NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 31 of 44

i asibitin . Ko da ya k'arasa , takwas tayi , yana shiga bayan sun gaisa da Mummy , Fatima ta gaida shi ya amsa cike da murmushi a fuskarsa, sannan ya mata ya jiki ta amsa da sauk'i , ya juya hankalinsa gaba ki d'aya wajen mahaifiyar ta sa," hajiya, ya kira sunanta , kasancewar indai zai yi mata maganar da take da muhimmacine haka yake kiranta, amsawa tayi sannan ya kamo hannunta " inason a d'auramin aure da Fatima kuwa ba tare da kowa ya sani ba , zaro idanu Fatima tayi haka ma Mummy, sannan ta ce............. Please Share & Comments To be continue........ 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 FANS DAN ALLAH KUYI MIN HAK'URI, BISA GA JINA SHIRU NA KWANA BIYU , WANNAN DALILIN YA SAMO ASALI NE SABODA INA BUSY , AMMA INSHA ALLAHU NA DAWO DA K'WARINA , LUV U ALL MY FAN'S😍😍. SHAFI NA 33_34. Mummy ce ta kalle shi had'i da fad'ar" lafiyarka kuwa Ahmad , wannan wacce iriyar magana kazomin da ita ne wai , ta fad'a tana kallonsa da son jin dalili", sunkuyar da kansa yayi k'asa ya kasa cewa komai , ganin haka ya sanya mummy sassauta murya saboda ta gane fushi yayi," haba son ta yaya za'ayi wannan d'anyen aiki baka ga abinda ya faru ba da matarka da daughter, son Fatima yarinya ce, bazata iya kishi da LAILA, kuma ko ba haka ba Fatima makaranta take zuwa , yanzu ta soma karatunta kana ganin in aka katse ta anyi mata adalci, tambaya tana jiran ya bata amsa"," Mummy ni dai kawai hakan nake so kuma bana San a d'auki lokaci mai tsawo nan da wani satin in Allah ya kaimu ya kama ranar juma'ah kenan", mummy ce ta dube shi , har cikin ransa da gaske yake ya sanya ta saukar da murya naji NA amince , amma da sharad'i za'ayi bikin amma nan da wata d'aya tunda ka matsu ayi a hakan", Fatima dake zaune jin abinda mummy ta fad'a sai da cikinta ya bada wata k'ara k'uuuuuuu , shikenan za'a kasheta da ranta ya zatayi kenan , kamata yayi ace tun kafin ayi auren nan ta samu ta fece, duk da son da mummy take mata ya kamata ace ta barta ko ba dan komai ba sai son tasan halin LAILA, a yanzu ma da ta gansu a tare ta fara sabauta mata rayuwa ballantana kuma ace ta auri mijinta ai shikenan kuma sai dai ta kai ta lafiya, tana cikin tunanin nan taji Mummy na kiran sunanta , cikin sanyin murya ta amsa. " ina fatan hukuncin da muka yanke yayi miki,mummy ta fad'a tana kallon Fatima da son jin me zata fad'a", Fatima tsintar kanta tayi da amincewa Mummy ba tare da ta San ta amince ba , murmushi mummy tayi , a gaskiya har cikin ranta ta aminta da Fatima , kuma tasan zata yiwa yaran d'anta tarbiyya, shi kuwa Ahmad da ke zaune sosai ya shagalta da kallon Fatima, sosai yarinyar take burgeshi, shi kad'ai sai kaga yana murmushi , mummy ce ta taimaka mata ta yi wanka ta gyara jikinta sosai a gurin cin abinci ne ta so tayi gardama , amma da Ahmad ya had'e fuska ya koma yallab'ai na asali, sai ta amsa ta fara ci sai da taji kamar zatayi amai sannan ta jijjiga kanta hakan ya sanya mummy ta k'yaleta, ganin da mummy tayi kamar Fatima na jin bacci ya sanya ta taimaka mata ta gyara kwanciyarta ba dad'ewa kuwa baccin ya kwasheta , su kuma suka ci gaba da tattaunawar bikin, nan Ahmad ya shaidawa hajiya ai LAILA tana gidansu , sosai ta nuna b'acin ranta akan haka , tace ya je ya taho da matarsa, ya fad'a mata bai ma San ta tafi ba jiya ne bai ganta a gida ba da ya koma , amma zai je ya dawo da ita, ya kuma sanarwa da hajiya Dan Allah ayi komai cikin sirri, wannan kenan. A chan b'angaren LAILA kuwa , sun barbaje a falo ita da k'awayenta duniya ta koma mata sabuwa, ba abinda yake damunta, duk inda taga damar zuwa babu mai hana ta , hakan ya sanya take cin karenta babu babbaka, wata wadda suke kira da woman leader ce ta dubi LAILA a yatsine" wallah babbar hajiya kina bani mamaki , kamar ba LAILA ba, y'ar k'walisa, ki tsaya namiji yana b'ata miki rai, in nice ai wallahi sai na barshi , ko da shine autan maza"," ki kyaleta abinda nakeso ta gane kenan amma tak'i ta fuskanta , Aliya fire ta fad'a tana kallon LAILA", "yanzu toh me kuke son nayi , LAILA ta tambayi su Aliya fire, " ki rabu dashi kawai kizo a kwashi rabo da ke, Aliya ta kuma fad'a "," a'a inason mijina bazan rabu da shi ba gaskiya , amma nasan me zanyi ", Aliya naga ta tashi ta zagaya wajen LAILA ,suka gama maganganunsu ban dai san me ta fad'a mata ba , suka kwashe da dariya , su ka tafa harda woman leader, sannan su ka cigaba da hirarsu a haka mummyn LAILA ta sauko , aka cigaba da hirar da ita . BAYAN SATI 1 Alhmadulillah, bikin Fatima yayi sauk'i sosai sai abinda baza'a rasa ba, zaune su ke, likita ya shigo ya duba ta , sannan ya sanarwa da mummy dama yana son sallamarsu ne tunda mai jiki Alhamdulillah ta warke, nan ya basu sallama , mummy ta kira Ahmad yazo ya d'auke su ya mayar da su gida , ko da suka koma sosai Fatima ta gasa jikinta da ruwan d'umi , tayi wanka , abinci taci kad'an sannan ta kwanta bacci kasancewar tana fashin sallah . A chan fa
🏠