a ki kwantar da hankalinki ba abinda zai faru inshaAllahu kinji ko, kuma nasan yarinyar nan shegiya mayya k'arshe ma dai sai kabari saboda ta jigata da yawa, tana magana tana k'ok'arin bud'e status d'in da Ahmad ya d'auka , wani uban ihu da zunduma had'i da ashar ",Aliya dake zaune ta mik'e dama a firgice take saboda tsananin tsoro sai a yanzu take danasanin sanarwa da LAILA , dan batasan LAILA zata iya yin haka ba "," zo kiga", kallan fuskar wayar tayi jarirai ta gani twins duk maza, kuma kamar su d'aya da Ahmad, bata tsinke da al amarin ba sai da ta karanta comment d'in da yayi a k'asan yaran ,a tare su ka furta " mun shiga uku , dama bata mutu ba" ai a hanzarce Aliya ta had'a yanata yanata ta bar gidan cike da tsoro da tashin hankali, ta bar LAILA ita kad'ai tana zulumi , shikenan asirinsu ya tonu matukar yarinyar ta ta shi to ba makawa ita zata fara ambata , matuk'ar aka tambaye ta Wanda ya aikata mata wannan d'anyaen aikin.
After 1 week
Sosai Fatima ta warke sai abinda ba'a rasa ba , ranar aka sallame su , aka bar bikin sunan wani satin , yaso abar masa Fatima a gidanta amma fafur Mummy tak'i wai ita zata kula da yarinyarta da jikokinta , haka ya hak'ura badan ya so ba saboda yana buk'atar matarsa a kusa da shi amma ya k'yale, Halima kusan kullum tana gidan domin duba mai jego da yaranta , haka a b'angaren LAILA duk wannan abun da akeyi bata tab'a zuwa ganin jarirai ba , kuma ba Wanda yabi ta kanta , har da shi uban gayyar domin shi a yanzu ta lafiyar uwar yaransa yake yi.
RANAR SUNA.
Sosai Fatima ta samu lafiya , ranar suna yara aka rad'a musu sunansu da kowanne yaci , anyi bajinta iya bajinta , sa aka yanka da raguna kowanne yaro biyu, an ci an sha , an raba kayayyaki , mejego tayi kyau k'arshe, ina daga gefe ba sai na hango Queen nersmerh tawo da tawagar y'an moonlight writer's, su Mrs breaker ana ta k'alala idanu , an sha atamfar roba , su latifa sai bud'e idanu akeyi anaso a hango Ahmad , ni kuwa na b'uya saboda banaso su ganni , ballantana su saka ran zan samo musu abinci.
Chan tawagar KISHIYAR UWA FANS su ma suka hallara, duk cikin su sis fareeda ce kawai sai sis humaira suka ci kwalliya , Dan haka na ja su gefe na zuba musu abinci , su kuwa su Queen na barsu da yunwa.🤪🤪.
Toh Alhamdulillah, a haka taron suna ya watse bayan an raba gifts sosai, aka tashi , aka bar me jego da yaranta, Mummy na kula da su , sosai yaran suna wayo kai baa ce y'an wata bakwai bane ba, a haka suka cigaba da zama har sun kusa wata d'aya.
A chan b'angare guda kusa , sosai Ahmad ya sanya anayi masa bincike, akan Wanda ya shigar masa gida a ranar da Fatima zata haihu, shaidar farko da aka samu a wajen mai gadin da ke kallon gidan Fatima ne, cewar LAILA ce da k'awarta ko da wannan magana ta isa ga kunnen Ahmad , ya razana sosai kuma yak'i gasgata hakan , amma yanzu ya gasgata, kuma abu kad'an yake jira ya sanya a kamo masa su , ko ya koma gida baya nuna mata damuwarsa , kuma har lokacin kowa al amarin gabansa yake yi , bai sanar da ita har a lokacin Fatima ta haihu ba, ita ma bata nuna masa ta sani ba , ganin anyi shiru da zancen ya sanya daga ita har k'awarta Aliya suka saki jiki, aka cigaba da harka da samarin bariki.
A b'angaren Ahmad, tun Fatima na kwana ashirin ya matsu ta koma , tun baya fad'awa Mummy yana jin kunyarta har ya same ta ya sanar da ita , amma fir tak'i, ko da ya tuntub'i Fatima da maganar ta shaidawa Mummy tana son komawa, k'in fad'a tayi , hakan ya hassala shi , domin yana buk'atar matarsa a kusa da shi da yaransa, sai ya d'auke musu wuta ya daina zuwa, ya maida kansa gun tabbatar da zarginsa akan LAILA, ya k'yale su , domin yanaso yaga iya gudun ruwan Mummy da Fatima.
AFTER 2 WEEKS.
A lokacin komai ya kammala na bincike , LAILA na zaune a falo tana shan ice cream aka k'wankwasa k'ofa , cikin gadara ta tashi ta isa wajen k'ofar tana tambayar ways , shiru aka mata , cikin fusata ta bud'e me zata gani y'an sanda , sun kusa bakwai maza sai mata mutum biyu , basu yi wata wata ba suka damk'i hannunta bayan sun bata shedar kamawa, sannan aka cilla ta bayan mota sai police station , ko da su ka k'arasa, tana ta so ta musu taurin kai aikuwa , ta sha jibga koni na tausaya mata 😩, DPO ne ya kira wayar Ahmad , ya shaida masa da cewar an kama LAILA tana hannunsu a halin yanzu aikuwa , yana wajen aiki amma haka ya tattara kayan aiki ya nufi office d'in y'an sanda.
Ko da ya k'arasa sosai LAILA tayi mamaki, da jin cewar wai Ahmda ya sanya a kamata , to me tayi abinda ta fara tambayar kanta kenan , amma sai ta dake, ko da aka fara fad'a mata abinda ya fara ai daskarewa tayi , bata gama dawo wa daga cikin duniyar da ta shiga ba, taji saukar takarda fara a hannunta , bud'ewa ya bata umarnin tayi , aikuwa tana bud'ewa ta zunduma ihu , " Ahmad ni zaka yiwa haka , ni zaka saka sakin ma na wulak'anci har uku ", " shi ne abinda ya kamata da a yi miki, domin dama na gaji bazan iya zama da wadda zata ga bayan iyalina ba , dama na gaji da halinki,