NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 9 of 44

nan Allah ya haɗa shi da mahaifiyar Fatima wadda ake kira da maimunatu ta kasance haifaffiyar garin zariya ce , sosai ya yaba da hankalinta , bai yi mata magana ya bita gidansu ya tambayi izinin neman aure mahaifinta ya amince , amma ya faɗa masa shi fataucine ya kawo shi zariya , shi haifaffen garin kano ne, ya kuma tambaya akan in ya tashi dawowa, magabatan sa zasu zo nema masa aurenta , a haka suka rabu badan junansu sun so ba , ko da ya fad'awa mahaifinsa yayi murna sosai ya faɗawa matansa amma yayi gargadi mai kyau akan kar wanda ya fitar da zancen, haka kuwa aka yi aka ɓoye maganar har sai da biki ya rage y'an kwanaki, amma Asabe bata da labari. Alhamdulillah lallai rana bata karya sai dai uwar ɗiya taji kunya , domin kuwa a ranar jumaah ne aka daura auren malam Iliya da maimunatu mahaifiyar Fatima , mace mai hakuri da kawaici , mahaifin malam Iliya shi yayi komai na auren. Sai ranar da aka daura auren sannan Asabe taji , ranar ansha bala'i domin kuwa gidansu malam Iliya ta tafi ta dinga yi musu hauka amma ba wanda ya kulata ta k'arashe rashin mutuncin ta tayi gida kamar mahaukaciya, ta koma a ranar , ko da ta koma gidan bai kulata ba ta ƙarasq wulakancinta ta hakura . Dare nayi 'yan kawo amarya suka kawota aka a jiye ta a ɗakinta suka mata fad'a sosai , aka ce a kirawo Asabe domin a musu fada amma ta aika musu sak'onnin zagi ba arziki su ka tattara yanasu yanasu su ka yi waje cike da Allah wadai akan halin Asabe , aka bar amarya a cikin gidan mijinta . Sai muce Allah ya bada zaman lafiya , ya kauda fitinar Asabe amin. Godiya mai tarin yawa a gareku yayata y'ar uwata wato Usaina musa saleh bisa ga gudummawarki gareni Allah ya taimakeki a aikinki ya bada sa'a amin. Godiya a gareku yan moonlight writer's association Allah ya k'ara had'a kawunan mu amin ya taimakemu amin , ina godiya sosai. Please🙏🏻 Share &comments To be continue........ 🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿 🌸🌹Kishiyar Uwa🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ Ina k'ara godiya ga Allah subahanahu wata'ala da ya kara bani damar ci gaba da littafina na kishiyar uwa, kuma ina godewa mahaifana da y'an uwana da suka jajirce wajen ganin na ci gaba da rubutu na , haka ma fan's nawa ina kara godiya. 🥰😍 ina ganin comments kuma inajin dadi sosai wallahi. Sadaukarwa ga duk makaranta littafin nan tare da y'an moonlight writer's association, Allah ya k'ara hada kawunanmu amin y Allah . Shafi na 6️⃣ Aka bar amarya gidan mijinta , da dare yayi sosai abokanan ango suka rakoshi , amma fafur Asabe ta k'ek'asa k'asa ta hanasu shiga gidan, ban yadda suka iya haka suka koma , suka yiwa malam Iliya fatan alkhairi shi ma yayi musu sallama sannan suka tafi , shi kuma ya shiga cikin gida aikuwa yana shiga ta ce da wa Allah ya had'ani in ba dakai ba ta shiga yi masa ruwan bala'i amma yayi mata banza wannan ya k'ara kular da ita sosai , ya juya zai tafi tayi sauri ta rik'e masa wuyan rigarsa ta baya , a fusace ya juyo ya sauke mata wani wawan mari a kuncinta wanda saboda tsabar razana da mamaki sai da ta zube k'asa , ni kuma da nake tsaye ina kallon abinda ke faruwa dariya nayi a hankali saboda kar masifar ta dawo kaina, amma ke ma Asabe in banda tsaurin ido ta yaya zaki rikewa sabon ango wuyan riga ki hanashi shiga d'akin amaryarsa abinda yafi haka ma zaki gani🥴 , saboda duk rashin mutuncinta bata tab'a rik'e masa riga ba da sunan rashin kunya sai yau , tana a zaune kafin ta dawo hayyacinta har ya shige d'akin amaryarsa Maimunatu sai rufe k'ofarsa taji garam aikuwa da sauri ta zabura kafin ta k'arasa har ya sanya sakata , sai dai muce asha amarci lafiya malam Iliya😍. Asabe kuwa kwana tayi tana hauka a tsakar gidan in ta gaji ta zauna in suka motsa mata tayi ta buga musu k'ofa haka ta kwana bata runtsa ba tsabar masifa. Washe gari da safe kuwa suna fitowa suka ganta a zaune a tsakar gidan rana d'aya duk ta lalace , saboda masifar kishi , aikuwa tana ganin sun fito haka ta nufi maimunatu da itace sauri yayi ya kareta tare da watsawa Asabe mari ni kuma abin nema ya samu matar direba ta haifi mota ina kallon ta ina mata gwalo amma bata ganni ba ta juyo kenan b'arina ni kuma na fece🚴🏻‍♀️ a miliyan, a ranar haka ta hanasu sakat a gidan ya zamana ko ina maimunatu zata shiga sai dai malam ya rakata , a haka ta dinga rayuwa har malam ya koma da sana'arsa wato fatauci , aikuwa gida ya zamar mata kamar birsin dam ma iyayen malam da k'annensa suna sonta shi ne abin ya zame mata da sauk'i . A lokacin da suka cika wata biyar da aure Allah ya azurta maimunatu da samun ciki zo kuga murna gurin malam Iliya , rana samun kulawa sosai , tunda Asabe
🏠