shin kin gama aikin naki ", tace “eh na gama", “toh yau ba maganar zuwa makaranta, rafi zaki tafi ɗebo ruwa, ga kayan Abu chan zaki wanke saboda sun yi datti", kusan fashewa tayi da kuka saboda ta shirya akan cewa za ta je makaranta saboda ta kwana biyu bata samu damar zuwa ba , " toh" ta amsa mata, sannan ta juya ta nufi inda kayan ruwan suke, bokiti ta ɗauka ta nufi hanyar kofar gida, “kafin ki dawo zan zube miki kayan a nan ", “to" tace sannan ta juya ta nufi kofar gida cike da ɗacin rai .
A hanya ta tsaya ta ci kukanta, ta ƙoshi, sannan tayi gaba , tana tunanin rayuwarta a nan gaba duk da ita yarinyace amma tana iya sanin masoyinta da maƙiyinta , ta ɗebo ruwa sosai har ta cika gidan dukka , kana ta fara wanke kayan , bata gama ba har sai da rana ta fito, sannan ta gama a wahalce , tana gamawa ta nufi dakin Asabe, " inna na gama" tace da ita, "to kije ki daura girki ", “inna wallahi banci abinci ba ", “ka ji min shegiyar yarinya yo dan baki ci abinci ba sai me, ai aiki yanzu ma kika fara shi , sai kin gama aiki tsaf, sannan ki duba idan 'yar lele ta rage abincin ", to ta juya idanunta cike da hawaye , sai da ta kammala abincin nan tsaf sannan ta zuba musu ka'ida ne daman sai sun gama cin abinci sun rage kafin ta ci dan haka sai ta jira suka gama sannan ta dauki sauran taci a lokacin ta galabaita sosai, tana jan jiki ta shiga ɗaki, zaunawa tayi, sannan ta soma cin abincin cike da kewar mahaifiyarta, duk kuwa da bata santa ba ta ya ya zata iya cigaba da fuskantar wannan rayuwar mai cike da tsanani da dana sani "Allah ka kawomin dauki amin" taƙarasa haɗe da share hawayenta da suka gangaro mata kuncinta , tana wannan zaman har bacci ya kwasheta .
Tana cikin bacci nan taji an kwara mata , a razane ta farka, "au ke yanzu dan ubanki maimakon ki zo kiyi abin da za ki yi, kin san ki na da aiki shine kika zauna , shegiya mai mugun hali , tashi shegiya kawai" Asabe tayi furucin da bokitin ruwa a hannunta, "to inna zan fito ", “au jiran ki zan yi ki fito dan ubanki" ta tambayeta tana kokarin fincikota hade da kai mata duka, “inna dan Allah kiyi haƙuri wallahi na gaji" , “au ni ki ke cewa kin gaji, lallai wuyanki yayi kauri yau zaki gane kurenki a gidannan fito" , ta fada tana ƙoƙarin shiga daki , dukanta ta shiga yi ba ji ba gani, sai da ta tabbatar bazata iya moruwa ba, duk jikinta ta fasa mata shi "kuma ki tashi kije ki yayo itacen da zakiyi girkin dare tunda yau mallam IIlyan bai dawo ba" tana nufin mahaifinsu su Fatima , da Ƙyar ta tashi da rarrafe ta dauki yagaggen mayafimta ta fita domin yo itace a daji bata dawo daga itacen ba sai chan yamma a lokacin ta gaji sosai, amma haka ta daure ta daura girkin bayan ga Abu a zaune tana faman barar gyad'a tana zubawa a baki .
A haka rayuwar Fatima ta cigaba da tafiya, cike da tsanani, da tsauri, da azabtuwa, har suka kai shekaru goma sha biyar ita da Abu a lokacin ne maƙerin budurci ya fara ƙera su , Fatima ta fito a matsayin kyakykyawar budurwa son kowa, to a sannan ne fa samarin kauye suka ƙara yimata chaaaa a kanta ciki kuwa har da Ado wanda har yanzu yake kan bakansa na soyayya da ita , domin har ya sanar da mahaifiyarsa domin ta sanar da inna Asabe. Duk da wannan kyawun nata daya bayyana, amma hakan bai hana tsantsar wahalar da take ciki , ta bayyana akan kyakykyawar fatarta ba.
A wannan shekarun abubuwa sun faru na daɗi, da akasin haka, ciki kuwa har gama makarantar Fatima, ta firamare wadda da ƙyar hakan ta samu, bayan gwagwarmayar da aka sha da inna Asabe akan harkar makarantar , a yanxu cikin ikon Allah komai ya zama tarihi game da makarantarta ta primary, secondary ce dai bata amince ba, duk kuwa da cewar malaminsu na makaranta, malam Ahmad yayi gwagwarmayar ta cigaba, ganin irin hazakar da take da shi amma fafur ta k'iya , ganin haka ya hakura har ya koma garinsu Kaduna, dama bautar kasa yazo kuma ya gama ya koma ba tare da samun ya samu ya cika burinsa na ganin Fatima ta cigaba da makaranta ba .
A yanzu gashi mahaifinsu girma ya kamashi dan haka baya iya tab'uka komai , duk da, ada ma ba iya yin komai ballantana yanzu da ƙarfinsa ya ƙare duk da yana gudu da ƙyamar abun a zuciyar shi, ganin yadda ake yiwa d'iyarsa , a lokaci da dama ya kan so ya baiwa yarinyarsa labarin mahaifiyarta amma idan ya tashi faɗa mata sai ya kasa , a haka yake barin abin a ransa badan yana so ba, wani lokacin ya kan ji kamar ya yi kuka, idan ya tuna da mahaifiyar Fatima da irin zaman da sukayi lallai ba shakka Fatima ta dauki halin hakuri irin na mahaifiyarta.
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
(Asalin labari)
Shin wai wanene mallam iliyasu mahaifinsu Fatima ?
Malam iliyasu hafaffen garin kano ne, a ƙaramar hukumar wudil yankin darki , yana zaune tare da iyayensa da yayyensa da ƙannensa, mahaifinsa malam Bello matan sa uku , laraba da hansai da kuma Rabi kowacce su tana da yara laraba itace ta fari, tana da yara biyar kuma itace mahaifiyar su mallam Iliya , bayan haka yana da ƙanne, biyu