NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 36 of 44

Fatima ta shiga bawa labarin irin rayuwar da ta tsinci kanta a ciki ba mahaifiyarta ta ta ba , hatta Mummy da kakarta sai da su ka zubarda hawaye, na tausayin halin da Fatima ta tsinci kanta a ciki , babu abinda ya gigita mahaifiyar Fatima sai labarin rasuwar malam Iliya mahaifin Fatima, tayi kuma sosai , sai da aka bata baki da nasiha sannan ta hak'ura ta dangana, a nan suka tsayar da zasu yi sati a nan , zasu kuma su bar Fatima wayen mahaifiyarta ta yi wata , duk da Ahmad bai so watan ba amma yana ganin in yayi adalci gwara ya hak'ura , haka kuwa akayi sun gama kwanakinsu, suka bar Fatima kasancewar anyi hutu dama, sosai suka dinga zaga dangi da ita aka nuna mata duk wad'anda bata sani ba , anan take tabbatar da cewa ita d'in y'ar dangi ce. A b'angaren LAILA kuwa rayuwa ta bud'e musu ita da Aareef su ke cin karensu babu babbaka, yanzu kam LAILA ta zama y'ar hannu ba inda bata zuwa, maza kowanne iri bi take yi , sai dai kawai mu mata addu'ar shiriya. ZARIA Sai da Fatima ta cika wata d'aya , sannan aka fara shirin komawarta bayan mahaifiyarta ta gyara ta sosai, domin Ahmad ya sanar mata bata tare a gidansa ba , ya fad'a mata duk yadda suka yi da Mummy, ta kira yayarta ta , ta rok'eta akan ta barwa d'anta matarsa, sosai ta mata magana ta yadda zata fuskanta, kuma ta amince da hakan , dama ita tunaninta a bari a samu dangin Fatima kuma an samu sannan dad'in dad'awa tayi hasashen akwai dangantaka da Fatima shiyasa, ko da aka sanarwa da Ahmad sosai yayi far in ciki, ya kuma shiga hidimar gyaran gidan da Fatima zata zauna kasancewar ba gida d'aya zasu zauna ba, hakan ne ya sanya Ahmad bai lura da halin da matarsa LAILA ke ciki ba , baya ma da lokacinta , harkar aikin gidan Fatima kawai yake yi. A ranar da ta cika wata d'aya tun asubah ya kama hanyar Zaria , karfe shida a k'ofar gidan ta masa, sosai ya ga ta sauya masa, tayi kyau saboda gyaran da aka mata, bayan sun gaggaisa , ya sanarwa da gwaggon na sa abinda ya kawo shi , duk da ya shaida mata tun jiya, tana son zama da d'iyarta amma kuma aure ya raba su, ita kanta Fatima bata ji dad'i da zasu rabu ba , a haka aka zuba mata kayanta a mota, suka yi sallama da kakannin na ta da mahaifiyarta, tana kuka ta shiga motar shima ya shiga ya ta da ta , bayan ya musu sallama, su ka d'auki hanya sai Kaduna............ Please Share & Comments To be continue................. 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 SHAFI NA 39_40 KADUNA Ko da suka k'arasa Kaduna, gidan Mummy kai tsaye su ka wuce, Fatima jin ta take yi a wata duniya ta dabam , ko a mafarki bata tab'a kawo Mummy a matsayin wadda suka had'a dangantaka da ita ba, har su ka Shiga gidan , bata sani ba sai da Ahmad ya d'an bubbuga jikin kujerar sannan tayi firgigit ta dawo daga tunani" sai ki fito in kingama tunanin ", yayi murmushi ita ma murmushin tayi sannan ta fita. A falo su ka tarar da Mummy , mamaki ne ya kamata , lallai Ahmad yanzu sai da ya je ya d'auko ta, ai ita tama manta yau ne ranar dawowar fatiman kai yaran yanzu ma sai dai a barsu kawai, gaisheta su ka yi ta amsa , sannan ta tambayeta mutanen Zaria , nan su ka shiga hira,Mummy ce ta kalli Fatima , "am daughter ki gama shirinki goben Allah ya kaimu , zaki tare a gidanki dan haka ki gama shirya komai", da " toh , kawai ta amsa , a sanyaye sannan ta tashi "Mummy bacci zanyi ", " OK , je ki kwanta nima bari na shiga d'aki ", da toh ta amsa sannan ta nufi d'akinta , ita ma Mummy haka. Ahmad su ka bari a falo , yana ganin Mummy ta shiga d'aki yayi zuruf , kamar wani b'arawo ya nufi d'akin Fatima, a hankali ya tura k'ofar d'akin , tana kwance tana niyyar yin bacci, da yake ta juya bata ji shigowarsa ba , jin an zauna a gefen gado , tayi tsammanin ma Mummy ce, sai da k'amshin turarensa ya buge ta, sannan tayi saurin juya wa," am yallab'ai , me kake buk'ata, ta fad'a tana k'ok'arin tashi , tunawa da tayi irin kayan da ke jikinta ya sanya ta koma ta kwanta", sai da ya gama k'are mata kallo sannan ya rab'a gefenta ya kwanta, cikin zaro idanu tace " amma fa yau Mummy tana nan ", " ai na sani ba wani abu nace zanyi ba, bacci zanyi " ya fad'a yana k'ok'arin janyo ta jikin shi ," dan Allah yallab'ai Mummy fa tana nan ", " kar ki dame ni " , abinda yace kenan ya rungume ta, ita dai sai rarraba idanu take yi har bacci ya d'auke su , ko da Mummy ta fito ganin baya nan tayi tsammanin ya tafi sashensa , sai ta koma d'aki ita ma domin ta d'an matse bacci. A chan b'angare d'aya , LAILA na hanga a zaune tare da wani saurayi , hannunsu a sak'ale da juna, banji mai suke tattaunawa ba, naga dai sai dariya suke shekawa, wa'iyazubillah , kamar ba matar aure ba, " wallahi Aareef kana ji da ni, irin wannan kyauta haka " , cikin dariya shi ma yace " ai in dai zaki dinga sanya ni farin ciki ba abinda bazanyi miki ba, fatana mu kasance har abada", da k'yar su ka rabu da juna , na nufi gida, sai a yanzu take da
🏠