NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 6 of 44

mata biyu, maza biyu, Khadija , Lami, da kuma Habibu da sulaiman , a dakin hansai wadda itace ta biyu yaranta huɗu , Adam, Muhammad, da kuma Salamatu, Rabi yaranta biyu , Hannatu da kuma Hadiza waɗannan sune zuri'ar malam bello . Mallam bello da iyalansa suna rayuwa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da tarbiyarsu, abin birgewa da sha'awa , yana kulawa da iyalansa yadda kowa kanyi sha'awar waɗannan iyalan . Hakama matan gidan suna da haɗin kai sosai kowacce duk da zaman kauye ne takan taimakawa ƴar uwarta, kuma suna taimakawa mijinsu . Malam iliya shine babba cikin yaran malam bello, gaba ɗaya ragowar yaran gidan kannensa ne , yakan sanya kannensa su tafi makarantar allo, kasancewar a lokacin babu makarantar boko, ya taimakawa ƙannenansa sosai wajen iliminsu na muhammadiyya. Sana'ar malam Bello noma idan ya girbe abinda ya shuka ya kai birni ya sayar , aikinsa noma da fatauci ta haka yake rike da iyalansa , lokacin da malam iliya ya kai mizanin samartaka sai ya sanya iliya akan harkar suna tafiya duk Inda yake harkar fataucinsa , in sun tafi sauran yaran maza sukan kula da harkar noma ta yadda zasu taimakawa mahaifinsu, lokacin da suka dawo gida fatauci Allah ya hadashi da Asabe wadda ta kasance yarinyace ƴar mace mahaifinta ya rasu tun tasa ƙarama dan haka ta tashi hannun mahaifiyarta babu kwaɓa , anyi gwagwarmaya kafin auren dan mahaifinsa bai so auren ba, amma ganin d'an nasa ya na ce yana sonta yasa ya barshi a haka akayi auren ba tare duk da ba kowa yaso auren ba amma a haka akayi auren ........... Please🙏🏻 Share &comments To be continue......... 🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿 🌸🌹Kishiyar uwa🌹🌸 (True life story) 🍁Daga alk'alamin Nussad🌸 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ Fatan alkhairi ga duk makaranta littafina , godiya ta musamman ga masu gyara min kura kurai na . Jinjina gareki aunty nersmah da aunty dije, kuna namijin kokari wajen kuga littafina yayi daidai ba tareda samun matsala ba ina godiya sosai Allah ya bar kauna a tsakanin yan moonlight writer's association amin. Luv u all my dear fan's🥰 wannan page din sadaukarwa ne gareku. Shafi na 4️⃣ A haka akayi auren har amarya ta tare , kadahan kadaran ake zaune tsakanin Asabe da dangin malam iliya, babu wani jituwa a tsakaninsu , da yake ita kuma ba wani iya mu'amala tayi ba bata damu da su ba su ma basa zuwa inda take itama haka , a haka har akaci wata hud'u da aurensu a sannan ne ya ci gaba ta tafiye tafiyensa zuwa garuruwa , sai ya hutashshe da mahaifinsa akan ya zauna tunda shi ya kawo karfi sai ya dauki kaninsa su ka ci gaba da tafiya. Abinda yake damun 'yan uwan malam iliya akan irin rashin mutuncin da matarsa Asabe keyi na bata ganin kowa da mutunci k'annensa basa zuwa gidan yayansu , duk kuwa da irin soyayyar da ta ke tsakaninsu dan shi Allah yayi shi mai so kyautatawa 'yan uwansa , amma kash sai Allah ya hada shi da mata marar sanin darajar mutane. Har iya wannan tsawon lokacin Asabe ko batan wata bata tab'ayi ba hakan ne ya sanya ta kara bakin jini cikin dangin malam iliya , abinka ga k'auye sai surutai kala kala akan taki haihuwa , dan haka mahaifansa mata su ka fara mishi zancen ya kara aure , a sa'ilin da malam iliya yajewa da Asabe zancen nan kamar wadda zatayi hauka dan kishi , ta ci alwashin matukar dana raye babu shi babu kara aure , cin zarafi kuwa babu Wanda bai sha ba a wajen Asabe , ranar tayi yaji ta sanar da mahaifiyarta , abin ka ga gidan da babu tarbiyya haka mahaifiyar ta ta ta goya mata baya , kwananta d'aya a gidansu washe gari malam iliya yaje gidansu Asabe biko amma anan uwar ta ta ta sauke masa kwandon rashin mutunci da cin al washin ba za'a ayiwa yarinyarta kishiya ba indai tana raye kuwa , hakuri yayi ta bayarwa akan insha Allahu hakan bazata faru ba sannan ta yadda 'yar tata ta koma gidan amma sai da tayi ak'alla sati guda sannan ta koma. Malam iliya zaune gaban mahaifinsa wanda ya sanya aka masa kiranshi , ya sunkuyar da kai kasa yana sauraron mahaifinsa cike da girmamawa , " kaji abinda na ce maka ba rigada na yanke hukunci na zab'a maka maryama 'yar gidan aminina malam kalla kuma umarni na baka ba shawara ba na yanke aurenka nan da saba'ar wata in Allah ya kaimu da rai da lafiya sai ka sanar da mai dakinka" , "to" ya amsa cike da girmamawa saboda baya tab'a jayayya da mahaifinsa akan komai ma , amma shi kadai ya san halin da ya ke ciki game da zancen da mahaifinsa ya fada masa , yayi masa sallama tareda shiga cikin gidan domin gaisar da iyayenshi mata , sosai inna hansai ta mishi fada tareda kwadaitar dashi romon da ake samu yayin da aka samu zuri'ah , ta gama yi masa nasiha sannan yayi musu sallama tare da innar sa
🏠