a rungumesa sosai tace “sannu da zuwa Salim, Ya China? Ya hanya”? Anatse yana warware muryansa dudda he’s still sounding strict yace “Alhamdulillah Ammi” sakinsa tayi suka shiga ciki zama yayi kan kujera daidai karaman na fitowa tasaka hula akanta ta kallosa adan tsorace, kallonta yayi da sauri ta sunnar dakai ta taho anatse babu wani girgir tana zuwa tadan duka gabansa tace “Yaya sannu da zuwa ya hanya?” Ahankali yace “fine! Where’s Ameerah”? Ahankali tace “gatanan zuwa” bawasa kan muryansa yace “go and tell her to loose that thing in her head kafin tafito nan” gyadamai kai tayi tace “toh” mahaifiyarsu dake kallonsa tace “dodon gida yadawo kowa saiya kama kansa” takallesa tace “Dadyn kuma gasanan zuwa tashi muje kaci abinci” dan yatsine fuska yayi yace “I want to shower tukunna Ammi” gyadamai kai tayi tace “to jekayi zama kafijin dadin cin abinci” Auwal ya kallesa yace “Yaya ka barmin motan nan please” gyadamai kai yayi yace “daman it’s yours” tashi Auwal yayi cikeda murna zai rungumesa Salim yamai wani kallo hakan yasa ya tsaya yana dariya yace “thank you Big Bro you’re the best” hararansa yayi yawuce duk suka bisa da kallo Ammi na murmushi sosai.
Bude kofa yayi yafice yatafi next flat dake gaban nan yabude yashiga komi a gyare tsaf yana kamshi an kukkunna AC, maida kofan yayi yarufe, da takalmin kafansa yawuce sama yabude wani daki ya shiga yazauna kan gado yana warware igiyan takalmin yacire ya jefar daidai wayansa na ringing, ciro wayan yayi kiran iPhone 16 yakalli screen din ansa Nanah ijiye wayan yayi saman gado yacigaba da ringing yashiga cire dayan takalmin kafansa wayan yashiga ringing akaro na biyu hakan yasa yakai hannu yayi swiping ya katse kiran, yayi dialing number back yasa a speaker yabar wayan agadon shi ya mike yana bude boturan rigansa ringing daya aka daga muryan mace ya bayyana mai zaki tace “Baby I’ve been calling you tun dazu baka daga ba” anatse yana bude boturan rigan yace “ina tare da Auwal ne” dan murmushi mai sauti tayi tace “to ya hanya I’m so happy you’re back, 11months ban ganka ba, Ya program din?” Daidai yakarasa cire rigansa yakalli tabon kunnan dake hannunsa na haggu sai yayi shiruuuuu kawai yana kallon tabon, jin shiru yasa tace “hello Baby are you there”? Jaye idanunsa yayi daga hannun ahankali murya ciki ciki yace “Alhamdulillah” ya ijiye rigan agado yazare farin singlet din jikinsa Ya Allah! Kirjinsa kaman na dan wrestling sabida yanda ya ginu kaman shiya kera kansa ga jijiyoyi a hannunsa a munmurde yake, dan rage murya tayi tace “akwatunana are so fine can’t wait nazama matarka” ba yabo ba fallasa akan fuskansa yace “yau saura kwana nawa?” Dan shiru tayi idan da sabo tasaba da halinsa he does abu kaman baya sonta, wlh kawai sabida Allah ya jarabeta da sonshi ne saisa, ahankali muryanta asanyaye tace “17days” kai tsaye yace “I have to go now i wanna shower, later” bai jira amsanta ba yakai hannu ya katse wayan yazare wando yawuce tafada bayi yajima aciki sannan yafito daure da bathrobe fari mai kyau kawai yahau gado sai bacci yagaji sosai.
Around 4 ya farka ahankali yatashi zaune yadan dafe kansa sannan yamike yashiga bayin wanka yakarayi sannan yafito agurguje ya shiga closet dinsa ya shirya cikin wani soft yadi dark ash color rigan jumper takamasa tsam ajiki hakama hannun ya bayyana muscles nasa sosai da yanda yake a mummurde turare ya fesa yasake wani slippers na Hermes yabude kofa yafice anatse yake saukowa yana tafiya daidai ga hayaniya dayakeji agidan sosai motocin daya gani ya tabbatar an dawo masallacin dake nan kofar gidansu yawuce yayi salla sannan yafito yashigo gidan, yaso yaci abincin Ammi but baison ganin jama’a kawai yawuce yashiga cikin wata uros yaja da gudun gaske yabar gidan barrack yawuce na chan Asokoro yana zuwa aka budemai gate ana gaidasa daga ganin plate number motan ana saramai ko kallonsu baiyiba yawuce chan VIP wings yatafi, kaman estate daban ne shi acikin barrack din sojojin wajen suka budemai gate suna saramai ya shiga yaja mota zuwa wani mahaukacin gida wanda yake number 3 a lane din, yayi parking gaban flat din gidan terrace ne ya kashe motansa yafito yakarasa yasa hannu fingerprint ne yabude yashiga, gidan yahadu Ya Allah kana gani kasan ba’a zama cikinsa sosai sama yawuce wayansa na ringing ganin Marshal yasa yadauki wayan kai tsaye yace “kazo mana da abinci” yayi shiru sai ya zare wayan ya katse yafada dakinsa dayayi kyau shima akwai kura but ba sosai ba rigan jikinsa yacire yasauko yashiga store yafito da wani machine dake mopping kasa da kansa yayi setting up yakai dakin yafara mopping shikuma yayi dusting bed yaciro sheet ya shimfida jin an danna doorbell yasa yasauka kasa yabude kofa wani magidancin mutum ne da akalla zaiyi 42yrs saidai baikaisa tsawo ba murmushi kan fuskansa sosai yana rike da warmer a hannunsa da leda yace “hold this ango bari naje nadauko mana juice” wani mugun kallo yamasa hakan yasa yay