NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 95 of 146

shin hawayen dake cikinsu zuciyarta na harbawa da Wani irin karfin dayake nuna tashin isashiyar lafiyan zuciya sbd jikinta ya karba yanayin daya tabbatar mata da Zuhrah ce a bayanta, Daqyar gangar jikinta ta dawo aiko daga wutar data dauke ta iya motsa kafafunta ahankali tana juyowa hannuwanta na rawa ta damqesu tareda qarasa juyowa gabaki dayanta ta fuskancesu suna bayanta daga nesa kana tsaye, Akan Zuhrah jajayen idanuwanta da taka suka ringa rikida suna qara rinewa suka sauka tana tsaye tsakiyar tenya da babbar baiwar da aka ware mata tareda wasu bayin sunkai goma a bayansu, Navy blue Kayane a jikinta da adonsu yake daukan ido fuskanta a rufe da mayafi mai Shara shara da ake iya ganin fuskanta amma ba sosai ba hakama itama tana iya ganin na waje amma ba sosai ba, Kasa motsawa Ayanah tayi daga inda take tsaye hakama idanuwanta basu motsaba daga kafe Zuhrah datai dasu kaman yanda zuhran itama ta kafeta da nata idanuwan dake son tsiyayo hawaye amma sun qafe qaf sbd halinda zukatansu ke ciki, Tsananin son ganin fuskan Zuhrah ne Ayanah taji yana danne kirjinta kaman zai kasheta amma Dukkaninsu babu Wanda yakeda ikon bude mayafin daya rufe da fuskarsa batareda ya isa ga Wanda shine kadai yakeda ikon budewa ba dan haka basuda daman ganin fuskokin juna da suke tsananin doki fiyeda komai na duniyar, Tsit duniyar tayi musu da gurin ma gabaki daya, Rawa jikin Ayanah yakeyi ahankali tanajin kafafunta na kasa daukanta bakinta wata rawa yakeyi amma ya kasa budewa dan ta Ambaci yar uwarta, Zuhrah kasa riqe kanta tayi ta daga kafarta tayi Taku daya dan zuwa ga yar uwarta amma tenya ta saka hannu ta riqe hannunta daya batareda tace komaiba ta girgiza mata Kai tana Hana idanuwanta cikowa da hawayen tausayinsu sbd iya abinda zata iya musu kenan na ganin juna amma bazasu taba magana ko rungumar juna ba Bare nuna sanin juna sbd tarin bayin datake tareda su da kuma cameras dake koina dan haka haka sake riqe hannun Zuhrah dake Wani irin rawan jiki tayi gam tana dagowa ta kalli Ayanah dake tsaye kaman an dasata ko baa fada ba kowane lokaci zuciyarta zata iya bugawa dan haka Juyawa tafara yi da Zuhrah a hankali zasu bar gurin Ayanah ta Lumshe ido ahankali ta rufe tana kokarin zubewa kan gwiwanta sbd kafafunta da suka gaza sakinah tayi saurin riqota duk da NUAB yana jikinta, Zuhrah ma kasa daukanta kafafunta ke kokarin amma tenya ta hanata kaiwa qasa ta tareta jikinta suna ci gaba da tafiya can qasan kunnenta ta rada mata ‘Kada ki Bari sadaukarwar yar uwarki da rayuwar data zaba miki ta tafi a banza dan sbd ki samu rayuwar da zaki rayu da aminci ta zabi rabuwar koda hakan zaiyi sanadin mutuwarta ta riga ta zaba inganta rayuwarki dan haka ki saka dangana indai kunada rabon sake haduwa Allah zai hadaku cikin yadda da amincinsa idan kuma babu rabon sake haduwan shikenan kuwa juna fatan alkhairi ko a raye ko mace amma daga nan kaddarar ku ta riga ta rabu’ Wasu irin hawaye masu tsananin Zafin da Zuhrah batasan dasu bane suka gangaro daga idanuwanta suna sauka fuskarta tanajin tamkar an zare mata Wani hasken rayuwarta yabar jikinta dan haka tenya tafara tafiya da ita batareda tasan inda take Dora kafafunta ba har suka bace wa gurin batareda kowannensu ya sake waiwayowa ba har suka bace sukabar su Ayanah gurin tsaye wadda ta kasa dauke idonta daga Zuhrah harta bace wa ganinta ta sake rintse idanuwanta ahankali tana Jin Wani nauyi ya danne kirjinta daya saka numfashinta kasa fitowa ta daga hannunta ahankali tana son dorawa Akan kirjinta amma hannun bai qarasa isaba bakinta ya feso Wani irin jini da karfin gaske daya fesu a Fuska da showel din NUAB dake hannun sakinah. Jajir idanuwanta sukai tana bude su ahankali zata sauke Akan ‘danta hakan bai samuba ta zube a gurin, Wani irin gigitaccen raruma sakinah takai mata tana rungumota jikinta ta hada da NUAB data kasa bawa kowa tana kankamesu tafara kiran sunan Ayanah din da karfin gaske koina nata ma rawa da shiga mafi girman rudanin rayuwarta, Bayin dake tsaye suma duk tashin hankalin suka shiga inda take akaje da gudun gaske aka kirawo doctors aka dauketa zuwa bangarenta cikeda matsanancin tashin hankali da rikice wa. Babban tashin hankalin da Masarautar ke shirin shiga shine rasa macen da a wannan Daren duk Wanda yake Masarautar ya tabbatarda itace cikar rayuwar sultan YASAR ALMAZ BOYEM dan kuwa take a qanqanin lokaci wishmah ta zama abar tsananin tausayi da tsoro sbd yanda ta koma fara tas tamkar babu digon jini a jikinta hakama babu alamar ma zata farfado dan hakanne likitocin dake kanta hankalinsu ya tashi da suka gama tabbatarda ciwon zuciyane mai tsananin gaske yake Neman rabata da ranta da a yanzuma basusan yaya ma zasu fara ba dan kuwa tinda ta riga ta fara aman jini abin yayi Nisan da sai wani ikon Allah. Mummunan labarin na isa kunnuwan sultan kasa yadda yayi da zai rasata dan haka da kansa ya iso cikin bangaren matansa a Karan farko ya isa bangaren Ayanah wadda take kwance fayau dasu oxygen da komai kamar ba ita ba a lokaci da
🏠