anshi , hawaye sosai ya gani akan idonta , cikin sanyin murya take magana" dan Allah yallab'ai ka taimaka ka barni na tafi , nasan dama zan kawo muku fitina a tsakaninku, shiru tayi sannan taci gaba , kaga kuna zaman zamanku zan wargaza muku farin ciki , daga zuwa na gwara ka barni na koma k'auye tunda yanzu rayuwa bata da amfani a gareni kuma.... Kuka ne yaci k'arfinta ta yadda ta kasa ko da motsa bakinta , shi kuwa shiru yayi yana kallonta kuma ya k'urawa d'an karamin bakinta ido ya gaza cewa komai , jiyayi kamar ya kamata ya rungume saboda rad'ad'in da yakeji na kukan da takeyi , yana yiwa Fatima kallon sani kuma yanayi mata kallon kanwarsa , amma to a ina yasan fuskar Fatima , tunani ya shiga yi gaskiya yasan fuskar amma ya manta , lallashinta yayi had'e da kwantar mata da hankali kuma ya shaida mata a hankali zai sanya a bincika mata dangin mahaifiyarta , haka da ya furta shi ya sanya ta yardarwa kanta da cewar zata ci gaba da zama a gidan har tsawon lokacin da za'a ga dangin mahaifiyarta , sai da ya tabbatar hankalinta ya kwanta sannan ya barta ta shiga d'akin shi kuma ya fita saboda b'acin rai , gaskiya dole ya san abinyi Laila ta sauya ba haka ya santa ba to me ya chanza ta ko dama haka take kawai dai dan tana sonshi ne ya sanya take bin umarninsa a baya , a haka ya k'arasa cikin mota ya kunna ya fice a gidan , Laila da ke bakin window tana kallon lokacin da Ahmad ya fita k'ara rushewa tayi da kuka, ta fad'a kan gadon d'akin tana k'udurtar yadda zatayi da rayuwar Fatima , tunani ta fara to tayaya zata yi mata illah , ta tambayi kanta , ni kuwa nace oho ke za'a tambaya😏.
Ko da Ahmad ya bar gida tafiya yayi ta ak'alla minti biyar kafin ya k'arasa inda zaije , a bakin wani tangamemen gida ya tsaya , da sauri aka bud'e gate din kasancewar gate man din yasan ko waye , gaisawa sukayi yayi masa alkhairin da ya saba sannan ya shiga ciki , gaskiya gidan ya had'u har yqfi nashi had'uwa , tun daga bakin k'ofar falon ya fara k'wala mata kira kamar k'aramin yaro " mummy , mummy , mummy! Da k'arfi yake fad'a wata mata dattijuwa ta fito daga cikin d'akin da yake hannun dama , "kai Ahmad wallahi baka girma , ta fad'a tana k'ok'arin zama a kan d'aya daga cikin kujerun d'akin ", gaisawa sukayi sosai ya kwashe komai da ya faru ya fad'a mata , " wai amma wannan yarinya bata kyauta ba , kaima kuma ka daina Marin mace hakan ba daidai bane ba , kaci gaba da hakuri , yauwa ita ina fatiman take tana cahn to in ba matsala ni ka kawomin ita zatafi jin dad'in zamanta anan ", ba'a son ranshi ba ya amsa da to ganin hajiyarsa ta nuna sah'awar zaman Fatima a gidan kuna batun haka shi kad'ai iyayensa suka haifa babu abokin taya hajiyarsa zama , hakan ya sanya ya amince da hakan , zancen gwaggonsa ta masa tace wallahi zanje gaidata aiki yamin yawa amma zan kirata, sallama yayi mata had'e da alk'awarin kawo mata fatiman.
Sai k'arfe takwas lokacin ya dawo daga fitar da yayi , yasan bazai samu abinci ba hakan ya sanya yayi take away yayiwa mutanen gidan ma , Fatima ya fara kaiwa sannan ya mata zancen zata koma wajen mahaifiyarsa dad'i sosai taji hakan ya mishi dad'i sosai dan haka ya haura zuwa sama, direct d'akinsa ya nufa ko takan Laila bai bi ba ya gama abubuwan daya saba yi ya kwanta bacci ranshi ba dad'i.
A b'angaren Laila ma hakan ce ta kasance tayi bacci marar dad'i ......
Please
Share
&
Comments
To be continue.....
🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿
🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)
🍁Daga Alk'akamin Nussad🌸
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
BARKA DA SALLAH FAN'S, FATAN ANYI SALLAH LAFIYA, ALLAH YA MAIMAITA MANA AMIN.
KAMAR YADDA NA ALK'AWARTA MUKU CEWAR ZANCI GABA DA RUBUTU NA , INSHA ALLAHU GASHI NA CIKA ALK'AWARI NA.
SHAFI NA 21_22
A b'angaren Fatima kuwa , ta yi bacci ne mai dad'i cike da walwala kasancewar Allah ya yaye mata zaman gidan , matar gidan sam bata da hali mai kyau , a haka har bacci ya yi awon gaba da ita.
Washe gari karfe shida na safe har ta shiyar tana zaman jiranshi a falo, ganin zaman bazai yi mata ba ya sanya ta fita falon gidan , kicin ta lek'a ta tarar da kukun gidan tana dafa Karin kumallon safe , gaisawa suka yi da yake ita kukun na da sauk'in kai cikin k'ank'anin lokaci ta ya ta suka had'a abincin , kunun tsamiya suka yi da kosai sai farfesun kayan ciki sai shi mai gidan da ake dafawa shayi , komai suka jera shi a dinning table , komawa suka yi kicin suka cigaba da hira, sosai kukun mai suna Aisha taji dad'in hira da Fatima duk kuwa da k'ank'antar shekarunta.
Alhaji Ahmad ne ya fara tashi sakamakon k'arar wayarsa da ta tashe shi , mahaifiyarsa ce da sauri ya d'aga suka shiga gaisawa , bayan ta jaddada masa cewar lallai ya tabbatar ya kawo mata Fati