nnan ya k'arasa ficewa, ko da su ka k'arasa bakin motar da kanshi ya bud'e mata sannan ta shiga , shima ya zaga ya shiga su ka bar gida bayan gateman ya bud'e musu gate.
A chan b'angaren LAILA kuwa, tana zaune a falonta ita da k'awarta Aliya fire, cike da jin haushi Aliya ta dubi k'awarta ta " ni wallahi kina bani haushi, ta ya ya kawai daga ce miki , kar kije sai ki zauna yayi ta juya ki , wallahi ni banga namijin da zai juyani kamar waina ba, ta k'arashe maganar cikin masifa", LAILA kuwa sai kallonta take yi yayin da maganganunta su na k'ara shigarta," kinga Aliya bari naje nayi wanka na shirya, ai wallahi baza'ayi babu ni ba, haka kawai jirani in zo mu tafi , LAILA ta fad'a had'e da mik'ewa tsaye tana k'ok'arin hawa up stair na gidan da toh Aliya ta bi ta sannan ta d'auko wayarta ta fara kiran k'awar ta su wadda ta gayyace su birthday, domin ta sanar da su LAILA zata samu damar zuwa, ita kuma LAILA ta k'arasa hayewa saman benen.
A chan b'angaren su Fatima kuwa, sai da suka yi tafiyar kusan minti talatin ba tare da kowa ya cewa d'an uwansa komai ba, chan Fatima ta dubi yallab'ai da ke aikin tuk'i " uhmmm wai har yanzu ba'azo ba , ta fad'a kamar ba ita tayi maganar ba ", " siyar da ke zanyi abinda yace kenan , yana k'ok'arin shigar da motarsa cikin wani katafaren wajen shak'atawa, da idanu kawai take bin wajen ba dai tsaruwa kam , kamar rak'umin da akala haka take bin sa, har su ka k'arasa wajen wani taro daga gani na manyan masu kud'ine a d'aya daga cikin jerin kujerun su ka zauna, kujerar d'an uwansa tana kallonsa, anyi decoration na k'ayatarwa a wajen , abokan nan Ahmad wad'anda su ka zo taro bikin zagayowar ranar haihuwar matar d'aya daga cikin abokinsu mai suna Muhammad lawan, ko wanne yazo suna gaisawa da Ahmad, suka dinga yi mishi tsiyar wai ya k'ara aure bai fad'a musu ba shi dai kawai dariya abin yake ba shi , sannan ya sanar da su ai k'anwarsa ce, a haka su ka dinga hira sosai Fatima ta bi dad'in had'uwa da wad'annan mutane masu karamci .
A chan b'angaren su LAILA kuwa, sosai su ka gama shiryawa, cikin wani hamshak'in leshi , mai tsananin kyau ta sanya , ta sha uban takalmi mai tsini ta sanya siririn mayafi, k'asa ta sauka ta tarar da Aliya na zaune, kod'ata ta farayi sannan ta shiga d'aukanta a photo , sosai tayi ma hotuna , sannan su ka shiga mota suka nufi wajen birthday partyn .
Sai da su kai kusan minti talatin , sannan suka k'arasa wajen , parking d'in motar LAILA ta yi, sannan suka nufi k'ofar shiga, a chan b'angare d'aya suka zauna , su ka fara hira da k'awayensu, chan wadda ake yiwa birthday d'in mai suna Ramlat ta k'arasa wajen su LAILA, da fara'arta ta isa wajen gaisawa su ka yi , sannan ta umarci LAILA da ta taso su gaisa da mijinta , da kuma babban amininsa , cike da karairaya ta tashi su ka nufi wajen domin gaisawa.
A b'angaren Mummy kuwa , shiru taji dan haka ta tashi ta shiga safa da marwa a falon , wayar ta ta d'auka ta shiga kiran Ahmad, amma me bai d'auka ba sosai hankalinta ya tashi , ta zauna ta shiga zaman jiran dawowarsu.
A b'angaren LAILA kuwa, tun daga nesa ta hango abokin mijin k'awarta ta , wanda take wa kallon kamar mijinta Ahmad , amma kuma ai wannan tare da kyakykyawar yarinya balarabiya ta ganshi, ni kuwa nace toh su LAILA an fara tsufa kenan๐, tana k'arasawa tana ganin kamanin wannan mutumin yana k'ara yi mata kamanin mijinta, sai da ta k'arasa wajen suka gaisa da mijin Ramlat, Ahmad da ke zaune kawai ya kalli LAILA k'warai ba zargi yakeyi ba LAILA ce matarsa , kawai kafe ta yayi da idanu, yana kallon ikon Allah , yanzu wannan itace matar da yake aure marabarta da masu zaman Kansu kawai d'aurin igiyoyin aurensa da ke kanta, ita kuwa LAILA jin kamar ana kallonta ya sanya ta juya domin ganin wake kallonta, k'walalo idanunta tayi sannan ta zunduma wani uwar ashar tare da fad'in " me zan gani , Ahmad wannan wacece a tare da kai , ta fad'a tana nuna Fatima ", sosai tsoro ya kama Fatima tayi wuri wuri da idanu, aikuwa jin sannan zagin ya sanya mutane suka jiyo suna kallonsu, ganin haukan da LAILA keyi ya sanya Ahmad ya daka mata tsawa , " aikuwa tayi ta kuwwa tana zagi , tana kururuwa, " Fatima koma chan kije ki zauna, ya fad'a yana nuna mata wajen zama", ai LAILA tana ji ta zunduma ihu , " shegiya , matsiyaciya , tsohuwar karuwa , wai dama kina mak'ale da mijina ban sani ba", ta fad'a had'e da janyo Fatima , ta wanchakalar da ita a gefe , kafin Ahmad ya zo ta kwashe ta da wani gigitaccen mari, juyawa tayi ta d'auko wani kofin tangaran ta sauke mata shi a kai , k'arar da Fatima ta saki ne ya janyo hankalin mutane dama shi kansa Ahmad d'in , akwai cikin hanzari , ya k'araso wajen ya wanke LAILA da wani azababben mari , wanda sai da taga taurari, kuwwa ta sake saki tana k'ara lalubar Fatima dan ta k'ara yi mata wata illar , k'ara kifa mata mari yayi, ya warb'ar da ita gefe, ganin Fatima tana kwance kamar ba rai a jikinta , ga jini da ya dinga zuba , aikuwa da sauri ya k'arasa wajen ciccib'eta ya nufi mota yana haki , saka ta yayi a