NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 16 of 44

ta ya bata ne , " inna sannu da gida , Fatima ta fad'a had'e da rusunawa tana mik'a mata kudin cinikin da tayi " karb'a tayi ta k'irga su tsab daga bisani ta tura su k'ark'ashin tabarmar da take kishingid'e, har zata tashi ta zaunar da ita sannan ta fara yi mata zancen bilya da duk abinda ya ke faruwa sannan ta k'ara da cewa " kuma wallahi auren nan kamar anyi shi angama, dan na yanke ranar auren nan da wata d'aya mai zuwa za'ayi shi", gaban Fatima ne ya fad'i sakamakon wannan magana da innar ta ta tayi , da to ta amsa sannan ta juya ta shiga d'akinta cike da tashin hankali. 🌸🌸🌹🌹🌸🌸🌹🌹🌸🌸 A cikin d'aki kuwa safa da marwa ta Shiga yi , tana tunanin yadda zata b'ullowa da lamarin, a gaskiya kota halin ya ya ne bazata tab'a yadda da auren wannan mutumin ba , zatayi duk mai yiwuwa wajen gujewa aurensa to ta ina zata fara , tayi zurfi a cikin tunani ta tuna da aminiyarta ta yarinta hannatu , aikuwa ta yardarwa kanta cewar lallai zata samu mafita bisa ga hukuncin da ta yankewa kanta , tana ta tunani har chan dare sai daga baya bacci b'arawo yayi awon gaba da ita. 🌸🌹🌸🌹🌸🌹🌸🌹 Da asuba ta farka da Sauri ta gama aikin gida tsaf , ta gama abin da zata fita dashi tallah , sallama ta yiwa inna Asabe bayan tayi aikinta tsab sannan ta fita talla, Alhamdulillah ta siyar da wuri dan haka ta wuce gidan hannatu domin samun mafita , da take itama hannatun tayi aure shekaru biyun baya da suka wuce , a tsakar gida ta tarar da ita suka rungume juna cike da murna , sosai sukayi murna na ganin juna, bayan sun gama murnarsu sanan Fatima ta fad'awa aminiyar ta ta abin da ya kawo ta , sosai hannatu ta girgiza da jin wannan maganar , ta dubi Fatima cike da kulawa tace " Fatima nasan kinyi hak'uri , a yanzu bazan baki shawarar ki zauna a aura mini mashayin giya da Neman mata ba , dan haka yanzu meye mafita, nan Fatima ta shaida mata Cesar tanason ta tafi neman dangin mahaifiyarta , hannatu ce ta k'arfafa mata guiwa na cewar hakan yayi indai tasan inda suke ta sanar da ita cewar mahaifinta kafin ya rasu ya sanar da ita garin mahaifiyarta ta , amma ita yanzu matsalarta guda rashin kud'i a hannunta , hannatu ta sanar da ita baza'a samu matsalar kud'i ba insha Allahu , haka su ka k'ark'are matsalar ta su haka ta tafi gida cikin farin ciki . 🌸🌹🌹🌸🌹🌹🌸🌹 Haka dai rayuwa tayi ta tafiya , cikin k'warin guiwa ga Fatima , na yarda ta samu damar zuwa Neman dangin mahaifiyarta , ko ba komai zata ga ko da hoton mahaifiyar ta ta , kuma ta sadu da sauran y'an uwa mahaifiyar ta ta, tana ta shirin barin garin , a yayin da inna Asabe a b'angarenta it a ma tana ta shirin biki ta sanarwa da kowa domin murnar da takeyi na cewar fatima zata shiga kabarinta ne , sosai fa takeyi shiri kamar ba bu abinda Yake ranta , bayan ta gama shawo kan y'an uwa malam iliya , da nuna musu alfanun yadda auren zai kasance , suka kuwa yarda da hakan har suke tunanin ma Asabe ai tayi hankali. 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 A haka har satin biki ya shigo , yayin da fatima ta shirya tsaf da komai nata bayan ta karb'i kud'i wajen hannatu domin shiga mota yayin tafiyar ta wajen kakanninta. Dangin ango sun kawo kud'in sadaki da kayan lefe , kaya sosai aka kawo duk da bak'in cikin da Asabe ke ji amma idan ta tuna yadda Fatima zata dawo sai taga ba komai bane ba , an fara biki yayin da Fatima take nuna musu ba abinda yake damunta . A Daren ranar d'aurin aure mutane mata mata masu girki NATA aikinsu , Fatima CE ta lek'o ganin hankalin kowa yana ga aikinsa ya Sanya cikin sand'a ta juya ta d'auko duk wani kaya da zata buk'ata da kud'in da k'awarta ta bata , lallab'a ta fice daga gidan ba tare da kowa ya ganta ba ta nufi k'ofar gida, tana tafiya kuwa ta had'u da mai mashin godiya tayi ga Allah duk da a lokacin bata kawo cewar zata samu abin hawa ba saboda dare yayi sosai , ta tsareshi had'i da fad'a masa tashar motocin garin zai kai ta , ya amince ta hau bayan sunyi cinki ta yarda , basu zame ko ina ba sai tasha , tana zuwa kuwa tayi sa'ar samun direban na k'ok'arin tashi Dama sauran mutum d'aya Duke jira aikuwa tanajin motar zariya ce da Sauri ta fad'a bayan ta sallami mai mashin d'in da ta hau , da take tafiyar ta dare ce babu wuya suka bita daga cikin k'auyen suka cilla babban titi , sai a sannan Fatima ta saki dogon numfashi samun nasara ....... Please Share &comments To be continue........ 🌸🌸🌸🌸🌹🌹🌹🌹 🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁 Daga Alk'alamin Nussad🌸 GODIYA GA ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA , DAYA BANI DAMAR CIGABA DA RUBUTUN LITTAFIN NAN , TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD, DA ALIHI DA SAHABBANSA MASU GIRMA. BAYAN HAKA NA SADAUKAR DA LITTAFINA GA D'AUKACIN Y'AN UWANA NA SABON RUWA'S FAMILY, LUV U ALL🥰🥰 AJUJI'S FAMILY KUMA HAR DA KU BAZAN MANTA DAKU BA , JINJINAR BAN GIRMA GAREKU ALLAH YA K'ARA ZUMUNCI , AMIN🥰🥰
🏠