a kallon Fatima kasancewar tayi girma, shi fa mamaki yake yi yadda ta zama cikakkiyar budurwa, Allah ya taimake shi ya k'ara dawo mishi da ita a karo na biyu, sosai ya ci abinci , sai da mummy ta tursasa masa sannan ya hak'ura ya nufi gidansa cike da farin cikin ganin Fatima.
Ko da ya k'arasa, cike yake da farin ciki, sama ya haura ya nufi d'akin LAILA, a kwance ya same ta a lokacin anyi sallar isha'i shiga cikin band'akin ta yayi, da idanu ta bishi sannan ta juya ta ci gaba da charting d'inta, fitowa yayi ya mata magana akan anyi sallah , nuna masa alamar zatayi tayi da kanta , shi kuma ya juya ya fita ya nufi masallaci.
A chan b'angaren Fatima , sosai ta shagalta da tunanin malamin na ta , kuma yallab'ai, lallai ya mata halarci, bayan ya tsaya mata a rayuwarta ta baya sannan yanzu ya mayar da ita y'ar dangi , ita kam dame ma zata saka mishi ne wai, tambayar da ta gaza amsawa kenan ta kwanta bacci aikuwa ba dad'ewa ya d'auke ta, cike da murnar ganin malamin na ta a karo na biyu.
Shi ma a nashi b'angaren, sosai ya gaza yin bacci , domin tsabar farin ciki, da ganin d'alibar ta sa, sai chan dare ya kwanta, LAILA ta yi mamakin ganin na sa , a cikin farin ciki amma kasancewar ta mai da damuwar wani ba na ta ba, ya sanya ta k'yaleshi kawai , a haka su ka yi bacci.
To fa shak'uwa sosai ta shiga tsakanin yallab'ai Ahmad da kuma Fatima , kullum zai zo in ya dawo daga aiki , ya zauna yayi ta tambayarta labarin bayan rabuwa, ita kuma tana bashi , wani yayi dariya wani yaji tausayinta , shi kansa ya gaza gane kansa game da ita, a farko ya d'auka tausayi ne amma daga baya kuma ya gane soyayya mai k'arfi yake yi mata, chab to fa fans din yallab'ai Ahmad gare ku😍😍.
Ana cikin haka kuma su Fatima suka gama aji biyu, kuma a wannan lokacin zata zana placement, wannan tsari ne daga yallab'ai, an biya mata komai sannan su ka zauna fara exam.
Masha Allahu sunyi exam , kuma Alhamdulillah , sun yi nasara , ita ma k'awarta Halima tare su ka yi , sosai ta yi murna ganin cewar tare zasu ci gaba da Halima.
A chan b'angaren Ahmad , kuwa sosai ya Sanya ayi masa binciken kakanin Fatima anyi sa'ar an samu Wanda ya san kakan nata amma kuma ya tafi fatauci legas sai bayan shekara zai dawo, sosai ya ji dad'in haka, kuma yana yin komai ne ba tare da sanin ita kanta Mummy ba ballantana kuma Fatima.
Achan b'angaren LAILA kuwa sosai hankalinta ya kwanta, ganin mijinta yanzu baya matsa mata wajen hanyar fita, don haka sai ta ranci na kare, kullum bata gida , daga gidan wannan k'awa sai bikin wannan k'awa, ni ko nace uhmmmm su LAILA manya a dai juri zuwa rafi tohm😝.
Suna zaune a falon mummy, Ahmad yana ta satar kallon Fatima, tana sane da kallon da yake bin ta dashi duk ta kasa sukuni , " uhmmmm Mummy please anjima inason daughter ta ki ta rakani unguwa , ya fad'a yana kallon mummy don jin me zatace "," Ina zaku je banason ka koyawa yarinya ta yawo bazata je ba,", " please mummy ba dad'ewa zamu yi ba, da kai ta amsa alamar ta yarda sannan ya juya ya kalli Fatima dake zaune , "ki shirya bayan la'asar , kafin na dawo abinda yace kenan sannan ya juya fita ita ma ta tashi ta shigewarta d'aki domin cika umarnin yallab'ai, kuma malami a gare ta , wato Ahmad............
Please
Share
&
Comments
To be continue.............
🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿
🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)
🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸
KU NA K'ARAMIN K'AIMI FAN'S, INA TARE DA KU NIMA, LUV U ALL 😍😍.
SHAFI NA 29_30
Mummy kuwa, bi Fatima tayi da kallo , tare da wani k'ayataccen murmushi , irin na su na manya wadda ita kad'ai tasan ma'anarsa, sannan ta girgiza kai , ita ma ta mik'e ta shige cikin d'akinta.
A b'angaren Fatima kuwa, tana shiga d'akinta wardrobe ta bud'e, tsayawa tayi tana duba kayan da zata sanya, rasa wanda zata saka tayi , saboda batasan inda za su je ba , sai da ta gama dube dubenta ,har ta mik'e zata kirawo mummy ta taya ta zab'ar kaya kawai sai ta hango wata marron color d'in doguwar rigar abaya , hakan ya sanya ta zaro ta , wadda taji stones kalar gold, sai siririn mayafinta, jaka da takalmi ta zab'o su ma kalar golden da agogo, sannan ta fad'a wanka , ko da ta fito sai da ta gama zafa lotion mai k'amshi sannan ta zura kayan ta yane kanta da mayafin rigar , takalmi ta zura sannan ta rataya jakar ta ta, ta feshe jikinta da turaren "Al' oud Al khalij", sannan ta nufi falon, tana fita yana shigo wa, da idanunsa masu rikitar da ita , a zuciyarsa ya furta masha Allahu , k'arar bud'e k'ofar d'akin Mummy ne ya dawo da shi daga duniyar da ya shiga , sannan ya k'arasa cikin d'akin ya zauna, " Mummy barka da fitowa , ya ce da ita ", sannan ya dubi Fatima wadda ta mak'e a jikin bango kamar zata shige " mu je ko , abinda ya furta kenan sannan ya yiwa Mummy sallama ya nufi hanyar waje" , ganin haka ya sanya Fatima ta bishi cikin hanzari, mummy ce ta musu a dawo lafiya , bayan ta sanarwa da Ahmad kar su kai dare, da toh ya amsa mata sa