NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 8 of 44

mma yaga sab'anin haka, hakan ya sanyashi ya tafi gidansu domin gaida mahaifins. Tana fita Asabe ta yi shirinta tsaf da magungunan da bokq sha yanzu ya bata ta zauna zaman jiran malam ya dawo daga gidansu .............. Please🙏🏻 Share &comments. To be continue........ Luv u all my fan's🥰🥰😍 🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿 🌸🌹Kishiyar Uwa🌹🌸 (True life story). 🍁Daga alk'alamin Nussad🌸 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ Ina matuk'ar godiya gare ku masoyana , saboda nuna kulawarku ga littafina mai suna Kishiyar uwa , a gaskiya na rubuta shi ne badan komai ba sai don tunanin da nayi wannan shi ne abin da yake damun al'umma , idan mata taga an bar mata 'ya'yan abokiyar zamanta idan har basa shiri da ita to fa su ma yaran nata sun Shiga uku , dan Allah mata mu kiyaye wannan hakkin lallai sai Allah ya tambayemu a kanshi , ki sanya a cikin ranki idan da yaranki ake yiwa haka ya ya zakiji a cikin ranki , Allah yasa mu gyara amin. Ina ganin comments naku gaskiya ina jin dadi , kuma ku ma burgeni , insha Allahu bazan baku kunya ba Comments🥰 Maman Ammar Kishiyar uwa🌹💞nicely sis Allah ykara basira ina matukar jin dadinsa wlh 🥰🥰 ~phareeeda Allah sarki Fatima zakisani kuka 😭😭😭😭😭😭😭😭 Duk naga comments ina godiya. Shafi na5️⃣ Ko da malam Iliya ya k'arasa gidansu ya tarar ana ta shirye-shiryen biki , wajen mahaifinsa ya fara zuwa ya gaida shi amsawa yayi kana ya mishi maganar "angama komai da ake buƙata yanzu abinda ake jira shi ne saboda su na so su kai kayan aure da sadaki, saboda auren ya kusa, amsawa yayi da to , kana yayi godiya, ya yi masa sallama ya shiga cikin gidan wajen iyayen sa mata , nan ma ya tarar suna ta shiri sosai , ya gaida su ya mu su alkhairi, ya tsaya sai da su ka ga ma komai na harkar kai kayan auren, da sadaki sannan ya nufi hanyar gidansa. A can gida kuwa Asabe ta gama har had'a komai da tasan boka sha yanzu ya ba ta, dan haka a halin da ake ciki malam Iliya kawai ta ke jira ya dawo gida, tayi wanka da magani ta shafa turaren da sauran kayan amfanin da ya bata za ta sanya masa a abinci. Da sallama ya shiga a bakin sa , amsawa tayi cike da kwarkwasa , ƙamshin turaren da boka ya bata shi ya shak'a ai kuwa ta ke yaji kanshi yana juyawa , wanka ta jashi yayi, a hakan dai ta bashi wannan abinci ya ci , kana ya fada mata kanshi na yin ciwo zai kwanta rakashi tayi har sai da ta tabbatar da ya kwanta sannan ta fito daga ɗakin ta, fita tayi daga gidan domin sanar da k'awarta halin da ake ciki. Har bayan magariba bai tashi ba har Asabe ta dawo daga gidan Baraka , sannan ya tashi daga baccin , zuciyarsa yaji ta b'aci gaba ɗaya yaji auren da ake shirin yi masa ya fita a ransa , yaji ya tsani yarinyar gabaki ɗayanta, haka ya kwanta ransa na b'aci, ko da gari ya waye mahaifinsa ya kirashi bai je ba , har aka kwana uku bai je ba , kai auren ya taho dangin sa nata harkokin biki amma shi banda shi, dan haka mahaifinsa ranshi ya b'aci yayi niyyar zuwa har gida ya same shi. Da wata ranar talata lokacin saura kwana biyu a ɗaura auren mahaifin nasa yayi dirar mikiya a gidan, faɗa ya rufe shi dashi, sosai shi kuwa ko a jikin shi ,sai ma duban mahaifin na sa da yayi yace masa shi ya fasa auren daskarewa mahaifin nasa yayi abinda bai taba ji ba , juyawa yayi ba tare da yace komai ba ya tafi gida cike da damuwa, ko da ya sanar da matan nashi sosai su ka ɗauki zafi akan haka, amma da yayi musu bayanin yadda zasu fi ganewa su san ba laifin sa ba ne ba, sai su ka daina hargagin da su ke yi , a haka aka bawa iyayen yarinya hakuri abin ka ga k'auye gari fa ya ɗauka aka yi ta ƙananan maganganu, daga baya komai ya lafa, ita kuwa data ga haka sai ta saki jikinta tayi ta iya shegen ta abin ta , ta kuma mai da zuwa wajen boka sha yanzu kamar masallaci, mahaifinsa ya nema masa ak'alla yara sunyi biyar tana wargaza auren daga baya mahaifinsa ya hakura ya zubawa sarautar Allah idanu, yayin da tsanar Asabe ta dawo sabuwa a zuk'atan matan gida da yaransu . Yanzu shekarar malam Iliya goma da aure , batun gwagwarmayar da ya sha , a harkar sana'arsa da rayuwar auren sa da Asabe Alhamdulillah, komai ya kankama ya samu rufin asiri sosai , babban abinda ke damunsa shi ne rashin haihuwa domin a wannan cikin shekarun aminyar Asabe Baraka ta haihu namiji aka sanyawa d'an nata sunan mahaifinta wato Adamu, a wannan shekarun mahaifin malam Iliya ya sanya ana tayiwa d'ansa addu'ah akan Allah ya dawo masa da d'ansa daga Sharrin matarsa Asabe, Allah kuwa ya amsa addu'arsa da ya dade yanayi. A garin yawon fatauci, wata rana malam Iliya fatauci ya kaishi zariya , bayan ya gama komai yana shirin dawowa gida a
🏠