mota sannan ya shiga ya tada ya fita daga wajen biki gaba d'aya , ya nufi asibiti hankalinsa a tashe.
B'angaren LAILA kuwa , zube wa tayi a k'asa ta hau rusar kuka, had'e da dana sanin zuwa wajen birthday d'in, Aliya ce ta kamata ta mik'e suka nufi mota , saboda tsabar tashin hankali, ita ta tuk'a motar , yayin da LAILA take ta kuka , su ka fice daga gurin bikin, suka nufi gidansu LAILA , bisa umarnin da LAILA ta bawa Aliyar.............
Please
Share
&
Comments
To be continue..................
🌿🌿🌿 NUSSAD🌿🌿🌿
🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)
🍁 Daga Alk'alamin Nussad🌸
HHHHH WALLAHI KUNA BANI DARIYA , FAN'S DIN LITTAFIN KISHIYAR UWA, HHHHH ALLAH YA K'ARA ZUMUNCI AMIN🤣
🤣😍
BAYAN HAKA YAU YADDA KUKA SANYANI JIN DAD'I , NIMA ZANYI MUKU TYPING SOSAI DA SOSAI, FATAN ZAKU YI ENJOINING SOSAI, LUV U ALL.
NA SADAUKAR DA WANNAN PAGE D'IN GA MASOYAN LITTAFINA NA KISHIYAR UWA
SHAFI NA 31-32
Ko da su LAILA da Aliya suka isa k'ofar gidansu LAILAN, horn sosai LAILA ta shiga dannawa, gateman d'in da sauri ya k'araso ya shiga kiciniyar bud'e gate d'in, kasancewar tsohon ne, hakan ya sanya duk ya rikirkice ya kasa bud'e gate d'in, aikuwa da sauri ta k'araso cike da masifa" dallah malam kana ganin zamu shiga sai wani salo salo kake yi ka gaza bud'ewa mutane, ta fad'a idonta na kan tsohon " yi tayi kamar zata bangaje shi ta nufi cikin gidan tana k'wallawa Mummynta kira, tana kuma rusar kuka, Aliya fire kuwa tana cikin motar a zaune da k'yar Baba maigadi ya bud'e gate d'in ta shiga da motar sannan ya rufe , ta rufawa LAILA baya itama ta shiga cikin gidan.
Chan d'aya b'angaren kuwa, hajiya tana zaune ta rasa inda zata tsoma ranta, gashi tayi kiran duniya Ahmad baya d'aga wayarta, gashi har k'arfe takwas na dare yayi, zuciyarta sai bugawa take yi da sauri da sauri, hakan ya sanya ta kissima abubuwa da yawa a ranta, shed'an ya dinga yi mata wasi wasi a cikin zuciyarta, gashi ta kuma yi ta d'auka wayarta, i zuwa yanzu ta kira Ahmad ya kai sau kusan ashirin, amma still baya d'agawa, sake kira ta yi a karo na gaba , shi ma baa d'aga ba hakan ya sanya ta nemi guri ta zauna ta zubawa ikon Allah idanu , tana kuma jiran dawowarsu a koda yaushe.
A b'angaren su Fatima kuwa, da gudu ya dinga tafiya kamar zai tashi sama, gani yake yi kamar ma yarinyar bata numfashi, hakan ya sanya ya k'ara k'aimi a tafiyar ta sa , yayin da hannunsa ke sak'ale a cikin na ta, ji yake yi Kamar ya zunduma ihu, amma ba shakka ya na kukan zuci , ya zaiyi idan aka ce yarinyar nan ta rasu, ina zai sanya rayuwarsa yaji sanyi lallai bazai yafe wa kansa ba, lallai idan har yarinyar nan ta rasa ranta ta dalilin LAILA wallahi sai yayi shari'a da ita , ko da duk abinda ya mallaka zai k'are ne ,a haka ya dinga tunani har ya k'arasa cikin asibitin, wanda da taimakon Allah ne kawai ya kai shi , nan wani asibiti mafi kusa ya kai ta saboda yana ganin idan har ya kai ta asibitin su Dr Sadiq lallai kafin ya k'arasa zata rasa ranta, ko da suka k'arasa , ganin irin ciwon da ta ji , jini duk ya b'ata mata jini, ya sanya likitocin suka ji tsoro, suka k'i karb'arta , sai da y'an sanda, hakan ya sanya ba shiri ya je police station mafi kusa da asibitin ya taho da y'an sanda guda biyu , suka yi cike cike sannan likitocin suka shiga da ita domin ganin ta hayyacinta, shi kuma ya nemi guri ya zauna, ya had'e kai da gwiwa yana sauraron hukuncin doctor d'in.
Tun daga tsakiyar falon ta fara kiranta, cikin k'araji, Mummy! Mummy!Mummy!, haka ta dinga k'walla mata kira, cikin sassarfa ta k'araso, " ke me ya faru na ganku haka, ta fad'a tana duba LAILA, wadda ta fad'a jikinta , fashewa tayi da kuka kamar hakan ya k'ara tayarda hankalin Mummyn ta ta, ganin ba zata ce komai ba ya sanya ta juyata kalli Aliya" Aliya lafiya kuka shigo a hanrgitse , ta tambaya tana jiran amsarta, " k'arasawa Aliya fire ta yi ta fara zayyanewa Mummy k'arya da gaskiya, wani uban ashar da Mummy ta yi sai da LAILA ta d'ago da sauri ta kalle ta, cike da hargagi ta ke fad'in " lallai Ahmad ya cika cikakken marar mutunci, yanzu amma ke kina cikin wannan halin baki sanar da mu ba , wallahi ba abinda zai sanya ya dakeki ya zauna lafiya , sai munyi k'ararsa kotu , da k'yar su Aliya suka rarrashe ta, ta hak'ura , bayan tasha al washin sanar da mahaifin LAILA in ya dawo daga, tafiyar da yayi ita kuwa LAILA ta k'udurta a ranta sai ta ga bayan Fatima ko ta halin yaya ne ,Mummy ce ta kwantar mata da hankali, kasancewar tace mata zata d'auki mataki akan Ahmad dama kanta ita Fatiman , hakan ya sanya LAILA ta ji sanyi a ranta , da kuma ta tuna yanzu fa tana gida zata ci karenta babu babbaka, ni kuwa na ce sai ki taci ai bazai wuce tafiya yawo ba ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta😏😚, sai da suka kwantar mata da hankali , sannan suka tsunduma hirar duniya.
ASIBITI
Sai da likitocin da nurses d'in suka kwashe wajen awa d'aya da rabi akan Fatima , sannan ta farfad'o da wani matsananci