kanta wato MAA TENYA dinsa da MAA SAKINAH Wainda su kadai ya taso ya gani a rayuwarsu shi da uwarsa,
‘Dan mistress yan uwansa suke kiransa Wanda shi hakan bai taba sosai ransa ba sbd hakan na nuna cikakken identity dinsa kenan da uwarsa wadda akanta shi sunan mistress yafi masa darajar sunan sultan me mulkin qasar gabaki daya,
Tin da qananun shekaru zafi da hayaqi sa ya bayyana ga duniyar masarautar BOYEM dan hakanne ya saka yan uwansa mata fara shakkarsa dan tamkar mahaukacin Zakin da baida hankali ko daya yake ga duk Wanda ya shiga huruminsa da baya buqatar kowa a cikinsa Bayan Mutum ukun nan da sune kadai ya saka a duniyarsa,
Zafi da tiririnsa ya saka zuciyar sultan shiga damuwan abinda zai iya zama sbd babu tsoro ko daya bare shakka a rayuwarsa,
Bai taba risinawa kowa ba a masarautar kaf dinta sbd har abada bazai taba risinawa duk Wanda baya kaunar mahaifiyarsa ba koda hakan na nufin bakin ransa to zai bada ran da hannunsa.
Ta bangare daya Li’ul ASIM ya taso mai tsananin tsoro da rashin wayo da dubara ko kadan,
Baida jarumta,jarumta baida kwazo baida jajircewa hakama baida dubara da tinani ko kadan duk abinda uwarsa ta dorasa haka yake hawa ba lissafi dan hakanne suka taso duniya biyu mabanbanta shi da LEUL kwata kwata duniyarsu bama iri daya bace dan shi hatta matan uban nasa mamaki da shakkar Zafin kasan da rashin tsoron sa sukeyi tareda fargaban abinda zai iya zamowa idan ya qarasa girma.
Da wannan tsoron sultan ya tattara sa yakai sa qasar RUSSIA karatu tareda bada umarnin bazai taba dawowa ba saiya gama karatunsa gabaki daya ya zama cikakken mutum tukuna zai sako Kafa a masarautar.
Wannan hukuncin ya masa Zafi da ciwo amma kuma sbd mahaifiyarsa da saiya tabbatarda tabar hannun sultan ta dawo hannunsa gabaki daya har qarshen rayuwarta ya Aminta ya tafi dan kafa duniyarsa da bayason ko kadan ta hadu data masarautar daya tsana a zuciyarsa fiyeda komai.
A hannun tenya da sakinah a tafi yabar mahaifiyarsa data kasa barinsa ta qanqamesa saida aka banbareta daqyar tana kukan da fiyeda shekara nawa bataiba sai yanzu da aka rabata da danta dan haka Bayan tafiyar sa rayuwarta ta sake komawa inda ta fito.
Barin NUAB ALMAZ qasar BOYEM ya bawa HAILE cikakkiyar damar fara yaqin maida danta cikakken jarumin da babu tsoro ko daya a zuciyarsa sbd sultan ya dorawa a mulkin dayake shakkar Dora NUAB ayanzu sbd zafinsa dayayi mummunan yawa,
A Morocco qasar iyayenta aka tura ASIM karatu amma shi yana zuwa Hutu a duk lokacinda yaso sbd Sam taqi yadda dayayi nisan dazai hanasa samun kusanci me karfi da sultan Wanda yasan a yanzu ne yaqi da qalubalen matsayin magajin BOYEM zai fara irin Wanda zai kawo fitina daban daban a tsakanin magajin biyu da duniyarsu ta banbanta,
Babban abinda yake saka zuciyar sultan girgiza shuke irin rayuwar da NUAB zaiyi a kusan shekaru masu yawan gaske batareda mahaifiyarsa da itace duniyarsa ba wadda shi kansa ayanzu bayajin har abada duk yanda zai shareta zai iya rabuwa ko barin ta fita hannunsa dan da itace zai iya riqe NUAB a hannunsa.
A ranar da NUAB ALMAZZ BOYEM yabar qasar a daidai wannan ranar aka bugo daga daular YUNAR dake kuwai imebeti zuhrah ta haifar masa yan biyu namiji da mace Wanda tukuicin haihuwan biyun a lokaci daya ya saka ya yantata tareda aurenta ya maidata cikakkiyar matarsa.
Koda labarin ya isowa su sakinah sujjada sukai cikeda tsanani farin cikin daya jima shekaru da barin rayuwarsu sbd Ayanah,
Kallan Ayanah sukai dake Zaune zuru suka fara fada mata amma bata ce komai batai reacting ko wane iri ba saima binsu takeyi da ido batareda ta tina matsayin Zuhrah akanta ba sedai suka gaji jiki a sanyaye suka kyaleta tinda dai ba haukacewa tayi ba memory kawai tayi loosing da walwala sai suke Jin sassauci a zuciyarsu hakama Bayan tafiyar NUAB babu ranar da baya video call da dukkaninsu yana magana da mahaifiyarsa da shi ne Wanda yake saka aji sautin muryanta Wanda a haka shekarun suka shude tamkar a mafarki.
#MAMUH
#THE BEGINNING
#THE GREAT LEUL NUAB ALMAZZ BOYEM
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
47
Masarautar BOYEM mai cikeda tarihi daya gabata na can baya qarni qarni da tarihin daya gabata a shekarun da basu Kai qarni qarni ba haryanzu tana cikin wadataccen arzikinta da daular datake sake ninkuwa ako Yaushe sbd arzikin da Allah yayi musu Wanda baya qasa koyaushe sedai gaba,
Shekarun da suka shude anyi su ne a cikin tinani da wasi wasin waye zai zama magaji a cikin jini biyu da sultan YASAR me mulki haryanzu daya haifa?
Akwai ‘dan asalin matarsa uwargidansa wato queen haile wadda take zuba taqama da ikon da kaf masarautar ake shakkarta Bayan sultan idan aka cire manyan fada wainda sune fada,
Itace macen datafi kowace mace daraja haryanxu a masarautar da wajen masarautar sbd tini aka shafe tarihin fada da tsantsar soyayyar da sultan yakewa wishmah dins