amu dake ya tambayeta ya kallonta "da ni nace ka damu dani ne ta fada cike da k'osawar ya barta ta shiga gida naji bake kikace ba amma kinsan ba wadda nike nunawa soyayya irinki ko kinsan dai 'yammatan garin nan suna kawo Kansu inyi soyayya dasu ko ," toh naji " ta fada tana kokarin shiga gida don ita a rayuwarta ta tsani zancen soyayya gani takeyi kamar dan iskane Wanda ke cewa yana sonta , duk kuwa da dama mutane samarin kauyen na kawo mata hari duk da yarintarta amma tana gocewa , maganarsa ce ta dawo da ita daga tunanin data tafi " zanyi mawa innata maganar , jitayi kamar ta sanya ihu saboda razana ita fa ta tsani wannan mutumin , baki ce komai ba ya fada ya na kallonta , shigewa gida tayi tare da banko kofar gidansu ta barshi a tsaye yana kallon kofar gidan tare da cewa lallai zanyi maganinki ta karfi tunda bakisan lallashi ba ya fada a cikin zuciyarshi a yayin da yake shirin barin kofar gidan.
Wannan kenan
Da sallama a bakinta ta shiga , a tsakar gidan ta tarar da mutanen gidan barka da dare ta musu kana ta mikawa inna asabe kudin warta tayi kana ta kirgasu sai da taga sun cika cif sannan ta saki fuska" tashi kije ga ragowar abinci Chan ki ci toh tace sannan ta tashi ta nufi wajen abincin.
Mahaifin Fatima Wanda tunda ta shiga baice uffam ba ya juya ya kalli yarinyar tasa cikeda tausayi a ransa ya na fadi lallai hakkin yarinyar nan bazai taba bari na ba ina so na fada gaskiyar labarin mahaifiyarta amma ina tunanin wata rana zata iya guduna zuwa ga mahaifiyarta , a cikin ransa yake wannan maganar sa'ilin da yake jin k'unar azabtar ta 'yarsa da akeyi yarasa gane kansa sai yayi niyyar yin magana sai ya kasa amma ya barwa Allah komai.
"Uhmm ni kuwa asabe dazu da rana na dawo bakya nan ina akaje ne , au shaf fa na sha'afa wallahi yar gidan yaya habu na kan tudu aka saka ranarta shine mukaje , oh ni asabe malam kai bakaga abin arziki ba ai mu dai mun sha kallo inayiwa Abu fatan samun haka , karkada kanshi kawai yayi lallai mata ba'a musu ita nata kawai ta sani Allah ya kyauta.
Anan inason naja hankalin mata wadanda ke zaune ya yaran kishiyoyinsu 'ya'ya na kowane babu Wanda kasan zai yi maka rana a rayuwa , amma wadansu matan ba wadanda suke ababen soyuwa a garesu sai yaransu kawai banda su kowa ma hotone , musamman in baa zaman lafiya da mahaifiyar yaron ko yarinya, Ku tuna su fa basu da laifi ko kadan hasali ma basu san yaya akayi gabarku ta kullu ba, mata mu kula amanar Allah ce in ka ci tabbas zata ci ka fatan zamu gyara ,Allah ya bamu ikon gyarawa amin summa amin.
Bayan ta gama cin abincin ta tattare kwanikan da akaci abincin dasu a dare nan ta wankesu , a lokacin data gama ba kowa duk an shiga daki dan haka itama ta wuce nata dakin dan kwanciya bacci aikuwa tana kwanciya bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita .
Wata mata ta hanga chan kan wani tsauni mai Nisan gaske matar ta juya mata baya , matar tana ta kiran sunanta Fatima! Fatima! Ta na ta kiranta tana so ta kama ta amma ina ita kuwa sai kasan wannan tsauni takeyi gangarawa takeyi tana k'walla ihun Neman agaji a haka ta farka daga bacci tana ihu , salati tayi tare da addu'ar tashi a bacci tana lekawa taga har ta makara dan haka tayi sallah ta soma aikace aikace kamar yadda ta saba , da yake ranar asabar ce ba makaranta sai karfe goma zata tafi makarantar allo wadda da kyar asabe ta yarda akan zataje da taso da safe ta rink'a yi mata tallar kosai amma hakan bai samu ba. Wannan lokacin data samu hakan ya bata damar yin aiki sosai .
Har ta gama ba Wanda ya fito da haka ta tsaya tana jiran fitowar masu gidan tare da addu'ar Allah yasa su fito da wuri dan ta samu damar zuwa makaranta...........................
Please🙏🏻
Share
&
Comments.
To be continue.......
🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿
🌸🌹Kishiyar Uwa🌹🌸
( True life story).
🍁Daga alk'alamin Nussad🌸.
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
Ina godiya da shawarwarinku , ga yadda zan tafiyar da littafina, musamman makaranta littafina da 'yan uwa da abokanan arziki.
Ina ganin yawan comments naku, ina jin dadi kuma insha Allahu nima bazan baku kunya ba.
Sadaukarwa ga iyayena da 'yan uwana da abokanan arziki , luv u all🥰
Wannan page din nakine sadaukarwa gare ki 'yar uwata Zainab, Allah y kawo miji na gari amin.
Shafi na3️⃣
Tana nan tsaye har karfe tara tayi kafin nan mutanen gidan suka tashi , da hanzarinta ta isa ga mahaifinta "Baba ina kwana" , tace“ lfy qlu , har kin gama aikin naki ", “eh na gama da shi" “toh Allah ya miki Albarka ", “amin" tace da shi , sai a sannan Asabe ta fito tsakar gidan , " Inna ina kwana", “lafiya "ta amsa a yamutse, “