NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 43 of 44

Kafin kace me gida ya cika da y'an uwa, Allah sarki har da baba Muhammadu, har kuka yayi, kuma yaji dad'in ganin Fatima da mahaifiyar Fatima, kowa mamaki ya kama shi ganin ashe dama Maimunatu bata rasu ba, sai da su ka sarara sannan , Fatima ta sulale ta nufi gidan rahina, sosai suka yi murnar ganin juna , sosai su ka yi hira sannan ta mata alkhairi , ta raka ta har bakin zaure , su ka gaisa da Ahmad sannan suka wuce........... Please Share & Comments To be continue........ 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹 KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁 Daga Alk'alamin Nussad🌸 SHAFI NA 49__50 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ 'KARSHE💃🏻💃🏻 Bayan sun koma ne, baba Asabe ke zaiya ne musu duk abin da ya faru, har da abin da ya faru da zainabu , tace" yaron nan ashe ba d'an arziki bane ba , ashe da ake cewa ya samu aiki a kudu , ba aikin Allah da Annabi ne ya kai shi ba, bayan aikin da yake yi , harda neman mata, watan su d'aya ta fara fuskantar k'alubale a rayuwar aurenta, da abun yayi tsamari , haka zai shawo kayan mayensa, ya shigo ya mata dukan tsiya , ya kawo mata yan mata karuwai , da k'yar tayi haihuwa d'aya a haka sai da ta Haifa masa wad'annan yaran , ba abinci , kullum sai duka , da k'yar bayan haihuwar jaririn nan ta samu Allah ya sanya ya sake ta , gashi ba kud'in mota , haka nan mak'wafciyarta ta bata kud'i da wadanda tayi aikatau ta had'a ta nufo gida, shi yana chan yana shek'e rayuwarsa a chan, ta fad'a tana matsar hawayen namada ", da k'yar su ka lallab'ata tayi shiru, sosai su ka jajanta mata, a ranar suka koma Kaduna da zama, amma kafin su tafi sai da su ka ajiye musu alkhairai da dama , sannan Fatima ta bada kwangilar a gyara gidan na su , ta bawa baba muhammadu jari , sosai tayi rabon bajinta wa dangin na ta , ana murna da komai su ka tafi duk da sun so su kwana amma mummy tace zata zo na musamman ta kwana, sannan su ka koma Kaduna. A chan b'angare d'aya , bayan an saki LAILA da Aliya , sosai ta shiga harka da samari , ta had'u da wani saurayi , sosai rayuwarsu su ke yi, bai fada mata yana da cuta mai karya garkuwar jiki ba , sosai su ke mu'amalarsu , bata tashi farga da cewar ta kamu ba sai da ciwo matsananci ya taje wajen likita gwajin farko aka tabbatar mata da cewar ta kamu da HIV , kamar zata yi hauka su ka dawo da mummynta gida , rayuwa duk ta sauya mata , gashi mahaifinta yanzu karayar arziki ta same shi , haka dai ta k'arasa jinyar cutar ta tana karb'ar maganin gwamnati a asibiti. Fatima ta koma gidan ta , soyayya mai tsabta su ke zuba wa, kullum tana godewa Allah da ya sauya mata rayuwarta zuwa mai kyau, a yanzu ta gama karatunta tayi jarabawar k'arshe su na jiran sakamako , saboda kamfanin Ahmad da yake k'asar waje yana buk'atar cigaba ya sanya yayi tunanin cewar gwara su tafi da iyalinshi chan , domin ita ma ta cigaba da karatunta a fannin Medicine. A b'angare d'aya soyayya mai k'arfi ta ginu tsakanin doctor Sadeeq da Halima k'awar Fatima tun lokacin da ya ganta a sunan y'an biyu ya rikice mata, a yanzu dai an Sanya ranar aure sai dai fatan Allah ya sanya ayi da mu Amin. Bayan komai ya kammala , su ka fara shirin tafiya kasancewar komai , ya yi kyau game da result na Fatima , hakan ya Sanya ana i gobe zasu tafi su ka shawarci junansu akan su kai ziyara asibiti, su bada taimako aikuwa , sunyi abinda ya dace , suna k'ok'arin fita daga asibitin Fatima taji ana kiran sunanta, da sauri ta juya , wata ta gani mai kama da LAILA sai dai wannan bata kai LAILA komai ba saboda a iya sanin Fatima LAILA ta kere mata da yawa, " baki ganeni ba ko Fatima , LAILA ta fad'a tana k'arewa Fatima kallo dama shi uban gayyar wato Ahmad , Wanda ya rumgume Al hassan a kafad'arshi , yayin Al hussain yana kafad'ar Fatima , bayani sosai tayi musu sannan su ka gane , aikuwa Ahmad yayi saurin jan Fatima domin ya tsani ganin LAILA a rayuwarsa , Fatima ce ta bashi hak'uri su tsaya su fuskance ta, LAILA hak'uri ta shiga bawa Ahmad dama Fatima , ta fad'a masa duk abinda ta masa, kama daga samun cikinta har zubar da shi da ta dinga yi, sosai yaji bakin cikin abun amma daya tuna da yadda LAILA take sai ya godewa Allah da ya sanya jininsa bai fito ta tsatsonta ba , sannan ta nemi yafiyarsa, yace shi ba komai, haka ma Fatima , ta zayyane musu abinda ke damunta sosai su ka jajanta mata, su ka mata al' kairi sannan suka barta tana zubar da k'walla na abinda ta yiwa rayuwarta , da tuni yanzu ita ke da wad'annan zuk'a zuk'an yaran, haka tana ji tana gani su ka tafi su ka barta . Ana i gobe zasu tafi suka je suka yiwa Mummy sallama, dama sun je zaria sun yiwa maman Fatima sallama , da dare suka gama shirya kayansu tsab , tare da na yaransu.
🏠