NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 30 of 44

n ciwon kai, sakamakon kofin da LAILA ta buga mata a tsakiyar kanta, sai da suka gama yi mata duk abinda ya dace kama daga wanke ciwo, suka d'inke mata wajen, lokacin da suka gama , su ka mata allurar bacci sannan suka fita, Ahmad da ke zaune, yayi zurfi a cikin tunani, wanda doctor na ta yi masa magana amma ya zurfafa sosai a cikin tunanin irin hukuncin da zai d'auka akan LAILA , tunanin da ya fad'o ma sa a rai ne ya sanya yayi murmushi Wanda ya fi kuka ciwo , toh fa fan's d'in yallab'ai gare ku, dan Allah Ku bincika mana me yake shirin k'ullawa😁😁, sai da likitan ya data shi sannan firgigit ya juya " doctor ya jikin na ta, ta samu sauk'i ko ya ya, ya yiwa likitan tambaya biyu a lokaci guda", " Alhamdulillah, tana lafiya, ta farfad'o zaka iya shiga domin ganin ta, amma dai ta samu bacci ya d'auke ta sakamakon allurar baccin da muka yi mata, Allah ya k'ara kiyaye wa", da amin ya amsa, sannan ya juya ya shiga d'akin da sallama a bakinsa, a kujerar da ke cikin d'akin ya janyo had'e da zama kusa da gadon, tana kwance , fuskarta tayi fayau da ita, hannunta ya kama ya murza a hankali , " Fatima ni ne sanadin fad'awarki a cikin wannan halin , ta ya ya zan iya yafewa kaina , a dalilina a karon farko kika kusan rasa rayuwarki, yanzu a dalilin mata ta, marar kan gado gaki cikin wani halin mai wuyar sha'ani, Fatima inaso rayuwarki ta zamato abar sha'awa ga kowa ta yadda duk wwanda ya kalleki bazai miki kallon k'ask'anci ba amma na gaza samar miki da farin cikin , ni wanne irin mutum ne wane iri ne ni, kuka ne yaci k'arfinsa bai ida k'arasawa ba, tashi yayi da ya tuna da cewar wayarsa na waje cikin motarsa, kuma bai sanarwa da Mummy halin da ake ciki ba , waje ya fita ya nufi motarsa , ko da ya d'auki wayar missed calls ya ganin rututu , yana duba wa ya ga Mummy ce, da hanzari ya d'auka dan yabi kiran sai ga wani kiran ya shigo , d'aga wa yayi had'i fad'in " Mummy LAILA ce , LAILA ce Mummy , fashewa yayi da kuka hakan ya razana hajia Amina ba kad'an ba" saurara Ahmad kamin bayani yadda zan fahimta, mai ya samu LAILAN, ta tambaya cike da zumud'in jin meke faruwa" , tsagaitawa yayi da kukan sannan ya zayyane mata duk abubuwan da su ka faru , salati Mummy ta sa ka sannan ta tambaye shi asibitin da suke , ya fad'a mata ta ce gata nan zuwa, da toh ya amsa ma ta sannan ya koma cikin asibitin. A b'angaren LAILA kuwa , ko da daddynta ya dawo , Mummynta ta sanar da shi , sosai ransa ya b'aci ita ma da yake uwar tsohuwar banza ce sai da ta k'ara da ta ta k'aryar bayan ta y'ay'an na ta, sosai ya yarda akan cewar LAILA ta zauna a gida , da shi a nashi ra'ayin ma Ahmad ya sakar masa yarinyarsa, ta yaya zaace yarinyar bata da ikon wata yawa a gidan aurenta said ya saka mata takunkumi, ganin LAILA ba ta yarda da cewar a sake ta ba ya sanya suka hak'ur, amma da sharad'in sai yaje da kansa shi Ahmad d'in sun ja masa kunne akan y'arsu, uhmmmm ayi dai mu ganu in tusa zata hura wuta😙🤨. A chan b'angaren Mummy kuwa sai da ta gama kammala komai da zaa buk'ata a asibitin kama daga kayan sanyawar Fatima abinda duk tasan d'iyar ta ta zata bukata, sai da ta d'aukar ma ta sannan ta shiga mota direba ya ja su ka nufi asibitin . ASIBITI Ko da su Mummy su ka k'arasa , a harabar asibitin su ka tsaya, waya ta masa , sanan ya zo ya tafi da su d'akin da Fatima take, sai da Mummy tayi kusan awa biyu sannan Fatima ta farka, da addu'ah a bakinta, fara tariyo abubuwan da suka faru tayi , k'wallace ya shiga zubo mata a kumatu , duk ta sanadin KISHIYAR UWA rayuwa ta take tangal tangal , duk da ina tunanin na samu hutu na gudo daga azabarta ashe ba haka bane ba , muryar Mummy da ta ji ne ya sanya ta saurin goge hawayen fuskarta ta k'ak'alo murmushin da yafi kuka ciwo , " sannu kinji daughter, Allah ya k'ara sauk'i , Allah ya baki lafiya ," da amin kawai ta amsa , ta koma ta lumshe idanunta , sai wajen sha biyu sannan Mummy ta sanarwa da Ahmad ya tafi gida ita zata kwana da Fatima , da yaso yayi musu amma kuma , sai ya kyale, ya shiga mota ya nufi gida. Mummy ce ta taimakawa Fatima tayi shirin bacci , sannan ita ma tayi , Fatima da tuni bacci ya d'auke ta , mummy ta tsaya kallonta lallai yarinyar tana cikin jarabawar rayuwa, kuma Allah kad'ai zai fitar da ita , k'ura mata idanunta tayi, Allah ya sanya hasashen da take yi akan Fatima ya kasance gaskiya ne amin, toh fa mummy ya ya dai wanne hasashe kuma🧐, ganin baccin Fatima yayi nisa ya sanya ita ma mummy ta nemi wajen kwanciya. 1:30am Har a lokacin ya gaza runtsawa , tunani fal ya cika NASA k'wak'walwa da zuciya, wallahi ba shakka sai LAILA ta game kurenta shi kad'ai yasan ko wanne hukuncin ya tanadar mata, zata gane tayi kuskure babba a rayuwart, sai wajen k'arfe uku na dare sannan bacci b'arawo ya sace shi , da zumud'in ganin gari ya waye, domin sanar da Mummy shawarar da ya yanke akan al amari. Washe gari ya so ya d'an makara dan sai 6: 15 am ya tashi a bacci, da sauri ya tashi yayi dallah , saboda makarar da yayi , bayan yayi wanka ya shirya , sannan ya nuf
🏠