NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 96 of 146

ya Allah ya maidata abar tausayin da kowane lokaci zata iya barin duniya. Tenya da sakinah da duk bayin da suke bangarenta suna cikin tashin hankali da damuwan da batada sauki a cikinta ko kadan sbd ganinta kadai Wani irin kuka mai tsima zuciya yake saka sakinah da idanuwanta harsun fara qanqancewa. A kuma daidai wannan lokacin yar uwarta daya tak datake da ita a duniyarta datake mutuwa dan babu tabbacin rashinta a wannan kwanciyan datake duk wani mai kaunarta kuka a wannan lokacin ne ake maidata cikakkiyar macen da itama tata zuciyar gap take da bugawa sbd daci da mataccen yanayin dake cikinta tareda sanin yar uwarta na can rai a hannun Allah a lokacin sbd labarin masarautar a take ake sanarwa dan kowa ya kiyaye. ******koda gari ya waye sultan yana Zaune a daddumar da yayi sallah sbd koda minti daya bai rintsa idanuwansa ba rokon Allah yakeyi yana qarawa ya raya AYANAH GHAZ koda shi ne zai tafi a madadinta zaiyi fatar ta rayu sbd dandana farin cikin da bai taba gani a idanuwanta ba ko so daya, Yana fatar ta rayu taga abinda ‘danta zai zama koda hakan zai bata farin ciki da murmushi koda so daya ne a rayuwarta kafin mutuwarta hakama bazai taba son NUAB ya rayu a hannun kowace macen daba mahaifiyarsa ba dan haka ya ringa fadawa Allah ya tashi kafadanta. Masarautar BOYEM ta dauki zafi dan kuwa duk manyan likitocin qasar kaf suna cikin masarautar dan Neman lafiyar Wishmah wadda take sake fading kaman ba macen da kyanta yake cike Idon duk mai kallanta ba. Tenya da sakinah ne tsaf a gurin kulawa da bada kariya ga NUAB Wanda Bayan sultan kaf duniya babu Wanda yake daukansa sai su biyun sbd tsaro, Ita kanta wishmah din tsaro sosai sultan ya saka a bangarenta na gaske dan kuwa akwai barazana sosai da hadari a yanayin datake yanzu dan haka sosai aka saka ido da tsananin tsaro babu me shiga gurinta idan ba doctors da tenya da sakinah ba sai kuwa shi mai gayyar Wanda hakan y saka HAILE kusan rasa hankalinta. Tinda aka kafa tarihin masarautar BOYEM babu Sarkin daya taba taka kafafunsa Yazo dakin macensa sai sultan YASAR Wanda hakan ya kafa Wani irin tarihi mai girma da shakka a zukatan matansa da manyan fada da suke ganin kaman zai iya rasa kansa Akan wishmah dinsa dan haka suka fara janyewa daga kaunarta rashin yadda da yar tsana na maye gurbin. MARAKI ma da batada matsala zuwan sultan bangaren ya saka hankalinta tashi ta qullaci Ayanah har zuwa matakin karshe tana yadda da itace macen data samu zuciyar da shekarun aurensu da jininsu bai samar musu ba dan haka kishinta ya fara komawa qiyayya me karfin gaske datake Neman take ta HAILE a fili. *****A Karan farko da tsoro da shakka suka darsu a zuciyar sultan me BOYEM gabaki daya sbd ganin macen da zai iya bada rayuwarsa dan karewa tako Ina hadari mai girman gaske yana dabaibayeta dan kuwa manyan fada da gaske a yanzu sun janye duk wata alfarmar su da kaunarsu akanta da gaske a iya matsayin mistress din suke kallanta, Hakama bangare daya zazzafan kiyayyar maraki akanta ta fito fili ga kuma HAILE da ita har abada yasan idan tanason abu zata iya komai akansa dan haka rayuwan Ayanaah daya NUAB bazata taba fita hadari da halaka ba a masarautar. Damuwa mai tsananin gaske da tsaro ya qara Akan Wanda yake basu gashi har lokacin bata farfado ba, Sakinah ma da tenya ta ko ina komai yayi musu zafi dan kusan so uku duk tsaron da ake bawa bangaren Ana samun attempt ta kawo karshen rayuwarta. Da wannan tashin hankalin sultan da kansa ya dauketa daga qasar zuwa Germany. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_ Mamuhgee 46 Daga sultan har su tenya saida suka isa qasar Germany suka samu nutsuwan jinyar wadda cikin ikon Allah ta farfado amma bawai samun lafiya gabaki daya ba, Farfadowanta sabuwar damuwa ya haifar musu sbd gabaki daya ta sauya daga Ayanah zuwa wata halittar daban, Baqin cikinta ya ninka, Quncinta ya ninka, Damuwanta ya ninka, Shiru da rashin kuzarinta ya ninka sosai ta yanda bata magana kwata kwata hakama bata kallan kowa NUAB ne kadai Wanda take kalla a koda Yaushe. Wata hudu suka share a qasar Germany na jinya kafin sukai guda daya na hutawa suka tattaro suka dawo BOYEM inda tarin abubuw suke jiransu ciki harda sabuwar rayuwar da basu tana tsamammanin Ayanaah zata samu ba daga sultan dan kuwa sauyi ne me sanyi yafara nuna mata ta hanyar dauke kulawansa kwata kwata akanta da NUAB a bisa wani sirri da shi kadai yabar wa kansa, Masarautar a yanzu ta dauki Zafi iya zafi na kowa ya zabi inda zai tsaya sbd shirin karban matsayi da mulki tako wane Hali idan lokaci yayi, Asalin bayyananniyar qiyayya da tsana me Zafin gaske ake nunawa Ayanah a bayyane tareda rashin imani dan kuwa koyaushe cikin ciwo take da aman jini Wanda ya saka take kokarin rasa ranta gashi maraki da imebētis din sultan sun hade Kai guri daya duka a qarqashin HAILE wadda ita babban b
🏠