ta huce mizanin y'an matantaka a k'auyen , abinda basu sani ba inna Asabe ce tayi asirin da ba Wanda zaiji yana Sonta kaf garin , tun abin baya damun Fatima har ya dawo yana damunta , in ta zauna ba abinda take tunawa sai rayuwarta da mahaifinta da kuma labarin mahaifiyarta Wanda mahaifinta ya bata , sai dai taci kukanta babu mai rarrashinta, abin d'aya ta k'udurta a zuciyarta Wanda idan tana tunawa takan samu sa'ida a zuciyarta , shine yake sanyawa ta k'ara nutsuwa , na cewar bashakka ko ba dad'e ko ba jima zata nemo asalin dangin mahaifiyarta ,wannan yakan sanya taji dad'i sosai a ranta.
🌹🌹🌸🌸🌹🌹🌸🌸
A yau Asabar tun safe ta tashi ta kama kiciniyar aiki sosai takeyin aiki sakamakon bak'in da zasuyi daga b'angaren inna Asabe d'an kanwar mahaifiyarta ne zaizo dan haka ta sanya Fatima yin aiki ganin shi a birni yake da zama kuma y'an birni lallab'a su akeyi, haka fatima ta zage sosai tanayin aiki , wajen k'arfe biyun rana bak'in suka sauka murna sosai inna Asabe tayi na ganin tare da d'ansa aka so mai suna Bilya , ko kad'an yaron baya da tarbiya komai kai tsaye yakeyi gashi sai ya had'u da sakalcen uban ai kuwa abu ya k'ara ta'azzara sosai , shaye shaye, Neman mata ba Wanda bayayi , kai ya kai mak'ura wajen aikata abinda bashi kenan ba, ganin d'an uwanta, cikin washe baki suka gaisa da juna tare da tambayar bayan saduwa, sunyi hira sosai , Fatima na jinsu tana d'akinta , inna Asabe ce ta kwala mata kira da sauri ta fito ta gaishesu , aifa tunda biliya ya d'ora idanunsa akan Fatima ya fara lasar baki kamar wani tsohon maye, inna Asabe ce ta umarci Fatima da ta kawo was bak'insu abinci haka ta dinga jigilar abinci tana kai musu , Shiva d'ari fita d'ari sai sun had'a ido da bilya , tun tana masa yakana har sai da ya k'ureta tako galla masa harara , ai sai yaga tafi d'azu kyau , sai da ta gama komai sannan ta juya ta nufi d'akinta ta barsu suna cigaba da hirarsu ta zumunci...........
Please
Share
&
Comments
To be continue.........
INA K'ARA GODIYA GAREKU FRIENDS NAWA DA FAN'S NAWA ALLAH YA BAR ZUMUNCI .
Please ayi manage da wannan I'm so tired.
🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿
🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)
🍁Daga Alk'alamin Nussad)🌸
Shafi na 1️⃣3️⃣-1️⃣4️⃣
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌹🌹🌹🌹🌹
🌸🌸🌸🌸
🌹🌹🌹
🌸🌸
🌹
Bayan ta fito daga d'akin inna Asabe , d'akinta ta nufa cike da takaicin bilya wannan wanne irin mai shegen kallo Allah ya had'a ta da shi , tana murna Allah ya raba ta da Ado ashe hakarta bata kai ga cimma ruwa ba ga wani mai nacin kallo ta had'u dashi , a haka dai tayi ta maganganunta tana jan tsaki .
A chan d'akin inna Asabe kuwa bayan Fatima ta fita , bilya ne ya dubi inna Asabe yace " gwaggo wacece wannan dana gani a gidan nan, saboda ban tab'a ganinta a gidan nan ba ", kyab'e baki tayi sannan tace" Fatima mana y'ar kishiya ta da ta rasu " zabura yayi cike da jin dad'i " yauwa anzo wajen ya fad'a yana sosa kai ," baban shi ne ya dube shi , yace ya akayi ne d'an baba , ya fad'a ya sauraronshi," baba dama gaskiya ina sonta kuma so nakeyi na aureta ", tashin hankali Wanda ba'a sanya masa rana , ai inna Asabe ji tayi kamar zata mutu , kallon d'an uwan nata tayi taji me zai cewa d'an nasa " ah Masha Allahu ai hakan ma yayi lallai yayi kyau , ah abu a cikin gida " ita dai Asabe ta kasa cewa komai, shi kuwa bilya murna jin mahaifinsa ya amince , sosai suka yi hira har bayan la'asar kafin su fara shirin tafiya , ita dai Asabe abin duniya ya dame ta saboda tana tsammanin ta yi abin da ba mahalukin da zai so fatima amma ga wata sabuwa, ta aurar da d'iyarta ga d'an birni tana ganin ba wanda zai k'ara cewa yana sonta amma gashi mai kud'i daga birni ya zo yana sonta, sallama yayi mata tare da sanar da ita cewa lallai ta sanar da Fatima halin da ake ciki kuma ba dad'ewa za'ayi ba za'ayi bikin saboda tsananin son abin duniyarta ta kwantar da kai , ya sallameta da kud'i masu tsoka haka shima bilya ya bata najin dad'in cewar ta amince za'a bashi fatima, haka suka yi sallama suka kama hanyar fita daga k'auyen.
A cikin gida kuwa bayan inna Asabe ta shiga kasa zaune tayi ta kasa tsaye , ta saka wannan ta kwance wanchan , duk dai akan Fatima ne da batasan ta auri bilya saboda tasan suna da kud'i kuma batason ta shiga daula tana son tayi ta ganinta cikin tsanani, amma da ta tuna da waye bilya da irin halayensa ai sai ta godewa Allah dan ko ba komai Fatima zata k'unshi bak"'in ciki saboda auren mashayin giya da Neman mata bazai haifar mata da komai ba sai tashin hankali domin kuwa babu kwanciyar hankali , k'arshe ma dai ciwon zuciya ya kamata ta mutu , wannan tunanin da tayi ne ya bata k'warin guiwar tunkarar Fatima da zancen.
🌸🌸🌸🌹🌹🌹🌸🌹
Da daddare bayan Fatima ta dawo daga tallan ta da ta saba , zuwa tayi ta iske Asabe a kishingid'e tana cin nama balagu da ta bayar da kud'i a siya mata wajen idi mai nama , duk kuwa a cikin kud'in da yayan na