu motan ta bude wani Benz na 2024 ta shiga ahankali itama tasa hannu tabude tashiga gaba taja kofan tarufe Salma ta tada motan da mugun gudu sukabar school din.
Tana tuki taja wani tsaki takalli yarinyar dake gefe tace “wai ga university Gwagwalada, gasu FCE, ga polytechnic akanme Momma zata wani saki a Nile fisabilillahi! Ni da ke daya ne? Ganinki tareda ni ma yanasa ajina naraguwa, imagine nike tukakima kaman wata baiwarki, thank God anyi hutu yau Momma saidai ta nemi mai kaiki ni nagama kaiki wlh mtswwww! I hate poor people wlh” takara dannama motan gudu dayasa ta runtse idanunta idan da abunda take tsoro takasa sabawa is mahaukacin mugun gudun mota gashi kullum sai Salma tayishi, kusan 30min suka bata a hanya sannan sukakai cikin GRA wani babban gida sukaje ta danna horn aka bude kofa tundaga nan gate ta hango wani magidanci sanye da wasu kodaddun shadda yana wanke mota, baida kiba ko kadan ga idanunsa dasuke nan ajuye kaman ya makance, but yana gani dasu saidai ba sosai and ba koda yaushe ba, yana ganinsu ya dakata da wanke motan yana murmushi cikeda farin ciki, parking tayi awajen atare suka fito Salma tamai wani kallon banza tace “ka wanke min motan nan Baffa yanzun nan cus zan sake fita, kaciro kayan boot ka kawomin cikin gida kayi sauri nafito baka gamaba ranka zai baci” sosuwa ranta yayi zata kalli Salma mutumin yace “toh yanzun nan zanyi” Salma tawuce abinta mutumin na murmushi sosai yace “Mamana an dawo ya makarantan?” Abu taji ya tsayamata awuya sosai da kyar cikeda kunci tace “bari natayaka aikin Baba” tawuce wajen plastic chair data gani a wajen ta ijiye jakanta da board zata juyo Baba yazo wajen yakama hannunta yace “mezakiyi haka? Maza wuce ciki yau Waleed nata rigima jeki karbesa wajen mahaifiyarki” baki tabude zatai magana Baba yace “wuce ciki nace ayyo ga r