NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 97 of 146

urinta daya ne kota yaya Ayanah da NUAB subar zuciyar sultan da duniyar gabak daya ita kuwa maraki zuciyar sultan takeson Ayanah ta Bari kwata kwata. *****da farko Bayan dawowan Ayanah daga Germany lafiya kalau ake kaita kwana gurin sultan dayake nuna mata kaunar da babu me nuna mata ita a duniya amma a hankali ahankali hakan ya fara ragewa, A haka haka su NUAB suka fara girma an yaye su sunfara wayo sosai da girma, Sultan dayaga babu sauki a rayuwan Ayanah dake rasa rayuwanta sauyi me girma ya kawo a rayuwarta daya fara mantar da ita rayuwarta ta baya batareda saninta ba, Likita daya mace da amanarta take daban data duka likitocin masarautar ya bawa umarnin Dora Ayanah Akan maganin da zai maidata weak ta mantar da ita rayuwarta data rasa koma wace iri ce sbd ta dena magana kwata kwata, ***Ahankali ahankali Ayanaah ghaz tafara manta rayuwarta da wace ita tana zama weak tamkar batada amfanin komai a rayuwa, Duk wani qunci da baqin cikin rashin yan uwanta ahankali ahankali yafara barin kwakwalwanta yana shafewa, Mutum biyu ne suka tsaya cak qyam a ranta da ko a cikin baccinta su kadai take gani babu memory dinsu ko daya daya fita a kanta sune ABAAS da NUAB, Memory din Abaas bai taba fita kanta babu kuma tinaninsa ko daya daya fita a kanta amma Sauran yan uwa sa iyayenta Sam tinaninsu shafe mata yake ko ta tinasu sai tanajin su tamkar baqi a cikin kanta, Tsananin so da kaunar datake wa dan uwanta Abaas itace ta zama abinda babu dare babu rana take tinani da Jin bazata iya rayuwa ba batareda ta sake sakasa a idonta ba koda ranarta ta karshe ce a duniya tanason Allah ya hada fuskokinsu. Rayuwa tana qara ja sultan yana qarasa janye dukkanin wata kulawansa da soyayyar sa Akaan wishmah da NUAB Wanda yafara girma a cikin tsangwamar yan uwansa dasu HAILE Akan zamtowansa dan mistress wadda batada cikakken hankali koyaushe shiru take tamkar hoto a Zaune, Tenya tana cikin qunci mai tsanani da damuwan da itama ta zamar mata ciwo ahankali ahankali Akan yanda sultan ya cire Ayanah da danta kwata kwata daga ransa da lamuransa a yanzu ASIM ne Wanda yake nunawa duniya yafi kauna Wanda hakan ya saka HAILE ajiye maganar Ayanah da NUAB kwata kwata sbd ta samu abinda take so, MARAKI ma kusan Bayan lokaci yaja sosai ta ajiye Ayanah daga ranta sultan dayayi watse dasu itada danta Ayanah din ta koma tamkar macen da batada amfani kwata wata a rayuwarsa dan kuwa ko sauran imebētis din sunfita gata da matsayi a Masarautar, Wannan dalilin ne ya saka a yanzu babu Wanda yake b takan Ayanah da danta sun koma tamkar wainda babu su a masarautar labarinsu ya shafe babu me Tinawa dasu rayuwa ce sukeyi a cikin qunci da gori da tozarci a tsakanin iyalan sultan din Wanda duk abinda yake faruwa yana sane, Sakinah da tenya sune gatan Ayanah da NUAB da suke tsaye akansu dukda a rayuwar Ayanah yanzu kamar hoto ce babu abinda takeyi ko kukan ma yanzu tintini ta dena iyaka cinta ido a komai, Abu Daya ne yake motsa zuciyar wishmah AYANAH GHAZ shine soyayyar ‘danta LEUL NUAB ALMAZZ BOYEM sai kuma dan JININTA ABAAS kaman yanda take fadawa dan ta sunansa a kunnensa koyaushe zata ce masa ‘BANASON MUTUWA BAN HADU DA JININA ABAAS BA,KAFIN NA MUTU NUAB KA CIKAMUN WANNAN BURIN SHI KADAI’ Wananna shine kalmar da NUAB ya tashi da ita a cikin kunnuwansa da zuciyarsa wadda shine kadai abinda kawai mahaifiyarsa ke iya furta wa koyaushe, Shi kadai ne takewa magana a rayuwarta Wanda shima duk maganar da zatai masa saita fada masa hakan dan hakanne maganar ta girku ta kafu a zuciyarsa tin yana qaraminsa dan hakanne tin yana qanqani ya fara girma da wannan Alkwarin na cika wa mahaifiyarsa wannan burin koda kuwa zai rasa rayuwarsa da tsallake mutuwa dari. ********LEUL NUAB Ya taso ya rayu a cikin masarautar datake ta ubansa cikin baqin cikin ganin rayuwar da mahaifiyarsa takeyi a cikin matansa da imebētis dinsa, Mahaifiyarsa itace rayuwarsa da zai iya komai da tsayawa gaban kowa akanta, Mahaifiyarsa itace fullstop dinsa da akanta ne kadai yake iya tsayawa ga duk abinda yakeji, Matan sultan suna Qinta, Yayan sultan suna qinta, Imebētis din sultan suna qinta, Yayan imebētis din sultan suna qinta, Manyan fadar masarautar BOYEM suna qinta, Shi kansa sultan din yana qinta….. Hakan daya taso yana gani ne a bayyane ne ya saka zuciyarsa fara bushewa daga dukkanin wata kauna datake duniyar gabaki dayanta, Ciwo yakeji mai Zafin gaske, Radadi yake ji mai azabar gaske, Fushi yake ji mai wutar gaske, Rashin kauna yakeji ga kowa mai karfin gaske duka sbd Shi itace rayuwa da duniyarsa gabaki dayanta, Bai damu da rashin kauna da shaquwan dake tsakanin sa da ubansa da duka wani jininsa ba sbd baya buqatan kauna ko soyayyar kowa a duniyarsa iya ta Amminsa da babu wata rai me daraja a gurinsa Bayan tata sun ishesa, Mutum biyu ne rak a duniyar Bayan mahaifiyarsa daya cirewa hular Zafi da tiririn da kansa yake fitarwa sune Wainda su kadai ya taso da sanin masu kauna da kulawan Amminsa da zasu iya bada ransu a
🏠