ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 11 of 44

kulawa da yarinyarsa haka kuma suka rufe masa baki ta yadda bazai tab'a fad'awa Fatima labarin mahaifiyarta ba. Wannan kenan ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ (ASALIN LABARI) Kwata kwata malam bayajin dadin rayuwar da d'iyarsa ke ciki , gashi yanzu yana halin rashin lafiya mai tsanani ga tsufa ya kamashi, gashi a yanzu ne yarinyarsa take buk'atar kulawa a gareshi . Ranar wata Asabar da safe baraka ta je wajen Asabe , da zancen auren Fatima da Ado tunda ya matsa mata , da sauri Asabe ta amince ga bisa la'akari da tayi na ganin y'an birni in dai sun shigo garin suka d'ora idanunsu akanta su ce suna San ta , iya kuma ba kowa tayiwa burin auren irin wadannan ba sai Abu , ta sanar da ita babu damuwa , amma sai da su ka sanya aka kulle musu bakin malam din , aikuwa tana fada masa ya amince duk da zuciyarsa bataso amma haka ya yadda, lokacin da ya sanarda Fatima bata mu da masa ba duk kuwa da babu Wanda ta tsana a duniyar nan sama dashi,sosai ake tayin shirye shiryen biki , a wannan lokacin ciwon malam yayi tsanani. Ranar wata Asabar bayan Fatima ta dawo daga tallah, sallama tayi a d'akin mahaifinta ya amsa mata muryarsa na karkarwa saboda ita kadai ke kulawa dashi , "Fatima ki yafemin na miki laifi na hadaki da wanda bakya so nasan ban kyauta ba amma ina ganin gwara haka fiyeda ki zauna cikin bak'in ciki , sai maganarsa ta katse numfashinsa yana kai kawo chan kuma sai taji shiru , aikuwa da gudu ta fita tana k'walawa inna Asabe kira ," Inna! Inna! Inna kizo wallahi baba ya rasu mun Shiva uku" da gudu Asabe ta fito ta nufi d'akin malam din abirkice dan ganewa idonta meya faru........ Godiya ta musamman gareku masoyana ina fatan kuna cikin k'oshin lafiya kuma zakuji dad'in karatu , ayi karatu lafiya. Luv u all my dear fan's๐Ÿ˜๐Ÿ˜ Please๐Ÿ™๐Ÿป Share &Comments To be continue........... ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟNussad๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ ๐ŸŒธ๐ŸŒนKishiyar Uwa๐ŸŒน๐ŸŒธ(True Life Story) ๐ŸDaga Alk'alamin Nussad๐ŸŒธ GODIYA GA ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA DAYA BANI DAMAR CI GABA DA RUBUTUN LITTAFINA , MAI SUNA KISHIYAR UWA . GODIYA TA MUSAMMAN GA Y'AN MOONLIGHT WRITERS ASSOCIATION, ALLAH YA K'ARA HAD'A KAWUNANMU AMIN GODIYA TA MUSAMMAN GA Y'AN UWA NA DA ABOKAN ARZIKI. GODIYA TA MUSAMMAN GA FANS DINA , DAMA FANS DIN LITTAFIN KISHIYAR UWA, INA GODIYA SOSAI, INA FATAN ALLAH YA BANI DAMAR KARASA ISAR DA SAK'ON DA NAKESO NA ISAR , KUMA BANA FATAN NA BAKU KUNYA . MASU TURO DA COMMENTS INAJIN DADIN HAKA. INSHA ALLAHU YANZU MUKA NUFA CIKIN LITTAFIN GADAN GADAN , INA FATAN ZAKU BIYONI DOMIN JIN MAI YAKE SHIRIN FARUWA. ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน SHAFI NA7๏ธโƒฃ-8๏ธโƒฃ Koda inna Asabe ta k'arasa cikin d'akin , ganin halin da malam yake ciki ya sanya ta zunduma ihu tana kururuwa , Abu ce ta fito daga d'akinta cikin yatsina fuska tana duban Asabe cikin gadara " wai ke inna ki damu mutane da sanyin safiyar nan baki ganin mutane suna yin bacci", galala Asabe ta tsaya tana kallon Abu cikin ido kana ta dubeta " yo ke dan k'aniyarki kina ganin mahaifinki cikin wani hali amma kuma kika tsaya kina yiwa mutane zancen banza" "ni dai gaskiya ana takuramin wallahi " ta fad'a ta komawa cikin d'aki ta banko k'ofar d'akin, maganar Fatima ce ta dawo da ita cikin hayyacinta " inna bari na duba in baba muhammadu yana nan "( kanin malam iliya ) , bata jira me zatace ba ta fallah da gudu ta bar Asabe na sallallami had'e da tafa hannaye. Ba'afi mintuna biyar ba sai gasu sun shigo cikin azama , kanin nasa ya shiga cikin d'akin da sauri dan ganin me yake faruwa, da Sauri ya dawo ya dubi Asabe "maza shiryashi asibiti zamu kaishi har yanzu da sauran ransa " wata ajiyar zuciya Fatima ta saki kana ita kuma Asabe ta shiga domin shirya shi . Baba muhammadu ne ya shigo shi da samari biyu suka taimaka masa suka Sanya malam a cikin mota , domin tafiya da shi asibitin , Fatima ta k'ekasa k'asa akan tanason zuwa amma Asabe ta hana ta haka tanaji tana gani aka tafi da malam asibitin. Ko da suka k'arasa basu samu wata matsala ba aka shigar da shi d'akin da za'a dubashi , an dubashi anan aka gane yawan tunanin da yakeyi da kuma wani abu da ya ajieshi a ransa ya haifar masa da ciwon zuciya mai tsanani, sosai wannan maganar ta razana k'anin nasa, haka ma Asabe ta girgiza da wannan maganar , ita bama wannan ba me malam din ya ajiye a cikin zuciyar tasa shi take tunani fiye da rashin lafiyar tashi , haka suka gama komai da ake buk'ata kana suka zauna tare da shi. Achan gida kuwa Fatima kasa tsinana komai tayi sai tunanin mahaifinta takeyi, bataso ta rasa shi a halin yanzu da take matuk'ar buk'atarsa a rayuwarta , ya Allah ka dubeta ka Sanya mata tawakkali a halin rashin lafiyar mahaifinta amin. Har k' arfe uku na rana basu dawo ba, lokacin har ta gama abinci da komai da komai na gidan sai dai tallah ne yau kam bazata iya zuwa ba , gashi ta Sanya abinci a cikin kwano tana jiran ko za'a daukawa mahaifinta akai masa , haka tayita zaman jiran amma shiru. Abu ce ta fito
๐Ÿ