m tsaye sbd yunwa da wahala hakama fatarta tayi duhu gabaki daya ga gashinta duk ya zama abin tsoro da qyama,
Suna barin gurin tenya ta aika baiwa ta isarwa da wishmah sakon Zuhrah ta fito kurkukun da babu komawa insha Allah har karshen rayuwarta.
Sakon yana isowa wishmah Lumshe idanuwanta tayi ahankali tareda silalewa qasa tana bin bango ta zube qasa tana bude idanuwanta Akan sakinah data riqeta tanason magana ta kasa sai kawai ta sake rufe idanunwata tana dora hannunta daya Akan kirjinta dake mata radadin azabar da har abada bazai dena ba sai ranar da ranta yabar jikinta dan kuwa baqin ciki ne da quncin da baida magani.
Sakinah da samun yancinta bai saka taji zata iya barin Ayanaah ba har abada itama sanyaye jikinta yake hakama ta shirya zama baiwar Ayanah har qarshenta ko da yanci ko babu yanci zata bauta mata ta kuma bauta ma ‘danta har girmansa.
******acan tenya kuwa Kai tsaye bangaren gyara ta isa da Zuhrah ta fara bada umarni aka wanke Zuhrah tas aka ringa cire datti harma da wasu qananun qwari a jikinta tsawon kusan wuni guda,
Taso a yanke gashinta amma sbd imebeti zaa turata tana buqatan dogon gashin dan haka sai aka barshi shima ya ringa Shan wanki kan wanki,
Ana gamawa gyaran kafafunta da hannuwanta akai na farce tukuna aka kirawo likitoci suka duba lafiyarta,
Magani dasu multivitamins aka bata sai kuma tenya data bada umarnin aka hado mata mai na gargaji dayake goge tabo a qanqanin lokaci dan goge tabon raunikan data yiwa kanta duk da sun warke sun fara bace wa da disashewa saura dakan Wanda shine kila bazai fita ba sai sun hada masa da magani.
Har dare sosai tenya bata huta ba tana kan lamarin Zuhrah da babu wani lokacin batawa matiqar tanason jefata a matsayin imebēti tana buqatar tsayuwan gaske a gurin gyaranta.
Ayanah kuwa a nata bangaren tinda Zuhrah ta fito sai taji jikinta yayi sanyi ta sake raunana da komai,
Ta bawa sakinah dukiya me yawa Akan ta tafi ta samu yanci tayi rayuwarta amma sakinah Sam bazata iya barinta ta kafe zata zauna da ita har karshen rayuwa,
Batada Sauran walwalan daya rage mata kokuma shaawar rayuwa dan haka bata takura sakinah dinba dan kuwa daman ita kadai ce a yanzu ta rage mata a asalin rayuwarta hakama tana buqatan Wanda zai tsaya mata ya tayata bawa danta kariya duk da ta zabar masa yancin zabar abinda yakeso da kansa ba tirsasawa tin yanzu Akan mulkin datake tsoron kada a illata mata shi akai,
Hakaman tayi hakan ne dan basa kariya daga masifu da hadarin da zai fara fuskanta ta ko ina tin yana jinjirinsa so yanzu zaa bar mata shi yayi rayuwa a cikin aminci tinda an riga an cika mata wannan alkawarin sai kuma idan ya girma idan yanada raayi hakan zai zama barazana ga Maqiyansa da masu so.
A bangaren sultan YASAR kuwa Ayanah ghaz tayi masa babbar sukar data rage mata matsayi a zuciyarta dan kuwa duk irin soyayyar da jinin BOYEM zaiwa mace baya taba sauya abinda yake yawo a jininsa dan ako Yaushe harkar mulkinsu da iko tareda abinda suke Buri yana gaban kowace irin soyayya da kauna,
Duka shekarun daya Debo na tsananin burin samun ‘da namiji sbd hakan ne,
Sbd tabbatarda magaji Akan karagarsa bama batareda ko yanada raayi ba ko bayada raayi amma a Karan farko na tarihin masarautar ta zabawa ‘danta kaddararsa tin yana zanin haihuwansa,
Yanada wani magajin Bayan NUAB da zai iya gadon karagar amma abinda tayi masa ya sakasa Jin ko zata rasa ranta sai ‘dansa da yayi raayi ya mulki BOYEM koda hakan na nufin fizge ta daga matsayinta sedai amma zuciyarsa na kasa barin sa ga aikata hakan dan kuwa kaman yanda jinin BOYEM da bazai taba barin burinsa ba yake a jininsa haka soyayyarta take a jininsa dan haka idan bazai iya cireta a zuciya da jininsa ba to zai iya cireta daga dukkanin qudurinta da bazai taba cika ba.
Haile a yanzu ne ta samu damar sassautawa zuciyarta ta fara Neman lafiyarta da gaske dan kuwa a yanzu ta samu tabbacin tanada dama me karfi ta qwatowa ASIM matsayinsa da aka bawa ‘dan mistress,
Bazata taba hutawa ba ko samun bugawan zuciya daidai har abada idan ba ganin ASIM BOYEM tayi ba Akan kujeran mulkin BOYEM,
Batada Buri ko kudirin daya wuce saka ASIM a zuciyar sultan YASAR fiyeda dan mistress dinsa,
Zata tabbatar ta dawo da matsayi da ikonta a hannunta na juya rayuwar kowace macen datake imebētinsa,
Zata ninka tsoronta da zafinta akansu ta yanda bazasu taba iya kallan Ayanah da ‘danta da darajar data wuce mistress ce da dan mistress dan kuwa a yanzu ne zata tada asalin rashin imaninta Akan abinda takeson ‘yayanta su mallaka,
Ko rai nawa zata kashe batada shakka zata kashesu tamkar dabbobi sbd saita tabbatarda Ayanah ko kallan inda take babu me yi bare bata girman matsayin datake dashi.
****Burika ne suka cike zukatan dukkanin masu jinin sarautar BOYEM Wanda hakan ya fara bayyanarda wasu manyan Zafafan hadari da rayuwa zata fara fuskanta dan kuwa a qanqanin lokaci kadan bayin Ayanah uku suka rasu batareda ansan menene yake ajalinsu ba amma kuma masu bincike sun tabbatarda koma menene kama