a tafi gida , kawartace ta fara shiga gida , sannan ta wuce daf da zata shiga yayi saurin shan gabanta tsaya mana tun daga nesa nake kiranki baki juyo ba danAllah Ado ina so na shiga gida inna na jirana , ai da saninta nazo wajenki dan nazo tace bakya nan kina dandali, eh ta amsa masa, amma yanzu zan shiga gida sai da safe saurin janyo mata hannu yayi kara ta saki sannan ta gartsa masa cizo ta shiga gida , kudin tallan ta bata sannan ta ci abinci ta shiga dakin mahaifiyarta wanda ya ratattake saboda asabe ta hana a gyara shi, kwanciya tayi a kan tabarmar kabar dake dakin , tunani ta fada yi shin ina zata ga dangin mahaifiyarta batasan mahaifiyarta ba gashi mahaifinta har yau bai fada maka tayaya akayi mahaifiyarta ta gujeta ba , hawayene ya zubo mata sakamakon tuna irin rayuwar da take ciki shin yaushe zata fita daga rayuwar da take ciki ita dai tun iya tashinta a haka ta taso ta ganta cikin wahala , Allah ya mata magani kawai a haka bacci mai nauyi na gajiya ya kwasheta ta niyyar tashi da wuri saboda tana da niyyar zuwa makaranta kota halin kaka ne , shiyaga take da niyyar yin aikinta da wuri ta gama a haka har asubah tayi ta tashi saboda ta saba tashi ta yi aiki sosai ta kammala kamin ta gama komai tayi sallama da mahaifinta tayi hanyar makaranta.
*Please๐๐ฝ*
*Share*
*Comments*
To be continue
๐ฟ๐ฟ๐ฟNussad๐ฟ๐ฟ๐ฟ๐ฟ
๐ธ๐นKishiyar uwa๐น๐ธ
(True life story).
๐Daga alk'alamin Nussad๐ธ.
๐๐๐๐๐๐๐๐
*๐โจMOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION๐โจ*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*```We are the moonlight writers we shine all over the world.``๐`* โ๏ธโ๏ธ
ุจูุณู ุงููู ุงูุฑุญู ู ุงูุฑุญูู
~~~~~~~๐๐~~~~~~~
Godiya ga Allah subahanahu wata'ala , da ya bani damar ci gaba da rubutun littafina wato kishiyar uwa .
Ina matukar godiya a gareku masoya na musamman na cikin group nawa na what's app da kuke ta nuna kulawarku ga rubutu na nagode .
Ina matukar godiya ga mahaifana da 'yan uwana da suka goya min baya wajen karfafa min gwiwa wajen yin rubutu na , na gode.
Shafi na 2๏ธโฃ
Bayan ta isa makaranta a lokacin karfe takwas na safe , dan haka tana Shiga ajinsu ta nufa , da sallama a bakinta kana ta samu wajen zama ta zauna saboda a lokacin malaminsu bai karaso ba .
Sunyi kamar zaman mintuna biyar sai ga malaminsu na English ya shiga , bada bata lokaci ba ya shiga yi musu darasi, ya dauki tsawon mintuna kana daga bisani yayi tambayoyi aka bashi amsa ya gama abinda zaiyi ya fita.
A haka aka fita break.
Alhamdulillahi kowanne malami ya samu damar shiga ajinsu a haka har lokacin tashinsu yayi sun kammala darasin ranar dan haka kowa ya kama hanyar gidansu .
Tana shiga da sallama a bakinta bayan tayi bankwana da kawarta rahane akan cewa sai sun hadu gurin tallah .
Tana shiga dakinta ta wuce sakamakon rashin jin motsin kowa da tayi wannan ya tabbatar mata daga inna asabe har y'ar lelen tata basa nan dama tasan mahaifinta bayanan yana wajen aikinsa a gona, kayan makaranta ta cire sannan ta hau aikin gida sakamakon anyi kacha kacha da gidan kuma tasan babu mai gyarawa sai ita ta gama sharar tsakar gidan tana shirin yin wanke wanke kwanika taji sallamar mahaifinta alamar ya dawo daga gona , " Baba sannu da dawo wa ta fada tana shirin karbar fatanyar a hannunsa"a'a gidan ba kowane ya tambaya yana sauraron amsar da zata bashi " eh Baba ba kowa , kada kansa yayi sannan ya shige dakinsa ita kuma ta ci gaba da aikinta.
Sai bayan sallar magariba ana shirin yin ishsha'i sannan asabe ta dawo ita da Abu diyarta fagajam fagajam suka shiga gidan ko sallama babu a bakin daya daga cikinsu , a lkcn Fatima har ta dauka tallarta ta fita . " inna ki duba mana abinci mana na kwaso yunwa Abu ce mai maganar cike da raini tana murguda baki alamar 'ya'yan da aka shagwaba aka lalata basu ganin Kimar kowa , " ah bari na duba in shegiyar yarinyar asabe tayi wannan furuci tana niyyar tashi tana dubawa ta tarar har ta gama abincin dan haka suka ci ba ko tunanin yin sallah saboda magariba ma a hanya ta isko su.
Achan dandali kuwa bayan ta karasa ta tarar da kawarta rahane har ta rigata zuwa " Fatima yau kinjima baki fito ba nayi tsammanin ma bazaki fita ba yau , zare idanuwanta tayi alamar mamaki sannan race " chab wallahi aiki na tsaya yi ne shine na dade ban fita amma ina gamawa na fita na samu gidan namu ne ba kowa to na gama aikin ina jiran su dawo ba Wanda ya dawo shiyasa na fita kawai da yake nasan inda kayan tallar suke, suna zaune suna hira har sukayi cinikin gyadarsu sosai kana suka taba wasannin su na yara suka nufi gida.
Rahane ta fara isa gida kafin nan Fatima ta nufi gida kamar kullum Ado ta gani a kofar gidansu " tsaki tayi ta wuce zata shiga gidansu da sauri ya sha gabanta cike da kare mata kallo kana yace " ke wai bakya ganin mutane ne sai kiyi wani fuska ki shige dan kinga an d