NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 99 of 146

a wadda tarihinta yayi bacci gabaki daya bata cikin kowane lissafi, Queen Haile ta karbi kowane irin iko,taqama da isar tsayawa ta tsayar da ‘danta ASIM ga zama cikakken mai jiran gado na karagar mulkin BOYEM kuma hakan ta Zaune dan kuwa masarautar da duniya gabaki daya sun gama shedar da hakan sun gama yadda da sanin ASIM ALMAZ ne Sarkin dazai mulki BOYEM Bayan sultan YASAR sbd shine a tareda mahaifinsa da qasar sa yanzu. Rayuwa ta dawowa Masarautar BOYEM sabuwa dal da Kama hanyar cikar Buri sbd kowa abinda yake tsananin so ne yake ganin yana Kama hanyar samu musamman queen haile wadda komai datake tsananin so shine ta samu hawan ASIM ALMAZ kujeran BOYEM ne kadai ya rage mata Wanda shima a yanzu yanda take ganin kusancin ASIM din da sultan tasan bama zai taba Hana masa ba sbd ya manta cewan yanada wani magajin kwata kwata tinda bai taba yiwa kowa maganarsa ba tinda yabar masarautar da suke ganin kaman ma korarsa yayi amma aka boye cewan karatu ya tafi dan haka haile ta gama samun dukkanin abinda take so itada danta ASIM Wanda yake zuba nasa iko da mulkin a cikin masarautar sbd ganin shine sultan na gaba kuma hakan ne ya saka gabaki daya BOYEM shakkarsa akeyi da basa tsananin girma duk da babu tausayin Jamaa ko daya a ransa amma mahaifiyarsa ta koya masa boye hakan sbd sake samun damar haye matsayin da suke tsananin buri kuma a shirye suke tsaf da iya kashe kowace rai da zata shiga tsakaninsu da abinda suke so dan haka kowa yasha jinin jikinsa akansu, MARAKI ma a yanzu ta rasa dukkanin power datake ita sbd haile ce me yaya take zuba iko da mulkin cikin gida, Hakama imebētis kaf da yayansu da duk wani me matsayi a cikin gida tsananin tsoronta ya ninka a ransu sbd a yanzu itace uwa ga sultan na gaba dan haka babu me iya ko dago Kai ya kalleta komai na mulkin Masarautar ma ya qara tsanani da wasu irin dokar da bayi basuda shaqat ko kadan. MARAKI duk da daman can kishin tsagwaron soyayyar data hango sultan yana yiwa wishmah da ‘danta ne suka sakota gaba ta sakawa zuciyarta zazzafar kiyayyar Ayanah da NUAB sbd bata taba kishin haile ba dan bata taba ganin soyayyarta data ‘yayanta a idanuwan sultan YASAR ALMAZZ kaman yanda taga wutar son Ayanah da danta naci a idanuwa da ruhinsa ba dan hakan a yanzu data shedar da sunyi tazarar da babu Sauran soyayya a tsakaninsu hankalinta ya dan kwanta ta tattara komai ta ajiye ta koma rayuwarta ta Hutu da kwanciyan hankali bata shiga matsalar da duk ba tata ba dan kuwa ko taya HAILE kishin nema wa danta mulki batajin zata iya sbd sanin ba lallai komai Yazo a sauki ba dan tayi imanin da idan ma sunyi nasarar cire Ayanah a idanuwan sultan to ba lallai sun cireta a zuciyarsa ba bare LEUL NUAB dayake jinin AYANAH GHAZ bazai taba fita a zuciyarsa ba dan haka ta cire kanta a wannan fadan iya abinda ta samu ya isheta ita a yanzu dan haka rayuwa sabuwa ta bude itama ta kwanciyan hankali da nutsuwa, Imebētis din sultan kuwa da damansu ahankali ahankali sun rasa rayukansu a hannun uwar dakin tasu wadda a yanzu Bayan ita bata buqatan kowace mace a rayuwar sultan Wanda ya rufe shafin karban kowace imebētin a rayuwarsa tinda ya samu Ayanah ghaz kofar shaawansa ga kowace mace ta rufe kwata kwata matansa ne kadai suma haqqin su ne kadai yake saukewa gashi rayuwar ma tayi tsayi yanzu tsufa da manyanci ya taho musu, A yanzu imebētinsa daya ce rak a raye itama ta jima da komawa tamkar baiwa ga haile ta zama kunnuwanta na dauko mata labarai da sirrin duk inda Hailen bata saniba dan hakanne take raye kamar fanko dan kuwa shi kansa sultan din tintini ya mance da ita baama maganarta a haka zata gama garari a masarautar ta tsufa ta mace, MARAKI batada kowane irin amfani itama a gurin sultan Bayan na biyan buqatan sauke hakkin aure a ganin HAILE kenan Shiyasa bata damu da ita ba ta tattara ta watsar tinda batada ko ‘dan kanta a duniya kuma tanada daman daukan ‘ya daya ko biyu ma daga cikin yayan imebētis din sultan ta riqe tamkar ta haihu amma Sam batada raayin hakan tin acan baya da akwai Sauran yarinta bare yanzu da duka sun manyanta hakama yaran da yawansu gabaki daya an aurar dasu Masarautu manya masu daula da iko daban daban gabaki daya a yayan sultan din manyan yayansa ne kadai basuyi aure ba wato yayan Haile su biyu Aslm da meryam ta ukunsu neesat tayi aurenta sbd rayuwarta akwai sauki sabanin ta yan uwanta, Rashin aurensu nada nasaba ne da rashin shaawan auren da basu da shi sbd raayin hakan da mahaifiyarsu ta cusa musu sbd batason su taba aure Masarautar da batai ko kusan matsayin ta mahaifinsu ba, Duk masarautun da ake aurar da yayan masarautar BOYEM basuyi ikon Masarautar boyem dinba sbd ta boyem din itace wadda babu kamarta dan hakanne dole sai wadda bata kaitaba amma suma Masarautun baa baya sukeba ko kadan ga tarin arziki da dukiyar da bata Jin kashewa tareda iko da mulki me karfi ta qasashe daban daban amma duk da hakan HAILE ta kasa barin yayanta su zaba ko daya daga cikin duk masauratun da ake kawo musu tayin aure gashi a al’adar BOYEM suk
🏠