ma a yau , amsawa yayi da to , suka yi sallama , da sauri ya Shiga toilet yayi wanka , kasancewar yayi sallar asubah , k'asa ya nufa a tare ya ga Aisha da Fatima suna hira a tare suka had'a baki burin cewar " yallab'ai ina kwana " amsawa yayi sannan ya nufi dinning area sosai yaci abinci , sannan ya yiwa Fatima nuni da ta taso su tafi , Aisha bataji dad'in tafiyar Fatima ba , ita kuwa Fatima taso yiwa aunty LAILA sallama , amma da taga ba fuska sai ta hak'ura , haka suka fita daga gidan suka nufi gidansu Ahmad .
Fatima bata ga wani nisa tsakaninsu ba, a bakin gate su ka yi horn gate man ya zo ya bud'e musu alkhairi Ahmad ya mishi kamar yadda ya saba sannan suka shiga.
A falo suka tarar da hajiya zaune da fara'arta ta tarbesu , Ahmad ne ya fad'a kan k'afar hajiya ya soma yi mata shagwab'a wai ta tasheshi yana bacci sosai suka burge Fatima , yayin da hajiya sai lallashin shi takeyi ," ah daughter k'araso mana , kika tsaya anan " , duk da Fatima bata san abin da ake nufi da " daughter " amma tasan ita ake yiwa magana k'arasawa tayi ta gaida hajiya , bayan sun huta hajiya da kanta ta raka Fatima har d'akin da zata zauna , sosai d'akin ya burge Fatima a ranta, sai da hajiyan Ahmad ta gama nuna mata ko'ina na gidan sannan su ka koma falo suka cigaba da hira, tun Fatima bata magana har ta dawo tana sanya musu baki .
A chan b'angaren LAILA kuwa duk a zatonta Ahmad zai zo ya lallashe ta kamar yadda ya saba amma taji shiru toh me hakan yake nufi kasa jurewa tayi ta sauka k'asa , babu kowa a falon sai motsin da taji a kicin hakan ya sanya ta nufi kicin din , Aisha ta tarar tana goge gogen kan gas , da sauri ta tsugunna har k'asa ta gaida LAILA , bata amsa ba sai ma tambaya da ta hurga mata " Ahmad ya fita ne, ta fad'a tana kallonta da jiran ganin ta bata amsa " , eh sun fita, shi da k'anwarsa " wani zabura tayi " sun fita fa kika ce "? " eh , kawai ta fad'a ta juya taci gaba da aikinta " , zagaye LAILA ta shiga yi da taga bazaiyi mata ba sai ta haye sama ta fara rusa ihu , daga ta d'auki wayarta lalubar numbersa ta shiga yi bai d'aga ba , wayar mummynta ta shiga kira amma bata shiga ba , kawai sai ta fad'a kan gado ta rushe da kuka.
A chan b'angaren su Fatima kuwa , sosai suka yi hira anan ta fuskanci shak'uwa mai tsanani , a tsakanin hajiya ta d'an tilon d'an nata, Ahmad kuwa ganin da yayi Fatima ta saki jikinta da hajiyarsa hakan ya mishi dad'i sosai , bashi ya bar gidan ba sai bayan sallar la'asar kasancewar ranar Asabar ne , hakan ya sanya bai koma gida ba ya wuce asibitin DR Sadeeq , sosai sukayi hira sai bayan sallar isha'i sannan ya nufi gida , bai bi takan LAILA ba kawai yayi kwanciyarsa yayi bacci , shirun da LAILA taji yayi yawa ne ya sanya ta lek'a ta window, tabbas ya dawo , zaman jiranshi ta zauna yi , har 1 bai shiga d'akin ba , kawai sai ta sauka daga gadon ta nufi d'akinsa , handle din k'ofar ta murd'a amma a rufe gam, ita fa Ahmad ya sauya mata , bai tab'a yi mata irin wannan cin kashin ba sai yanzu da ya samo kilaki, ni kuwa nace au baki daddara ba ko LAILA, saura kad'an ta jiyoni ni kuwa na fece a miliyan😝.
A ranar ma bacci marar dad'i tayi.
Sosai rayuwar gidan yallab'ai Ahmad ta sauya babu walwala tsakanin ma'auratan kasancewar LAILA tayi fushin ta sauka amma Ahmad ya nuna baisan tana yi ba , kasancewar mai hak'uri bai iya fushi ba , yayin da a b'angaren Fatima kuwa sosai rayuwarta ta sauya tayi fresh tayi kyau , sai Sam barka , a yanzu ma hajiya shirye shiryen kai ta makaranta take yi abin gwanin burgewa .
Shin wai wanene yallab'ai Ahmad ,kuwa wacece LAILA, ya ya akayi suka had'u ?
OPPHHH DAN ALLAH AYI MANAGE DA WANNAN JIKI DA JINI SAI A HANKALI.
GAISUWAR BARKA DA SALLAH GAREKU DUK MASOYANA DA KUMA MASOYAN KISHIYAR UWA 🥰🥰
DAN ALLAH A DINGA YIMIN SHARE NA BOOK DIN NAN 👏🏻👏🏻👏🏻
Please
Share
&
Comments
To be continue..............
🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿
🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)
🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸
" :; ' ". ; .
' :
"
DAN ALLAH NAJI K'ORAFINKU KUYI HAK'URI WALLAHI BANDA TIME , A YANZU INA BUSY AMMA INSHA ALLAHU ZANYI K'OK'ARIN GANIN NAYI MUKU YADDA KUKESO.
INA GODIYA BISA GA NUNA KULAWARKU DA KUKE A GARENI , INA JIN DADI SOSAI , ALLAH YA BIYAKU , AMIN.🥰
SHAFI NA 23-24
Ahmad Muhammad Ahmad , haifaffen garin kaduna ne , a unguwar kawo , mahaifinsa Alhaji Muhammad shahararren d'an kasuwa ne, mahaifiyarsa hajiya Amina ita kuma haifaffiyar garin Zaria ,mahaifiyar Ahmad sun had'u ne ata dalilin bikin abokinsa da akayi anan ne suka had'u sosai ya yaba da halinta , aka sasanta har Allah ya sanya akayi aure , hajiya amina su biyu ne kachal Allah ya basu daga hajiya amina sai k'anwarta Maimunatu , a lokacin da hajiya Amina tayi aure taso tafiya da k'anwarta maimunatu , saboda halin rashi da iyayensu su ke fama amma mahaifan nasu suka k'ek'asa k'asa , suka hana ta tafiya da ita .
Shekararta d'aya Allah ya azurta ta da samun haihuwa ta haif