NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 10 of 44

taji maimunatu na da ciki shikenan fa hankalinta ya tashi abinda take ta gudu gashi ya faru , da sauri ta garzaya gidan aminiyarta baraka , a tsakar gida ta zube had'e da dafe kai " na shiga uku ni Asabe Baraka tawa ta k'are a gidan malam " ta fad'a cike da tashin hankali " nutsu kiyimin bayani" cewar Baraka wadda ke yiwa Ado wanka a lokacin yana da shekaru takwas da haihuwa," wai wachchan matsiyaciyarce keda ciki " a razane Baraka ta dubeta da gaske kikeyi mun shiga uku , to yanzu menene abin yi "? Ta tambayeta " to ai nima shi nake nema shiyasa na zo gurinki " bara na gama shirya Ado " ta ce tana kokarin tashi" to kawai Baraka tace domin kuwa hankalinta ba'a jikinta yake ba , rana gama shirya shi ta barshi a gida suka dauki hanyar wajen boka , sunyi masa bayani a cikin bayanin kuwa har da son haihuwar da Asabe ta ke son tayi yace musu zai fara ba ta haihuwar kafin nan , aikuwa a take ya sanya aljani ya shiga jikinta a take a wajen ta samu ciki sannan yayi mata alk'awarin sawa malam kiyayyar maimunatu da abinda ta haifa godiya sukayi masa sosai suka tafi gida . Bayan kamar wata biyu da samun cikin Asabe ya bayyana malam yayi murna sosai na tunanin Allah ya dubeshi lokaci guda ya bawa matan sa ciki , a koda yaushe ya kanyi addu'ar Allah ya saukesu lafiya , a b'angaren Asabe kuwa burinta ta haifi namiji kullum burinta kenan, ana cikin wannan yanayin mainmunatu ta fara fuskantar matsala wajen malam gashi cikinta ya farayin nauyi , tsangwama sosai take sha wannan alamu ne na Cesar boka ya cika aikinsa, ana cikin wannan rintsin Allah yayiwa malam mahaifin malam Iliya rasuwa bayan gajeriyar jinyar da yayi Allahu Akbar giwa ta fad'i aikuwa anayi rashi ba Kad'an ba , gashi a wannan lokacin sosai aikin boka ke ci saboda tun iyayensa basu gane ba da 'y'an uwansa har suka gane sosai iyayensa sukayi masa fad'a amma abu kamar tiri , sai ma gaba abin yakeyi ,. Bayan wasu 'yan watanni da rasuwar malam lokacin cikin maimunatu ya tsufa sosai gashi ba kwanciyar hankali , wannan ya sanya ta rame ta lalace , tayi bak'i , abin tausayi ga ba kulawa daga wajen miji sun rigada sun maidashi rak'umi da akala bayajin maganar kowa sai ta Asabe, Allah ya taimaki maimunatu kannensa na zuwa ta tayasu hira dan haka sai damuwarta ta ragu sosai, ana wannan yanayin ciwon nakuda na kamata ga malam baya nan , ciwo takeyi sosai tun dare har safiya amma Asabe na jinta bata koda lek'a ba , ita a burinta ma kawai maimunatun ta mutu kowa ma ya ana cikin haka Allah ya jefo da hadiza k'anwar malam din aikuwa tana ganinta cikin wannan halin ta juya ta sanarda mahaifanta aikuwa basu dade da zuwa ba Allah ya sauketa lafiya ta samu d'iyarta mace masha Allahu yarinya son kowa kyakykyawar sosai, kowa in ya ganta sai ya kara kallonta saboda tsabar kyau, a lokacin da Asabe taji anyi haihuwar an samu mace murna tayi sosai da sosai a ganinta ita zata haifo namijin , haka akayi suna malam bai dawo ba k'anin malam din shi ya sanyawa jaririya sunan mahaifiyar maimunatu yarinya taci suna Fatima, komai y'an uwan malam sukayi saboda yana chan harkar fataucinsa, ko da ya dawo bai wani nuna murna sosai ba duk kuwa da abinda yake nema shiya samu , haka dai rayuwa tayi ta yin juyi da rayuwar Maimunatu da yarinyarta Fatima cikin rashin kulawa da k'unci , bayan watanni hud'u Asabe ma ta haifi d'iyarta mace bataso hakn ba amma kuma ba yadda ta iya lokacin malam yana nan dan haka zo kaga murna da farin ciki ba kama hannun yaro , ranar suka aka sanyawa yarinya zainabu , anyi shagali sosai , a haka rayuwa tayi ta tafiya har Fatima tayi shekara d'aya ko tsakar gida basa iya fitowa, a sannan ne Asabe it a da k'awarta sukayi mata asiri akan in ta tafi karta dawo gidan a lokacin ne aka aika mata da zancen mahaifinta bashida lafiya , da kyar aka barta ta tafi da sharad'in bazata tafi da Fatima ba haka ta barwa mahaifiya malam iliya ta tafi, cike da kewar yarinyarta, Allahu Akbar a hanyarsu ta tafiya Allah ya aiko da wani gagarumin hatsarin motar da maimunatu take ciki tayi hatsari mutane da yawa sun rasu Allahu Akbar Allah ka jik'an musulmi amin, a lokacin da labarin hatsarinsu ya Shiva cikin k'auyen ba k'aramin tadawa mutane hankali yayi ba da kuma aka sanar musu da cewa ba Wanda yayi rai a cikin matafiyan lallai mutanen k'auyen sunji rasuwar tata musamman ma y'an uwan malam dashi malam din , amma Asabe a lokacin ne ma duniyarta ta koma sabuwa ba ta da wata damuwa a haka har aka karaci alhinin rasuwar akabar masu rashi da rashinsu. Bayan kamar data biyar a lokacin Fatima tayi wayo sosai dan haka Asabe ta takura da sai an kawo mata ita ai itama mahaifiyarta ce da kyar iyayen malam suka bada ita, to fa tun lokaci ta fara zan wahala har kawo yanzu ba wanka ga aikin da yafi karfinta shi ake bata tunda ta tashi bata san mecece kulawa ba duk kuwa da 'yan uwan malam na k'ok'ari amma wani lokacin basu ma San anayi ba , babu irin rayuwar da Fatima bata gani ba a gurin KISHIYAR MAHAIFIYARTA data baya da abin ya fara sakinsa sai ya bar harkar fatauci ya koma gona don ya dinga
🏠