NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 18 of 44

masallaci , domin yin sallah har suka dawo daga sallah Fatima bata farfad'o ba, dan haka Ahmad ya bar Fatima a hannun Dr Sadeeq ya nufi unguwarsu dake cikin wata GRA dake garin Kaduna. 🌹🌹🌸🌸🌹🌹🌸🌸🌹🌹 Tangamemen gate mai kalar ruwan madara masu gadin gidan su ka bud'e , hancin motarsa ya danna cikin gidan, ma'aikatan gidan sai kai kayo sukeyi , masu ban ruwa suna ta bawa furanne ruwa , duk inda ya gifta masu aiki na ta gaida shi yana amsawa cike da fara'a akan fuskarsa duk kuwa da cewar a zuciyarsa ba haka bane ba saboda yana tunanin me zai tarar a cikin gidan uwa uba kuma Fatima dake gadon asibiti. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 Shin wai meke faruwa ne a chan k'auyen Darki ne bayan Fatima ta baro 'yan biki da inna Asabe? Ana ta aikin biki har safiya tayi , inna Asabe ta shiga cikin rububin mutane , hakan bai Sanya an farga da cewar amarya ta gudu ba har sai da hantsi ya fara fitowa ana ta shirye shiryen d'aurin aure ganin har wannan lokacin Fatima bata fito ba ya sanya inna Asabe ta aika Abu da ta kirawo mata Fatima domin ta shirya saboda an kusa fara d'aurin auren , a lokacin Abu nada juna biyu dan har ya fito sosai , lek'awa tayi cikin d'akin cike da gatsali " dalla chan ai saiki fito banza kin wani zo kin zauna a d'aki kin bar mutane , " shiru taji dan haka cike da bala'i ta chusa kai , wayam ta gani dan haka ta fito da gudu ta nufi d'akin inna Asabe.......... Please Share & Comments To be continue........ 🌸🌸🌸🌸🌹🌹🌹🌹 🌿🌿🌿 NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹 KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ NA SADAUKAR DA LITTAFINA GA MASOYA LITTAFIN KISHIYAR UWA. SHAFI NA 17_18 D'akin Inna Asabe ta nufa ko sallama babu," ! Inna , ta kwad'a mata kira da k'arfi , juyawa Asabe ta yi ," ke lafiya" , ta tambaya ta mik'ewa tsaye, " inna fa Fatiman ba ta nan fa" wani ihu inna Asabe ta zuba , tana duban mutanen d'akin da su ka zuba mata idanu, Abu fa kamar wasa k'aramar magana ta zama babba , tun kafin mutanen wajen y'an d'aurin aure su hallara ake nemanta duk inda aka san za'a ganta an nemeta amma shiru , nan fa aka ba za ma ko Allah zai sanya a ganta , amma shiru , lokacin da iyayen ango su ka zo aka Sanar da su , sosai hankalin ango ya tashi na b'atan amarya Fatima , aka yi nema aka gaji hakan ya sanya aka hak'ura da d'aurin auren aka ba ri sai an ganta tukunna , zancen fa ya cika k'auyen Darki na cewa Fatima ta gudu, wad'ansu na cewar dama bariki ta ke yi shi ya sanya zaman k'auyen ba zai yi mata ba dole ta shiga duniya , haka dai aka hak'ura duk da cewar y'an uwan marigayi malam Iliya sun koka na rashin Fatima amma suka hak'ura, wannan kenan. KADUNA STATE Lokacin da Ahmad ya isa k'ofar falon , thumb print ya danna , aikuwa a take k'ofar ta bud'e , shiga yayi da sallama , masha Allahu wani tangamemen falo ya bayyana , ga sanyi Ac da ya gauraye wajen , a d'aya daga cikin kujerun d'akin , wayar shi ya d'aga ya k'ira daga chan aka d'aga "haba habibty gani fa na dawo ina falon k'asa , kuma wallahi na gaji ," daga chan b'angaren aka yi magana , ban san me a kace ba na ga ya b'ata fuska , ya kashe wayar , kai shi ya zai yi wajen ba dad'i cikin gida ma haka , "Allah ka duba lamari na, ya fad'a yana duba k'afar bene , wata mata ce take saukowa daga ganinta kasan hutu ya ratsa ta akalla ba za ta wuce Ashirin da bakwai ba a duniya , sosai tayi kyau ba k'arya , ba ta da tsayi sosai amma fara ce , anyi mata kitson attach ya zubo har kafad'a , daga ganinta kasan idanunta sun bud'e da duniya, ' LAILA ' kenan uwargida wajen Ahmad , " haba Laila kina sa ne da cewar jiya mu ka yi zan dawo ai kya kirani ki ji me ya tsayar da ni amma kika yi ignoring nawa, kamar ba mijinki ba haba Laila, ya fad'a yana dubanta ", tab'e bakinta tayi " haba my luv ka san dai nima banda time ko saboda ka ga nima na fita aiki , " kallonta kawai yayi ya girgiza kai ya rasa meyasa kwata kwata LAILA bata damu dashi ba yana matsayin mijinta , ganin ba za ta tambayeshi meya faru ba ya sanya ya fara fad'a mata abin da ya faru da shi , "uhmmm Allah ya kiyaye" kawai ta ce sannan ta juya ta fita a d'akin , girgiza kanshi yayi sannan ya tashi ya shiga band'aki , wanka yayi sannan ya shirya yana fitowa falo wayar shi tayi k'ara dubawa yayi ya ga Dr Sadeeq ne ya kira dan haka ya d'aga cikin hanzari , sallama yayi , aka amsa tachan d'aya b'angaren ," ok to gani nan zuwa , kawai ya fad'a ya nufi saman d'akin LAILA , ya na bud'a d'akin ya hango ta akan bed tana charting, sallama yayi mata bata amsa ba , kawai ta d'aga mishi kai , juya wa yayi ya fita had'e da girgiza kansa , harabar gidan ya nufa sanye da yadi d'an Abba
🏠