ta kora da ruwa, sannan ta nufi d'akin ta .
A b'angaren LAILA kuwa, sai k'arfe biyar ta koma gida , ko da ta shiga , ganin Aisha a kicin tana girkin dare , hakan ya sanya ta tambaye ta ko ya dawo, anan ta shaida mata ai dama bai fita ba, sai bayan ta fita sannan ya fita, kasancewar LAILA y'ar duniya ce hakan bai sanya ta damu ba tayi shigewar ta d'akinta.
Sai bayan sallar isha'i sannan ya koma gida , bayan ya yi musu sallama , ya nufi hanyar gidanshi, ko da ya koma bai nunawa LAILA yasan ta fita ba, har tayi zaton ko Aisha k'arya ta mata , shi kuwa yana sane , amma ya share ta , saboda ya gane bazata shiryu ba, sai wani ikon ubangijin.
Ana cikin haka , aka koma makarantar su Fatima , sosai tayi murna da komawar ta su kasancewar ba wani Hutu ne sosai ba, ko da ta koma yallabai shi ya ci gaba da kai ta makaranta kafin a samu mai kaita , na musamman a cewarsa๐๐ฅด๐ณ.
Ranar Friday misalin k'arfe biyu a lokacin an yi sallah, ya nufi gidan na su, a falo ya samu Fatima ita kad'ai kasancewar Mummy ta fita tun safe, bayan ta gabatar masa da abinci ta juya zata nufi d'akinta , cikin d'aga murya ya kirawo sunanta , chak ta tsaya , " gurinki na zo ba gurin Mummy ba ina son , ki fad'amin gaskiyar ke wacece, saboda ina miki kallon wadda na sani amma kin k'aryata ni, ina jinki bismillah fara ", a sanyaye ta zauna , sannan ta fara bashi labarinta daga farko har k'arshe sannan ta d'ora da cewar ina son nayi karatu mai zurfi, duk da a baya jajirtaccen malamina yaso nayi, amma Allah bai nufa ba", " sannan kuwa wanene , har haka mai muhimmacin da bazaki manta dashi ba , ya fad'a ya na kallonta da son ta ba shi amsa ", nan ta zayyane mishi komai daga bisa tace" har yau har gobe ina mishi fatan alkhairi a rayuwarsa , saboda ya so rayuwa ta da ci gaba, ta fad'a a yayin da hawaye ya sulmiyowa fuskarta", " ko zan iya sanin sunan malamin ", abinda ya ce kenan,"" sunansa malam Ahmad " dam gabansa ya fad'i shikenan hasashen da yake yi ya zama GASKIYA , yau ga Fatima yarinyar da ya tafi ya barota a k'auye cikin wahalar rayuwa , Allah ya k'ara had'a su , yarinyar da tun lokacin da yaje bautar k'asa ya d'aura idonsa akanta yake k'aunar yarinyar tun tana y'ar k'aramar yarinyarta, cikin dashewar da rawar murya ya furta " da.. da....dama kece dama kece Fatima , Allah na gode maka..............
MASOYA YALLAB'AI AHMAD GAREKU๐ฅฐ
Dan Allah a dinga yimin sharing na book d'in nan plz.๐๐ป๐๐ป
Please
Share
&
Comments
To be continue.....................
๐ฟ๐ฟ๐ฟNUSSAD๐ฟ๐ฟ๐ฟ
๐ธ๐นKISHIYAR UWA๐น๐ธ
(True life story)
๐Daga Alk'alamin Nussad๐ธ
๐๐๐๐๐๐๐๐
*๐โจMOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION๐โจ*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*```We are the moonlight writers we shine all over the world.``๐`* โ๏ธโ๏ธ
ุจูุณู ุงููู ุงูุฑุญู ู ุงูุฑุญูู
~~~~~~~๐๐~~~~~~~
INA GODIYA DA IRIN RUWAN COMMENTS DA KUKE TA ZUBA WA , INA JIN DAD'I SOSAI.
INA GANIN ADDU'O'INKU , MASOYA NA DA MA MASOYAN BOOK D'IN KISHIYAR UWA, ALLAH YA K'ARA DANK'ON ZUMUNCI AMIN.
SHAFI NA 27_28
Ita kuwa Fatima, kallonsa kawai ta tsaya tana yi , ta gaza fuskantar kalma d'aya daga cikin zantuttukan da yake yi, komawa tayi kamar wata sokuwa , idanu da hanci ta zuba mishi kawai tana kallon , shi kuwa zuba mata idanu kawai yayi kallon ikon Allah, " Fatima dama kece, dama , daman ni nasan , ina yawan ganin nasan fuskarki, ashe dama kece, Allah na gode maka, ya fad'a yana k'ara kallonta", " kingane ni, ni ne fa malaminki mai k'aunarki , malam Ahmad", da sauri ta d'ago kanta cikin razana da jin abinda yake fad'a, kuma da alama baya cikin hayyacinsa, domin tafi zaton sumbatu yake yi, " yallab'ai wai me yake faruwa ne, ta fad'a kamar zatayi kuka", kallonta ya tsaya yanayi cike da shauk'in k'ara ganinta a karo na biyu, " Fatima dama kina nan , nayi ta Neman ki sak'o da lungu , a lokacin da na dawo daga k'asar waje naso in zo in da kike amma ban samu dama ba , wayyo gsky Allah yana sona " , ita dai tsayawa tayi tana kallon ikon Allah, gaskiya itama tayi ta tunanin inda tasan fuskar yallab'ai ashe shine mutumin da ya zamar mata garkuwa kuma jigo a rayuwarta da karatunta, hawaye taji yana k'ok'arin zuba a fuskarta , saurin sanya hannu tayi ta share hawayen da ya fito ta gefen idonta, " cikin rawar murya ta furta, uncle da..da..dama kana nan a raye, ta tambaya tana kallonsa ", gyad'a mata kai kawai yayi kasancewar ya kasa magana ma, suna cikin wannan yanayin Mummy ta dawo tun kafin ta huta Ahmad ya sanar mata wacece Fatima , sosai tayi mamaki , duk da haka ita ma Mummy na yi mawa Fatima kallon sani , chab k'ak'ak'ara k'ak'a, toh ita kuma mummy me take nufi oho.
Suna zaune a haka har magriba ta k'arato , hakan ya tursasa shi tashi ba dan ya so ba ya nufi masallaci, domin gabatar da sallah , su ma nufar toilet ko wacce tayi domin d'auro alwala.
Bayan sun idar da sallah , shi ma ya shigo , abinci su ka ci sosai ya shagalta d