a maida hankalinta ga samarinta yayin da a b'angare d'aya, shi kuma Ahmad yake samun wannan damar in kwanan Fatima ya zagayo, a haka su ka koma makaranta, taci gaba da karatunta, bayan ya shaidawa principal d'in makarantar akan cewar zata yi jarabawar gama secondary a aji biyun senior
Hankalin Fatima ya kwanta , sai Sam barka , suna wata na hud'u da aure Allah ya a zurta , zo kuga murna lokacin da Dr ya sanar musu da wannan sakamakon , wanda a wannan lokacin suna daf da fara jarabawa,sosai ya shiga kula da Fatima cikin so da k'aunar juna , tarairaya ba wadda bata gani, ita kanta idan ta zauna godewa Allah kawai take yi , dan ganin Allah ya sauya mata rayuwarta ta da , da jin dad'i , rayuwarta dai abar sam barka da kwatance.
A b'angare d'aya kuma, Mummy tawa Ahmad magana akan cewar tunda yanzu rayuwar Fatima ta sauya, kamata yayi ya kai ta k'auye domin ziyartar y'an uwanta , a kuma shaida musu duk al amarin da suka faru, sosai ya gamsu da haka, ko da ya koma ya sanarwa da Fatima abinda Mummy tace,tayi murna sosai, ya sanar mata da cewar ana gama jarabawarsu, za su tafi , harda mahaifiyarta.
Fatima a zaune a falo, yayin da cikinta a lokacin ya kai wata bakwai,sallama taji anyi hakan ya sanya ta mik'e da k'yar ta nufi bakin k'ofa kasancewar tayi nauyi, da fara'arta ta bud'e k'ofa," ah aunty Aisha barka da zuwa, wallahi tun d'azu nike jiranki ,ta fad'a tana kallon mak'ofciyar ta ta , wadda suka shigo ita da wata bak'uwa, " ke dai bari Fatima wallahi Aliya ce ta tsayar da ni, kinganta nan k'awata ce sai dai ita bata ji ko kad'an," harara r wasa Aliya ta jefawa Aisha, da sannan Fatima ta matsa musu suka wuce, zuwa cikin falon, da hanzari Fatima ta wuce, domin kawo musu ruwa, Aliya ce ta dubi Aisha cikin mamaki bayan ta yi nuni da hannunta zuwa cikin wani photo,wanda Ahmad ya rungume Fatima aka musu photo, sunyi bala'in kyau sosai kamar ka sace su ," Aisha wannan fa waye, ta tambaya cike da mamaki, " lah ai mijinta ne " , cike da mamaki Aliya ta kalle ta, miji kuma ," girgiza kai tayi sannan tayi shiru, ita kad'ai ta san me take k'issimawa a ranta, Ahmad mijin LAILA shine ya zama mijin wannan yarinyar gashi ma ta lura akwai rabo a jikinta, a hanzarce ta sha ruwan da ta k'agauta ta fita ta sanarwa da LAILA halin da ake ciki, ko da suka gama bata koma gidan Aisha ba ta wuce gidan LAILA.
Tun daga bakin falo take k'wallawa LAILA kira, a hanzarce LAILA ta sauko daga upstair, " haba Aliya ta yaya zaki shigo kina min ihu bayan kinsan ina chan ina hutawa ta"," dallah chan wanne irin hutu , kina hutu amma mijinki yana chan shima yana hutawa " ," bangane ba, ta fad'a tana zare idanu"," toh ki sani cewar mijinki ya k'ara aure ba tare da kinsani ba ", wata uwar ashariya ta doka " ni za'ayi was hauka lallai ma amma ta yaya aka yi kika san cewar Ahmad yayi aure kin tunanin zaiyi aure ba tare da cewar ya fad'a min ba ta fad'a cikin k'araji "," yau da idanuna ma na kalla matar Ahmad harda tsohon ciki "," tsohon ciki fa kika ce tabbas kuwa," , " Aliya rakani in ganewa idanuna domin dai na tabbatar da cewar kina min wasa ne ko kuma gaskiya kike fad'a min , cikin hanzari da tashin hankali ta nufi sama domin daukar mayafinta, sai da ta sauko sannan Aliya ta ja ta , suka nufi mota , Allah Allah LAILA take yi su isa aikuwa ko da suka k'arasa sunyi sa'a mai gadi ya jagaya masallaci , aikuwa cikin hanzari suka shiga , sallama Fatima taji ya sanya ta fito bak'uwar d'azu ta gani , gabanta ne ya fad'i ganin wadda suke tare, " aunty LAILA , ta furta da k'arfi ", LAILA ce ta zare idanu wa take shirin gani kamar wannan mayyar yarinyar nan , aikuwa d'aga idanun da zata yi taci karo da hoton Fatima tare da Ahmad, wani uban hanzari ta daka gami da finciko Fatima , wallahi sai na kashe yarinyar nan , hankali na zai huta, jibgarta ta shiga yi tun Fatima na kuka harsai da ta suma sannan suka k'yaleta , aikuwa jini ya b'alle mata ganin haka ya sanya suka yi shirin ficewa daga gidan.
Ahmad wanda tun yana zaune a office , yaji gabanshi yana fad'uwa, hakan ya sanya ya baro wajen aiki ya nufi gidan Fatima , a bakin gate ya tsaya yana horn, shirin da yaji ya sanya ya fita daga motar ya nufi cikin gida , tin daga k'ofar d'akin ya fara sallama , shirun da yaji ya sanya ya shiga ciki, a kwance ya hango ta , da Sauri ya k'arasa inda take kwance, jijjigata ya fara yi , d'aga ta da yayi ne ya kalli jini na kwance a k'asa , cikin zare idanu, ya shiga girgiza ta yana kiran sunanta," Fatima ki tashi, ki tashi karki mutu , karki mutu bazan iya rayuwa in babu ke ba , ganin haka bazai kai ba ya sanya ya d'auke ta ya nufi mota cikin hanzari ya ta da mota ya nufi asibiti da ita.
Su LAILA kuwa b'oyewa suka yi ganin motar Ahmad ta nufo cikin layin, sai da suka bari ya wuce sannan suka wuce , ta k'yar su ka k'arasa gida suna maida numfashi , bayan sun huta Aliya ta dubi LAILA , "amma kina ganin yarinyar nan bazata fallasamu ba kuwa, ni fa inajin tsoro wallahi ,", " ke ni fa bai dame ni ba Allah yasa ma ta mut