amma abinda zan iya cewa , akwai sark'ak'iya cikin labarina, ka bari in mun samu lokaci ba school, kazo ni kuma zan baka labarina ", murmushi ya sake yi , a daidai nan su ka k'arasa bakin gate d'in gidan , sun shiga cikin ko gama parkinga bai yi ba ta fita da gudu ta nufi falo da sallama ta k'arasa a lokacin shi kuma ya kunno kai , a cinyar hajiya ta zauna , "wash sai kin karyani , cewar hajiya da take k'ok'arin d'aga ta daga kan cinyarta ", shagwab'e fuska tayi ta turo d'an k'aramin bakinta waje , Ahmad dake tsaye zuba mata idanu yayi abin kawai ya burgeshi , lallai wannan yarinyar shagwab'ab'b'iya ce , hajiya ta mishi magana , firgigit ya dawo daga tunanin da ya tafi , gaisawa su ka k'arayi , a yayin da Fatima tace" mummy wallahi makarantar akwai dad'i sosai bari nayi wanka nazo na baki labari "," to kiyi Sauri ina jiranki, shi kuwa Ahmad rakata yayi da idanu har ta shige d'akinta.
Bayan tayi wanka tayi sallah ta fito ciki Riga doguwa sai siririn hannu , kalar ruwan hoda , rigar ba ta da nauyi , tayi parkinga gashinta da ribom shi ma pink , a kusa da mummy ta zauna ta shagwab'e fuska , ni kuwa nace su Fatima an samu abinda akeso ko da da kike hannu Inna Asabe anayi oho, " mummy yunwa nake ji wallahi", tashi maza kije kici abinci kinsan bana San kina zama da yunwa ", tashi tayi ta nufi dinning area , yayin da Ahmad ya rakata da idanu , ya rasa abinda ke faruwa dashi komai yarinyar tayi abun birgewa ne, " tana da kyau abinda yace kenan ya kautar da kansa gefe guda", da sauri ta nufi wajen zama ta zauna abinci taci sosai sannan ta koma su ka ci gaba da hira , Ahmad bashi ya bar gidan ba sai bayan sallar isha'i.
A b'angaren LAILA kuwa, sosai duniya ta dawo mata sabuwa, saboda sun shirya da Ahmad yadda ya kamata, kuma a nata tunanin ai Ahmad ya mayar da Fatima garinsu , batasan su na tare da mahaifiyarsa ba kasancewar ita d'in ba mai son zuwa gidan sirikarta ta bace ba, sosai hankalinta ya kwanta , takecin Karen ta babu babbaka , hmmmmm hajiya LAILA muje zuwa , mata a gidan Alhaji Ahmad.
A b'angaren Fatima kuwa, sosai ta ke karatun ta cikin hazak'a , kuma halinsu yazo d'aya da Halima, dan a waje d'aya suka bambanta da juna shine , ita Fatima miskilace , while Halima kuma na da surutu da yawa, jarabawar farko , Fatima ta d'auki first class , Halima kuma second class, sosai yallab'ai Ahmad ya ji dad'in haka , yasan kuma ba asarar kud'insa yakeyi a banza ba, kyauta ta musammam yayi mata , kuma had'a mata da waya k'irar IPhone 11 pro, murna sosai tayi , da wannan kyauta bayan sun samu hutu Fatima ta tambayi hajiya kan tanasan taje gidansu Halima , hajiya a barta , ta kuma fad'awa driver ya kaita , sosai su ka yi murna da ganin juna, har k'arfe bakwai , sannan ta koma gida bayan mahaifiyar Halima ta bata kyauta da kyar su ka rasu, ko da ta isa gidan , a falo ta tarar da hajiya da yallab'ai , sannu da gida ta musu sannan ta nunawa hajiya kyautar da mamansu Halima ta mata, ran Ahmad ne ya b'aci au dama fita take yi any how any time , sai da ya bari bari hajiya ta tafi d'akinta sallah , sannan ya kutsa kansa d'akin Fatima a lokacin ta idar da sallar isha'i kenan , fuskarsa babu walwala, " ke dama yawo like zuwa, ya tsare ta da idanu yana jiran amsarta ", sosai ta tsorata , dan haka cikin rawar murya tace" am...am..ba.. ba haka bane ba , wallahi..... ba ta k'arasa ba ya katse ta " kar na k'ara ganin k'afarki a waje kin tafi yawo kinji na fad'a miki ", sannan ya juya ya fita, saboda ranshi ya b'aci ko sallama bai yiwa hajiya ba fice daga gidan ya nufi gidansa, ita kuwa Fatima zama tayi ta fashe da kuka sai da ta yi mai isarta sannan ta yi shirin kwanciya bacci , shi kuwa ko da ya k'arasa gidan ko takan LAILA bai bi ba ya kwanta . amma ne fafur bacci yak'i zuwa, ransa ya kai mak'urar b'aci , minti bayan minti sai ya juya yayi tsaki , to shi menene ma zai dameshi dan ta fita, ni kuwa nace muje zuwa malam yallab'ai Alhaji Ahmad, hhhhhhh. sai da tsakar dare sannan ya samu bacci ya d'aukeshi, bayan ya gama tunane2sa ko na menene oho🥴
A b'angaren LAILA ma gajiya tayi da jiranshi , ganin bai dawo ba sai kawai ta kwanta ita ma , kasancewar ita ba ta damu da damuwar wani ba ta ta kawai ta sa ni.........
DANALLAH A DINGA YIMIN SHARING NA BOOK DIN NAN PLZ👏🏻
Please
Share
&
Comments
To be continue........
🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿
🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)
🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸
CHAB ANA WATA GA WATA GASKIYA BAZAMU LAMINTA BA ACE KHAF BABU MASOYAN LAILA INA, AI MU GASKIYA MUNA BAYAN LAILA 100%.
HMMM SISTER BABU RUWA NA IN KIKA HAD'U DA FANS D'IN FATIMA , ZAKIYI BAYANI🥴😝
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
SHAFI NA 25_26
Washe gari da safe ko fitowa