NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 19 of 44

kalar sky blue da hula zanna bak'a , da sauri direba ya taso, girgiza masa kansa yayi alamar ba tare zaku fita ba hakan ya sanya ya koma kan bencin baba mai gadi , shi kuma ya nufi motarsa , shiga yayi , ya kunna , baba me gadi ya wangale masa bakin gate ya cinna hancinta wajen gidan ya nufi titi . ASIBITI Da sauri ya k'arasa asibitin , a bakin office ya had'u da Dr Sadeeq yana k'ok'arin fita domin komawa d'akin da Fatima ta ke , " ah mutumin ya haka tun d'azu na kiraka amma sai yanzu , ko dai madam ta rik'e ka ne , ya fad'a had'e mik'a masa hannu domin suyi musabaha" , shi dai Ahmad bai ce k'ala ba , suka juya suka nufi d'akin Fatima, a lokacin ta farka har nurses sun taimaka mata tayi wanka tayi sallah , da sallama suka shiga amsawa tayi had'e da kallon k'ofa , Dr Sadeeq ne ya fara k'arasawa cikin d'akin had'e da zolayar ta ah lallai kin warke irin wannan kwalliya haka , ya fad'a ya nunawa Ahmad wajen zama Wanda ya kafe a tsaye yana kallon yarinyar da ya kad'e , kyakykyawa ce ya fad'a a ransa , zama yayi , doctor ya gabatar da shi a wajen Fatima , gaisar dashi tayi cikin murya mai sanyi amsawa yayi, kuma bai d'auke idonsa daga kanta ba , shi dai yana yiwa yarinyar nan kallon sani , " ya sunanki ya fad'a yana dubanta ", Fatima " abin da tace kenan ta juya suka cigaba da hirarsu da doctor jefi jefi yake sanya musu baki , ya dad'e sosai daga bisani ya nufi gida bayan yayi mata sallama ya tafi ita kuma ta kwanta saboda har lokacin bata dawo daidai ba. Sai da Fatima ta kwana kusan bakwai ta warke garau , amma ba ta tab'a fad'awa kowa maganar y'an uwanta ba , a nashi b'angaren Ahmad yayi tunanin ya tambaye ta ko dan ya mai da ta danginta amma ganin cewar ba ta da lafiya ya sanya sai a yau ya tare ta da zancen dangin na ta , bata b'oye masa komai ba dan tana ganin kamar wannan wata mafaka ta samu ko Allah zai sanya ya taimaka mata ta wani fannin ganin cewar yana da tausayi , jin labarinta ya sanya yayi alk'awarin cewar zai tafi da ita cikin danginshi kafin ya san me zai yi akai . Satin Fatima biyu Dr Sadeeq ya ba ta sallama , har bakin mota Dr ya raka su , sannan ya koma su kuma suka fita daga cikin asibitin zuwa gida Alhaji Ahmad......... Please Share & Comments To be continue........... DAN ALLAH AYI HAK'URI DA WANNAN SABODA NA GAJI . SAI ALLAH YA KAIMU WANI SATIN ZAN K'ARAYIN TYPING , LUV U FAN'S🥰🥰 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 NA SADAUKAR DA LITTAFINA NA KISHIYAR UWA GA, PHAREEDA , INAJIN DAD'IN COMMENTS D'INKI SOSAI DA SOSAI, ALLAH YA BIYAKI.🥰 SHAFI NA 19_20 Ko da suka k'arasa cikin unguwar , tun daga bakin layin Fatima ke rarraba idanu , " oh ni Fatima na kawo kaina ga mahallaka , yanzu ace ni zanyi rayuwa anan , anya ma kuwa ba d'an mafiya na biyo ba , innalillahi wa'inna ilaihir raji'un , shikenan tawa ta k'are , duk abinda take fad'a tana fad'ar shi ne a cikin zuciyarta" , a take tayi dana sanin gudowarta daga k'auye , dama ta tsaya an d'aura mata auren da bilya da wannan yawon gashi bata ga tsuntsu bata ga tarko, shikenan a banza a wofi wasu mutanen zasu cinye ta , garin lalubar dangin mahaifiyarta ta b'ige da zuwa mahallakarta madadin ta ganta a zariya sai gata a Kaduna , ta shiga zurfin tunani da tashin hankali ta yadda har su ka iso k'ofar gidan mai gadin gidan ya bud'e suka shiga bata sani ba . Cikin sexy voice nashi ya kira sunanta "Fatima" har sai da ya kira sau uku ana hud'un ne tayi firgigit ta farka daga mummunan tunanin da take yi , kallon gefen da ake magana tayi shine dai a tsaye yana kallon ta da tuhumar abinda take tunani , "sauko , yace da ita " a hankali ta sauko da k'afafunta kasa ta fito daga motar , kallon gidan da suka shigo ai da hanzarinta tayi hanyar bakin gate , gudu takeyi ba k'ak'k'autawa , shikenan ita kam k'arshenta a duniya ya zo , sai a sannan hawaye ya fara zubar mata a ido , da Sauri ya bi bayanta domin sanin meke faruwa, har ta kai bakin gate din gidan bata tsaya ba , ja tayi ta tsaya turus sakamakon tashin sanin ta ina zata fita , shima tsayawa yayi yana kallon ta , da mamaki fal a fuskarsa , to kodai hatsarin da ya faru da yarinyar nan ko dai ta samu matsalar k'wak'walwa ne, gabansa ne ya fad'i yayi saurin kawar da zancen daga cikin zuciyarshi , to ko kuma Aljanu gare ta , ah to ba mamaki ma aljanunne, ni kuwa nace to fa su malam Ahmad wata kam aljanu sune masu laifi ba kai ba🥴, k'arasawa yayi a hankali ya kamo hannunta ya jata zuwa har bakin falon gidan , thumb print yayi wa k'ofar aikuwa ta bud'e , shiga suka yi ciki , wani tsoro ne ya k'ara shiga zuciyarta, ita fa gaskiya mutumin nan tsoro yake bata , ga uban gida kamar ba'a duniya ba , inama ya kasance mafarki take yi ba gaskiya ita bazata zauna ba yana tafiya zata gudu, " to kuma idan kika gudu ina kika sani, zuciyarta ce ta bata wannan tambayar" , "babu , ta fad'a har sai da ya juyo " wajen zama ya nuna mata, sannan ya fad'a mata cewar bara ya haura sa
🏠