NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 10 of 69

yaja kofa ya tsaya gaban dakin yace “ku rama akaina karku tabamin karaman yarinya, ransu baci yayi suka shiga dukan Baba Safeerah na ihu tana kuka jin yanda ake dukan Baba Mama ma haka, before u know it aka tashi a unguwan, warwas suka sumar da Baba suka sama gidan wuta Safeerah da Mama na daki, sukabar gidan, Safeera da Mama suka bude kofa suka fito suna tari, kamo Baba Mama tayi suka fito dashi waje wuta ci yake sojoji suka iso, karban Baba sukayi suka sa amota Mama da Safeera suka shiga kaisu wani asibiti sukayi suna saukesu suka juya komawa unguwan, aka karbi Baba akace su ijiye dubu dari ko biyar babu ajikinsu ko sun koma gida ma an sama gidan wuta, wayan Baba Mama tacire daga aljihun jallabiyan sa tana kuka, Number Yayar Baba Kubura dake Abuja takira, ta sanar da ita komi dake faruwa, Mama Kubra ranta yabaci tadinga masifa ta tura kudin kawai ta aiko driver yadaukesu, wuraren 6 na safe driver ya iso haka aka cire Baba daga treatment aka sakasa a mota Mama takama hannun Safeerah dake kuka mugun zazzabi ya rufeta suka shiga motan kawai aka wuce dasu Abuja. Bayan 5yrs!!! 💫IT’s NEVER TOO LATE💫 ✍🏻M SHAKUR EPISODE 5️⃣ Bayan 5yrs Tampatsetsen gidane mai lafiyayyen kyau, kalan yan gayu da abubuwan zamani, gidan nada girman gaske irin gidajen nan ne da kana ganinsu kasan sai wane da wane ne keda kalan gida haka, ga securities biyu dake sanye da wasu bakin uniform na wajen gate tsaye kaman gumaka, anata aikace aikace a gidan kaman akwai wani event, masu fenti nayi, masu gyaran flowers nayi, ga motoci dayawa parke a compound din. Wata hamshakiyan mata ce zaune a hadadden parlour dayaji kayan duniya tana sanye dawata shadda dayasha aiki wuyanta da kunnenta duka zinare ne, waya na kunnenta tana magana while wata haka na zaune agabanta tana samata kunshi akafa, sai wasu yammata haka masu kyau su biyu zaune a falon da bazasu wuce 21yrs ba dayan kuma maybe 23-24yrs dukansu suna kama da Maman kagansu farare tass dasu, zare wayan mahaifiyarsu tayi daga kunnenta hakan yasa babban yarinyar tace “Ammi I can’t believe finally Yayan mu is getting married wai har an tafi kai akwatin auren sa yau” dayan karaman tace “I cant wait to see him yaushe zai dawo ne Ammi”? Murmushi matan tayi tace “he said yau” zatai magana wata mata sanye da uniform na Chef tafito daga wani babban kitchen tazo gaban matan tace “everything is ready Madam” gyadamata kai Ammi tayi tace “ok, sannunku da aiki” matan tawuce. Tundaga nesa security ya hango motan sojoji na tahowa bayanta kuma yaga wata arniyan mota 2024 GLK baka kirin taji uban tinted itama tana tahowa, dasauri yabude gate da yanzun nan daman ya rufe, shiga ciki motocin sukayi, parking motocin akayi sojoji guda biyu sanye da uniform dake motocin sojojin suka fito suka kame, bude gaban GLK akayi wani matashine yafito wanda bazai wuce 34yrs ba haka, baki dashi yana sanye da shadda mai ruwan toka ga waya a kunnensa yana magana, bude kofan flat nasu akayi yammatan biyu suka fito karaman tafito da gudu ta taho tanajan crocs nata tasaka batama karasa sakawa ba ta taho dasauri tana ihu. “Ya Auwal ina Yaya Salim”? Awani irin hankali yabude kofa yasauko da kafansa dake cikin wani black hadadden safety boot na sojoji, kafafunsa na cikin wandon sojoji na kaki kafin yakarasa fitowa gabaki dayansa daga motan sojojin suka saramai. “Sir!” Da alamu yamusu da hannu sutafi suka koma mota suka kunna sukabar gidan, dogone sosai yanada dan jiki irin full body nan, he’s very huge, suna kama da mai tukin saidai yafi mai tukin duhu shi and yafisa kyau sosai da girman jiki da budewa da fashewan kirji, dan wani irin baki yakeda shi mai bala’in kyau ga idanu yan kanana kaman yanajin bacci masu dogayen gashin idanu, ga gashin gira kaman yasakama relaxer sabida yanda suke baki sidik suna shinning, yana sanye dawata black glasses a idanunsa da idan ya kalleka dashi sai kaji gabanka ya fadi kallon yammatan yayi hakannan kowaccensu ta tsaya chak cus dukansu babu wacce hula ke kanta and bawai wani gashin kirki ne dasu ba dayan ma kalaba ne akanta takara attachement dayan kuma gashinta tayi parking gashin ja, gimtse dariya Auwal yayi daya gama waya, dukansu yanmatan suka juya sadaf sadaf Auwal yace “Ya Salim sunzo maka oyoyo ne fa I’m sure sun manta ba mayafi kansu” baice ko kalaba yashiga tafiya ko tafiyansa babu wasa aciki, namijin zaki kenan! Auwal yabisa da kallo kiransa da akayi yasa yakalli wayansa yace “kun fara dawowa daga kai akwatin?” Yayi shiru chan yace “okay” ya katse wayan yabi Yayansa kafin yabude kofa aka rigasa dudda akwai kunshi akafanta saida ta tako tazo tabude kofan fuskanta cikeda fara’a tana kallonsa tace “Sojoji na” for the first time yayi dan karamin murmushi baice komi ba, Ammi kawai takai hannu taja bakin glasses din idanunsa tace “haba dan Allah ciremin wannan tabarau dake maidaka wani zalum saikace Boss na Indian film” kyawawan kananun idanunsa masu long eyelash suka bayyana Ammi t
🏠