i jaririn d'anta namiji Wanda yaci sunan Ahmad, sosai ake nunawa jariri gata da soyayya , musamman Maimunatu k'anwar hajiyan, Ahmad ya tashi cikin gata , shekarar goma a lokacin ya gama primary zai tafi secondary akayi auren k'anwar hajiya wato Maimunatu , aka kaita garin kano, sosai basu ji dad'in rabuwa da juna ba amma ba yadda suka iya, haka suka hak'ura.
Ajin Ahmad biyu a secondary , Allah ya azurta Maimunatu k'anwar mahaifiyarsa da samun k'aruwar yarinya mace hakan yayi masa dad'i sosai ganin cewar dama bai tab'a zuwa gidan gwaggon ta sa ba, amma kash lokacin yazo musu ana dab da fara jarabawa , haka ya hak'ura , ya gama makarantar secondary da kwali mai kyau , a lokacin business din mahaifinsa ya bunk'asa dan har k'asar waje yake fita , a haka Ahmad ya fara makaranta , toh a wannan lokacin Allah ya had'a shi da LAILA, y'ar gidan Alhaji Abbas mai dollar , tunda LAILA ta d'ora idanunta akan na Ahmad , taji ta kamu da sonsa, tun baya lura da ita har sai da tasan yadda akayi ta cusa masa soyayyarta a zuciyarsa , sunyi soyayya sosai , a lokacin da iyayensu suka sani abin ya musu dad'i sosai ganin ko wanne a cikin yaran nasu daga babban gida ya fito , a wannan lokacin kuma Ahmad ya tafi bautar k'asa a wani k'auye a kano cikin k'aramar hukumar takai , bayan ya gama bautar k'asarsa ne aka d'aura musu aure kuma ya tafi da LAILA k'asar wajen domin k'aro karatun na sa, a farkon aurensu sosai LAILA takeyi mishi biyayya , sun zuba soyayya amma daga baya kuma sai abin ya chanza salo rashin mutunci sosai ta farayi masa , ya rasa gane kanta , a iya saninsa LAILANSA bata da mugun hali amma ya akayi ta fara nuna masa wani hali na daban, babbar matsalarsa guda d'aya itace ta rashin haihuwa , da farko ya zaci yana da matsala amma da akayi masa bincike aka gano ai lafiyarsa k'alau , yayi nacin duniya LAILA taje a duba ta amma tace ita ba inda zataje ai haihuwa ta Allah ce, baisan da gangan LAILA take shan magungunan hana d'aukar ciki ba , bayan tabi shawarar k'awayenta , su Aliya fire, lokacin da ta sanar dasu tana da ciki suka ingizata ta zubar da shi a cewar su wai zata tsofe da wuri , tun daga nan take amfani da maganin hana d'aukar ciki , Allah sarki ko shi Ahmad d'in baima San tayi cikin ba kuma an b'arar masa da abinda yake nema ido rufe, a haka suka yi shekarun da zasu yi su ka dawo Nigeria , ko da suka dawo yaso su zauna a gidansu amma tace ita za'a takura mata , haka bada yaso ba ya gina musu gida , a wannan shekarar da su ka dawo , Allah ya yiwa mahaifin Ahmad rasuwa sunji rasuwar ba kad'an ba amma daga baya su ka hak'ura suka dangana , su ka ci gaba da rayuwa ,Ahmad kuma ya ci gaba da kula da kamfanin nikan da mahaifinsa ya rasu ya bar masa.
CIGABAN LABARI.
Ranar litinin da wurwuri Fatima ta shirya , domin tun dare hajiya ta sanar da ita cewar da safe , yayanta zaizo ya kaita makaranta , dan haka kafin k'arfe bakwai ta gama shirinta tsaf , tana jiransa , a bakin k'ofar falo su ka yi kicib'us lokacin ya shigo ita kuma zata fita , da sauri ta dafe k'irjinta tsabar tsoro dan bata zata shi bane ba, " yallab'ai ina kwana , ta fad'a tana dubansa ", shi kuwa lulawa yayi chan duniyar tunani , ya'akayi yarinyar nan ta girma , to kwata2 kwana nawa rabona da ita , ko da yake dama wahala ce kuma tana sanya haka, " yallab'ai fa ina gaisheka ," sai a sannan ya farga sannan ya amsa , tambayarta yayi ina hajiya ta fad'a masa tana cikin d'aki , juyawa yayi yana tunanin girman da Fatima tayi a k'ank'anin lokaci, gashi kayan makarantar sun amsheta gaba ki d'aya kayan maroon colour ne amma rigar tasu mai gida gidan bak'i a jikinta , kuma hijjabin d'an karamine dan da kad'a ya haura k'asa k'irjinta,da sallama a bakinsa , sun gaisa da hajiya , ya fad'a mata zasu wuce makaranta zai kai Fatima, sosai ta musu addu'ah sannan su ka fita daga cikin gidan bayan sunyi sallama da Fatima, toh a hanya sosai su ka yi hira , har ya dinga mata tambayoyi tana bashi amsa daidai ," am ni kuwa Fatima har yau bansan labarinki cikakke ba , ko za'a taimaka a bani nasha", ya tambaya yana murmushi , sosai ta shagala da kallonsa, har sai da ya juyo ya kalleta sannan ta sunkuyar da kai tana murmushi, shima murmushin yayi , dab da sun k'ara bakin gate d'in makarantar , anyi mata cike cike da komai na sabon d'alibi , sannan aka bata aji , shi kuma Ahmad ya tafi wajen aiki.
Koda aka kai ta a desk din da aka ajiye ta su biyu ne," sannu ta cikin bencin ta fad'a", " yauwa sannu" ," suna na Halima Nasir, nice too meet you", ni kuma suna na Fatima Iliyas ", murmushi ta mata sosai suka yi hira , a rana ta farko su ka shak'u ko da aka tashi , Halima taso su kai Fatima gida kasancewar yallab'ai Ahmad bai zo ba amma Fatima ta sanar mata yayanta zaizo d'aukarta, ilai kuwa suna tsaye ya k'araso sallama sukayi kowa ya nufi wajen Wanda yazo d'aukarsa , a hanya sosai Fatima ta saki jikinta da Ahmad ta dinga bashi labarin makarantar da sabuwar k'awarta da tayi, shi kuwa ba abinda yakeyi sai murmushi, " to kince zaki bani labarinki ko ba yanzu ba", " zan baka