MAHAIFIYATA ALLAH YA JA DA RANKI , HAJIYA FATIMA TURAKI ADAM , LUV U MY MOM❣️❣️
KISHIYAR UWA FAN'S NA GAISHEKU SOSAI DA SOSAI.
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌹🌹🌹🌹🌹
🌸🌸🌸🌸
🌹🌹🌹
🌸🌸
🌹
SHAFI NA 15-16
A haka sukayi tafiyar kusan awa d'aya da rabi kafin nan su isa cikin garin zaria, bayan an karb'i kud'in motarsu , kafin nan suka k'arasa garin zaria, bayan an Shiga cikin tasha a lokacin kusan k'arfe ukun dare , mutane suna ta sauka daga motar yayin da Fatima tana chan ta shiga duniyar tunani bata ma san an k'arasa cikin tashar ba , direban ne yana k'ok'arin juya motar domin komawa ya k'ara d'ebo wasu fasinjojin , juyawar da zaiyi ya hangota a zaune tana tunani , "baiwar Allah direban ya fad'a ya d'an dukan saman kujerar" firgigit ta farko daga duniyar tunanin , sai a lokacin ta farga da cewar lallai fa sun isa garin zariya , " ki sauka anzo fa , ya fad'a had'e da nuna mata wajen da sauran mutanen suka fita, tsimmokaran kayanta ta d'iba sannan ta sauka daga motar , tana k'ara rik'e kayan nata, shi kuma direban ya juya da motar ta sa bayan ya sauke dukkan fasinjojin, domin komawa , sai a lokacin Fatima ta fara tunanin ina zata shiga , waye ta sani a garin zaria ita yanzu ya ya zatayi , sai a sannan ta ji tsoro ya kama ta , ga dare ya yi gashi cikin tasha ne ga mutanen da suka zo da su duk kowa ya kama gabansa , gefe ta koma ta zauna ta zubawa sarautar Allah idanu kafin gari ya waye tasan nayi , mutane taga suna gilmawa kamar walk'iya , tsoro ne ya kama ta , d'ago kanta tayi aikuwa taga sun yi mata rumfa , irin yan iskan cikin tasha ne , wani gabjeje ne ya yi magana cikin kakkausar murya , yana mai nuni da ita ," ke me kikeyi a nan ya fad'a yana k'walalo idanu " kakkarwa jikinta ya fara yi , tsoro sosai ya shige ta , " magana ake yi miki ba , wani ya fad'a daga cikin wad'annan y'an mutane , " kaga rik'emin ita kawai kagani babban nasu ya fad'a , chafka d'aya daga cikinsu ya kaimata da sauri ta zille ta fara ihu ga babu mai taimako, gudu take yi suna bin ta a baya har suka fita daga cikin tashar suna bin ta a baya, sosai takeyi gudu har ta hau kan babban titin garin basu daina bin ta ba, ga babu mutane sosai kowacce mota kawai wuce was takeyi , a lokacin Fatima ta gaji lik'is tana neman fad'uwa , tsautsayi ya sanya tana k'ok'arin tsallaka titi mota ta d'ebo da gudu aikuwa ta kwasheta , k'arar da ta saka ne ya sanya wad'annan mutanen suka juya da gudu suka koma idan suka fito , da sauri mai motar ya fito daga cikin motar ya k'arasa inda ya ga yarinyar a kwance hasbunallahu ya furta ganinta da yayi cikin jini ko motsi bata yi , a cikin zuciyarsa ya fara tunanin to me ya fito da wannan yarinyar cikin wannan daren ganin tunanin bazai kai masa ba ya sanya ya d'auke ta da Sauri ya nufi cikin mota da sauri gashi dare yayi a haka ya tada motarsa ya figa da gudu kasancewar yana Sauri ne dan haka madadin ya kaita asibiti kawai sai ya wuce da ita cikin garin Kaduna ya bar zariya da ita kasancewar gaba ki d'aya ya gama rud'ewa .
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Sai ana kiran sallar asubah sannan su ka k'arasa , asibitin cikin garin ya wuce da ita saboda yana da amini Dr Sadeeq, tun kafin su k'arasa ya sanar da shi halin da ake ciki, dan haka suna isa ya tarar da nurses suna jiran isowarsa ciki kuwa harda Dr Sadeeq din , da sauri aka d'orata akan gado aka shiga da ita cikin asibitin , shi kuwa mutumin da ya kad'eta kwata kwata ya rasa nutsuwarsa , ya kai ya kawo haka ya dinga yi " haba Ahmad kayi a hankali mana ko sai ka jawowa kanka wata matsalar , Dr sadeeq yayi furucin yana duban abokin nasa , " girgiza kai kawai Ahmad yayi saboda bayaso ya zama sanadiyar salwantar rayuwar wannan baiwar Allah , " bakasan me nake tsoro ba sadeeq , wlh ina cikin tashin hankali bansan me zanyi akai ba idan yarinyar nan ta rasa rayuwarta ta sanadiyya ta , Ahmad ya fad'a kamar zaiyi kuma , " d'aya daga cikin likitocin asibitin ne ya fito kasancewar Dr Sadeeq ya tsaya wajen abokin na sa domin kwantar masa da hankali ," a gaskiya yarinyar nan ta auna arzik'i amma mun samu ta farfad'o daga doguwar suman da tayi ,Dr Khalil ya fad'a yana duban Dr Sadeeq"," yawa Dr sannu da k'ok'ari min gode fa " , " ah ai babu komai ai maigida Ahmad ai namu ne Allah ya kiyaye gaba ", suka amsa da amin a tare , sai a lokacin ne Ahmad ya sauke nannauyar ajiyar zuciya , Dr Sadeeq ne ya dubi Ahmad , " am abokina ya akayi ne al'amari irin wannan ya faru" a take Ahmad ya bawa Dr Sadeeq labarin yadda abin ya faru tun daga farko , sannan ya k'ara da cewar hasalima ina sauri ne saboda laila na sanarda ita cewar zan dawo a yau daga kano shiyasa ", " amma baka tsammanin iyayen ta zasu nemeta , Dr Sadeeq ya fad'a yana duban Ahmad ," nima haka make ta tunani amma komai ma in ta farka zamuji" daga haka suka cigaba da hirar abinda ya faru.
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Sai da akay kiran sallah sannan suka tashi daga hirar suka nufi