NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 37 of 44

nasanin yin aure , ashe abinda su Aliya suke fad'a mata gaskiya ne , ba komai a cikin aure sai nadama , da ace a lokacin Aareef ta had'u da shi da aurenta tafi jin dad'i , a haka ta shiga gida har a lokacin bai dawo gida ba abinci taci sannan ta haura sama domin hutawa, wayar hannunta ce tayi k'ara , ganin mai kiran ya sanya tayi dariya had'i da d'agawa, " lallai matar nan kin samu duniya kin manta damu ko, aka fad'a daga chan b'angaren ," ah haba Aliya wallahi guy d'in da na had'u da shi ne ya k'ure k'arshe , amma ban manta da ke ba , so ya gida ", daga chan b'angaren Aliya ta amsa, nan su ka ci gaba da hira cikin nishad'i , ita kuma LAILA tana bawa Aliya labarin Aareef, bayan sunyi sallama , ta kishingid'a bacci kuwa yayi awon gaba da ita. A b'angaren su Fatima kuwa sosai baccin ya musu dad'i musamman ma Ahmad yaji dad'in baccin sosai, sai k'arfe kusan biyu sannan suka tashi, Ahmad ne ya riga tashi dan haka da azama ya nufi k'ofar falo Allah ya taimake shi Mummy bata falo hakan ya sanya ya tafi part d'insa , domin yin sallah. Ko da Fatima ta tashi , ganin baya nan ta ji dad'i , hakan ya sanya ta shiga toilet domin yin alwala. Ko da tayi sallah , kasa fita falo tayi gani take yi kamar mummy tasan Ahmad a tare su ka yi bacci da ita , a chan falo ganin Mummy tayi har lokacin Fatima bata fito taci abinci ba , "am baba na duba min kaga daughter ta lafiya , naga har yanzu shiru, ko gajiyar ce har yanzu", tashi yayi ya nufi k'ofar d'akin Fatima, da sallama ya shiga cikin d'akin tana zaune a bakin gadon tana ganin shi tayi zumbur ta mik'e , " ki je inji Mummynki , domin naga yanzu kin k'wace min fada ta", murmushi tayi kawai tayi hanyar waje shima ya bita, ko da su ka gama con abincin , sai ya zauna su ka dasa hira shi da Mummy, ita dai Fatima bata samu su baki kasancewar akan tariyar tata ake yin maganar , ganin abun na su yayi yawa ya sanya ta shiga d'aki ta barsu, sai wajen bayan magriba sannan ya tafi gida . Ko da ya isa gida , bai bi takan LAILA ba ya nufi d'akinsa , kasancewar yayi sallah a masallacin gidan Mummy , ana shirin yin isha'i , ya nufi masallaci, ana idarwa ya dawo ,a d'aki ya zauna , aiki yayi sosai sannan ya kwanta , da farin cikin gobe ya war haka yana tare da Fatima a gida d'aya , ji yayi kamar ya janyo goben, a haka dai ya lallab'a yayi bacci cikin nishad'i. A b'angaren LAILA ko da ta ga bai shigo ba, kuma taga dawowarsa hakan ba k'aramin dad'i ya mata ba kasancewar tana charting da wani sabon saurayi da suka had'u a Instagram, sosai guy d'in ya tafi da imaninta, soyayya suke zubawa , kamar ba matar aure ba, a yanzu ma da shi suke chart, ko da yake sauran ma bata rabu da su ba , sai misalin karfe d'aya sannan ta kwanta bayan sunyi sallama.............. Please Share & Comments To be continue.......... 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁 Daga Alk'alamin Nussad🌸 SHAFI NA 41__42 Washe gari , tun asubah ya tashi , kasancewar akwai aikin da ba'a k'arasa ba a gidan Fatima, kuma ya bar masu aiki , zasu yi aikin kwana, da hanzari ya shirya, k'arfe bakwai daidai ya fita daga gidan bayan ya sanarwa da LAILA cewar zaiyi tafiya, kafin ya dawo ta shirya masa kayansa a jaka,da murnarta ta amsa har sai da yayi mamaki, kasancewar in dai zaiyi tafiya ta dinga k'orafi kenan , yana fita daga gidan ta shiga falo , had'i da lalubar number Aareef , kasancewar ya shaida mata lallai su had'u a yau , dan haka ko da ya d'aga da murnarta ta sanar masa shima yayi farin ciki, sannan ya fad'a mata inda zasu had'u. A chan b'angare guda bayan ya k'arasa gidan ya tarar da komai ya kammala , saboda ya makara a office ya sanya bai biya gidan mummy ba sai dai ya sanar da ita amgama aikin, saboda ta shaida masa cewar za'a so jere, bayan ya gama sanar mata ne ya wuce office. A chan gidan mummy kuwa, daga ita sai mahaifiyar Fatima sai kuma aminiyarta , wato hajiya sadiya, kasancewar ta sanar da su dalilin auren d'an nata ya sanya su ma suka yadda da hakan , sannan suka sanya albarka, su da kansu suka yiwa yarinyar ta su jere na gani na fad'a, komai masha Allahu, sai san barka, wannan kenan. Fatima a zaune a d'aki, yayin da Halima k'awarta tana ta aikin lallashi, " kinga Fatima ki nutsu ki k'watarwa kanki y'anci, kinga dai yadda yanzu rayuwa take , wallahi da ni na samu ya Ahmad da wallahi yaga yadda ake tarairaya, , dan wallahi ko ita LAILAN zata yi mamaki , ki rik'e mijinki hannu biyu biyu , kinji na fad'a miki " , cikin sheshshek'ar kuka Fatima tace " Halima bazaki gane ba ina tsoron LAILA wallahi , saboda irin matan nan ne masu mugun kishi akan mijinta ba abinda bazata yi ba walllahi", " shi yasa na fad'a miki ki jajirce tunda yanzu matsayinku d'aya da ita , a da dai ke ba kowa bace ba amma a yanzu gaji y'ar uwa a gare shi kuma mata , ki sanyawa kanki salama", sosai ta mata nasiha yadda jikin Fatima yayi sanyi sosai ta yaddarwa kanta cewar zata iya , sai
🏠