ma ya yiwa matar gidan magana ta sauko su gaisa , sai ta bata wajen zama kafin komai ya tsagaita, " dama yana da aure , dama anayin aure idan mutum d'an mafiya ne kuma ya ajiye ta a gidan mafiya , anya ma ta sani kuwa, to kodai ita ma y'ar mafiyar ce , domin ita har yanzu bata yadda da cewar ba gidan mafiya ta ke ba , k'arar takalmi mai tsini taji na dukan tiles , hakan ya sanya ta kallon inda k'arar ta ke fitowa , wara idanunta tayi had'e da mutsitstsika su , "masha Allahu ta furta a hankali gaskiya matar gidan mai kyau ce ita ma ga gashinta har gadon baya , " ni kuwa nace lallai Fatima har yau kina da yarinta bakisan gashi natural ba bakisan na kanti ba , karasowa suka yi har falon hannunsu had'e da na juna , Ahmad ne ya kalli Laila wadda tayi kicin kicin da rai ganin an kawo mata budurwa gida ," Laila zauna mana yayi mata nuni da kusa da Fatima ," chab Allah ya kiyaye na zauna kusa da tsintacciyar mage " duk da Ahmad baiji dad'in yadda Laila tayi ba, amma yadda yaga Fatima tayi abin bai mata zafi ba ya sanya ya basar , magana ya soma yi takan Laila ya fara kasancewar ita ce babba " Laila ga y'ar uwa nan na kawo miki , ke kuma Fatima kinga wannan antinki ce banason tashin kunya duk da ba d'abi'ar ki bace ba, ki kula sosai , zaki dinga taya ta zama da hira kinga ko ba na nan , kinji ya tambaya ya na kallon fuskarta ," eh , kawai tace " ita kuwa Laila ranta in yayi dubu ya b'aci ta yaya za'ayi a kawo mata yarinya y'ar k'auye ace ta tayata zama amma Ahmad ma ya raina ta da ajinta da komai ya rasa wadda zata tayata hira sai bagidajiya , tsintacciyar mage, duban Ahmad tayi had'e da kallon ka raina min hankali ma wallahi , sarai ya gane me take , amma yayi banza da ita , gajiya tayi da zaman hakan ya sanya ta mik'e tsaye , tare da fad'in " in ka gama ina da abin yi , I can't stay and wasting my time about this rubbish, ta fad'a tana k'ok'arin tashi gyad'a kai kawai yayi saboda tsabar haushi domin bai ma san me zai ce mata ba, hayewa sama tayi ta barsu a wajen , Fatima batasan me Laila ta fad'a ba amma ta fuskanci bata maraba da zamanta a gidanta , ai taji dad'i ma da matar gidan bata so ta zauna , itama gwara haka, juyawa yayi ya kalleta " tashi muje na nuna miki masauki, abinda yace kenan ya yi gaba " ita kuma Fatima ta bishi a baya.
Sosai ya nuna mata yadda ake amfani da kayan band'akin kasancewar wasu ma ko ni bansan yadda ake amfani da su ba ballantana fatima🥴, bayan ya gama nuna mata komai sannan ya fita ya barta domin ta yi wanka, tunawa da yayi ba kaya a hannunta ya sanya da sauri ya fita ko d'an aike bai tsaya nema ba , ya hau mota ya tafi wani store na kusa domin samo mata kayan sawa domin a gurin hatsarin ta rasa kaya , dohayen riguna ya saya mata Arabian gown masu kyau , ko da ya dawo ta fita a wanka , ta sanya kayan ta da ta taho da shi , bata kayan ya yi ya mata umarni da cewar ta sanya ta fito ta ci abinci , bayan tayi sallah ta fita falo, a zaune ta tarar da shi a zaune a kujera ya dafe kansa , cikin sanyin muryarta ta masa sallama , d'agowa yayi masha Allahu kawai ya furta a cikin zuciyarshi " yarinya kamar balarabiya , " " me kace , ta fad'a, " a'a babu komai zauna kici abinci ga dinning chan ya nuna mata da hannu " cikin tafiyar k'asaita ta k'ara ta zauna a saman d'aya daga cikin kujerun , rasa yadda zatayi ta bud'e food flask din , juyowa tayi tana son yin magana ta kasa, ganin haka ya sanya ya gane me take nufi hakan ya sanya ya tashi yaje har kusa da ita ," matsa kawai yace " ta matsa ya bud'e mata yana k'ok'arin zuba mata a faratin , yayin da Laila tana k'ok'arin saukowa daga benen gidan , ihu da k'arfi ta sanya, ! Na shiga uku ni Laila me zan gani a gidana a kawomin karuwa , wallahi sai na kasheki yau , tab lallai ma," kanta tayo tana gurnani kamar zakanya tsabar rud'ewa Fatima batasan lokacin da ta k'ank'ame Ahmad ba wani yarrr yaji a cikin shi yana wannan yanayin bai san har Laila ta k'araso gurin k'ok'arin janyo ta Laila ta fara ita kuma tana k'ara k'ank'ame shi , hakan ya sanya Laila ta k'ara haukacewa , ta biyo Fatima ihun da ta saki ya fargar da Ahmad, hakan ya sanya yayi saurin maidata bayan shi Laila ta fad'o kanshi " wallahi bazan bazan yarda ba , haka kawai an kawomin yarinya tsintacciyar mace hakan ma bai isa ba sai anti karuwanci a gaba na kuma wallahi..... Ai bata k'arasa ba sakamakon gigitaccen Marin da Ahmad ya yi mata a fuska , abinda bai tab'ayi ba a iya zamansu na aure , ita kanta Laila sai da abin ya bata mamaki , tunda suke Ahmad ko da wasa bai tab'a sanya hannu a jikinta ba ko da ta sigar wasa ne , amma yanzu saboda wata bagidajiya , wawiya dabba ya sanya hannu har ya made ta , hakan ya k'ara mata tsabar Fatima a ranta ta yadda tana jin kamar ta kashe ta , lallai tunda daga zuwanta ta wargaza mata farin cikinta itama sai ta zauna cikin bakin ciki har iya rayuwarta a gidan dan da k'afarta zata gudu basai wani ya fitar da ita ba, da gudu ta haura sama fitar da batayi ba kenan ta shiga d'akinta ta hau rusar kuka.
A b'angaren Ahmad kuwa , dawo da Fatima yayi gab