NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 7 of 44

ya tafi gida cike da fargabar ta ya ya zai fadawa matar sa Asabe a haka ya yini ya kwana babu sukuni da walwala , har sai da Asabe ta gane tambayarsa tayi yace mata ba komai wucewa tayi ba tare da kulawa ba . Washe gari da safe ya tashi da nufin sanar da mai dakin nashi, amma ya kasa , haka yayi ta ajiye da maganar har biki ya kusa saura sati biyu bai sanar da iya ba. Asabe na zaune a tsakar gida aminiyarta ta shigo da gudu cike da alamar firgici a fuskarta , dubanta Asabe tayi cike da haushi ta ce " wai baraka yaushe zakiyi hankali ne wai ke ba kiga cikin da ke jikinki ba kika shigomin irin haka salon ki zo haihuwa ki mutu " dakatar da ita Baraka tayi ta hanyar cewa " yo ba gwarama mutuwa ba an san lokacin ka ne yayi akan wannan bala'in da ya ke shirin tunkararmu" " wanne bala'i kuma Allah ya tsaremu da shi "ta fada tana tura d'an kwalinta gaba har zuwa girarta , " ke Asabe da labari na zo miki naga alamar ke baki sa ni ba ko " ? Ta tambayeta ta jiran amsarta "dan Allah ki fadamin mana kina wani jan zancen" ta sake tura dan kwalinta gaba, "to wallahi mijinki yqna nan yana shirin k'ara aure" , "kan uban chan ba Ankara da garin da ta b'arar ba , ta zunduma wani uban ashariya ," haba biri yayi kama da mutum , shiyasa ya kasa sukuni a cikin gidan nan har ya tafi fataucin nan ashe ya san abin da su ke shiryawa shi da matsiyatan iyayan na shi ", lallai ya taro wa kansa bala'i wallahi ," a'a tsaya mana ai ba hargagi zakiyi ba " cewar baraka da ta ke sake neman wajen zama, " tsayawa zamuyi mu fitar da maganin matsalar da ta ke tunkaro mu", zaman 'yan bori tayi ta zuba uban tagumi hannuwa biyu biyu , " inajinki baraka" ta fada dana kallonta " me ki ke so ayi yanxu "? Ta tambayeta tana kallonta , " kinsqn babu yadda za'ayi nabar wata mata ta auri malam wallahi kina ganin bana haihuwa ta yaya zaayi na bar wata ta shigo ta haifawa malam iliya d'a musamman ma na miji ta yadda zata cinye dukiyarsa " " kinyi gaskiya kuwa aminiyata" yanzu kinaso a tsayar da maganar aurenko"? Ta tambayeta ," eh " ta bata amsa " to yanzu tashi zakiyi mu tafi chan kauyen lajawa akwai wani hatsabibin boka , sunanshi boka sha yanzu magani yanzu , amma ina fatan kinada kudi a hannunki "? Ta tambayeta tana kallonta ," eh da akwai wanda malam ya barmin da zai tafi ban tab'a komai ba ", " to tashi zakiyi mu tafi dan kinsan da zafi zafi akan daki karfe", " eh to bara na Shiga na dauko mayafina" ta shige daki a birkice domin dauko mayafi ,sannan su ka yi waje cikin hanzari. Mata mu kula! Mu kula ,a kula! , kawaye sukan kawo cikas sosai a zaman aure , kar ki bari kawarki ta rudeki takaiki ta baroki akan tudun dana sani , sirrinki ki boyeshi karki sake ki bayyanawa kawarki halin da kike ciki da mijinki , zata sanyaki kiyi danasani a rayuwarki da rayuwar aurenki baki d'aya, daga k'arshe mijinki ya sakeki , in batada aure ta aure miki shi , Allah ka shiga tsakanin na gari da mugu amin . Basu k'arasa cikin dajin ba sai da sukayi tafiya sosai har rana ta fad'i kana suka karasa , dan har Asabe ta sare amma Baraka ta k'arfafa mata guiwa da kyar su ka karasa bayan bakar wahalar da su ka sha k'afafunsu sun kumbura sosai sun jigata , kana su ka karasa wajen , tunda su ka nufi wajen Asabe takejin iface iface namun daji kukan tsuntsaye da sauransu , a haka su ka karasa ," Ku shigo da baya" cewar boka sha yanzu , cikin wata gabjejiyar murya, da sauri suka juya har suna kokarin bige junansu , Baraka ta zunduma ashar ta yiwa Asabe da nunin itama tayi wannan itace sallamar Shiva wajen bokan , aikuwa itama tayi , sannan ya basu izinin zama , su ka zauna ,Asabe ta bud'e baki zatayi magana yayi mata nuni da tayi shiru , zuwa kamar Minti biyar sannan ya bushe da wata mahaukaciyar dariya sai da yayi mai isarsa sannan ya dakata, yayi nuni da wata kwarya sai ta taho da kanta ta zauna a mazauninta kan wata tararriyar kasa , yayi nuni da ruwan cikin kwaryar aikuwa yayi bakikkirin daga baya kuma ya koma fari, aikuwa ya shek'e da dariya" angama bukatarki ta biya za'a fasa auren nagama komai , yanzu maganar aure babu ita na Sanya kiyayya mai karfi tsakaninsu " Myrna sosai Asabe tayi najin an fasa auren malam iliya ,su ka yiwa boka sallama da zasu tafi ya bata maganin da zata zuba masa a abinci da Wanda zata zuba tayi wanka sai turaren da zata sanya Wanda idan har ya shak'a to zai manta da kowacce mace a duniya sai ita, sannan suka nufi hanyar gida a lokacin anyi sallar magariba sannan su ka karasa gida , sai da suka huts sannan Baraka ta nufi gidanta itama, da kudirin aikata abinda boka ya sanyata ta kwana , dan tana tsammanin dawowar malam a tsakankanin wannan lokacin , a haka tayi bacci tattare da mummunan k'udiri a ranta. A chan gidan su malam iliya kuwa anata shirye shiryen biki saboda wannan bikin na so ne , ana wannan yanayin malam iliya ya dawo saga fatauci , lokacin da ya je gidansa da yaga Asabe bata nuna masa wata alama ta nuni da cewa tasan zancen hakan ya saka ya ji dadi kuma yayi mamaki bisa ga yadda yasan qauye da gutsuru tsoma , a
🏠