una inda aka tanada dan zamanta da nasu take aka fara gabatar da kosher din Wanda yake tamkar daurin aurensu ne zaayi.
Dukiyar kosher datake tamkar sadaki aka gabatar daga jinin BOYEM na manyan cousins din sultan dake qasashe daban daban suna rayuwar mulki da daula tareda hutawa a qasashen turai daban daban dayake dik jinin BOYEM indai suna raye ko a ina kake Ka Halarta dan haka masarautar take shaqe da masu duniya a hannunsu.
Irin dukiyar da aka bayar ya saka masarautar jijjiga take aka karba dukiya aka bawa jakadiyarta sbd itace gatanta wadda kadai take da ita aka fara adduar kosher din tsawon lokaci kafin aka rufe da Amin Wanda Amonsa sbd yawa ya ringa amsawa har wajen Masarauta.
YUNAR KAREEM ALMAZZ BOYEM Shine babban dan wan mahaifin YASAR Wanda yake Zaune a qasar Kuwait da matarsa daya da Yaya uku sai yaya hudu daga imebētinsa daya dan haka shine ya isar da cika Burikan wishmah guda uku Wanda Kai tsaye budar bakinta idanuwanta a kafe kan NUAB dayake kan kafafunta muryanta na tsananta sanyi da karfin Hali tace Abu na farko datake so shine a yanta bayi dari a cikin bayin dake kurkukun masarautar,
Sai Abu na biyu shine tanason a ‘yanta mata baiwarta daya tak sakinah,
Na ukun shiru tayi zuciyarta na yin Wani irin rauni da sanyi ta dago idanuwanta da sukai ja ta saukesu Akan sultan tace tanason ko tana raye ko baya raye idan NUAB ya girma kada a tirsasata hawa mulkin Masarautar BOYEM matiqar baida raayi idan ba shine yayi raayi ya hau dan raayin Saba.
Tsit kowa yayi koina ya dauki Wani irin shiru mamaki na kashe kowa musamman sultan da HAILE da Wani irin sanyi a Karan farko ya dan ratsa zuciyarta ta kafe Ayanah din da ido tana mata kallan mahaukaciyar data rasa tinaninta dan kuwa batada labarin cewa tinda ta fada wannan burin saiya cika koda zata mutu Akan sauya hakan,
Tayaya zata ce idan danta baida raayi kada a basa mulki?
Ta kuwa san menene samun mulkin Masarautar BOYEM?
Sultan kuwa kafeta yayi da idanuwansa Wani irin daci mai karfi yana Sosa zuciyarsa dan kuwa tamkar Kai tsaye ta kallesa ta yaga burinsa daya kullata koda zai mutu ne ta yaga a gaban idonsa,
A matsayin datake dashi harta isa samun wannan tinanin?
Menene nufinta na fara lalata burinsa Akan dansa tin yanzu?
Tabbas tayiwa burinsa na shekara da shekaru tabon da har abada bazai goge ba musamman idan abinda ta fada din ya tabbata.
Manyan fada dik da shock din da suka shiga take aka sanar babu burinta da baama gama cika wa dan haka take aka bada umarnin a saki bayi dari biyu ma da suke kurkukun,
Sakinah ma take aka yantata tareda kyauta me tarin yawan data saka Ayanaah din rufe idanuwanta ahankali hawaye masu dumi na gangaro mata sbd samarwa sakinah yancin da sukam bazasu samu ba har abada.
Har tsakar dare sosai Ana hidimar sai kusan gap da asuba aka gama kowa ya watse zuwa masaukinsa.
Washe gari da sassafe aka saki bayin da akace a saki,
Koda aka fara fitowa dasu tenya na bakin kurkukun dan cika sabon aikin daya hau kanta na hadawa mai girma YUNAR BOYEM sabuwar imebeti a matsayin tukuicin dukiyar kosher daya bayar ta wishmah daga mai girma sultan YASAR,
Tin farko tasan daman zaa bada tukuicin imebeti ga duk Wanda ya bada dukiyar kosher din wishmah a matsayin tukuici Shiyasa ta fadawa Ayanaah sadaukar da zatai na rabuwa da Zuhrah har abada sbd ita zata bayar dan hakanne zaisa itama ta samu rayuwar da har zata haifa nata yayan amma sun yafe juna kenan har abada sbd daga ranar da aka gane jininsu daya duka su biyun zasu rayuwarsu matiqar ba yayansu sunyi girman da zasu sassauta musu hukuncin hakan ba kuma a yanzu Ayanah ta yadda da hakan matiqar zasu rayu Zuhrah ta Gina tata rayuwar harma zuriar kanta,
Hakanne ya saka tenya take tsaye a lokacinda aka fito da Zuhrah wadda ta fita kamanninta gabaki daya Kai tsaye gurin duba lafiyarta tasaka aka wuce mata da ita dan shiri da gyaran gaggawa zaa fara yi mata na tsawon wata daya cif kafin a Kai masa ita ya wuce da ita qasar kuwait.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_
Mamuhgee
44
A daidai lokacinda Zuhrah ta sako kafarta wajen kurkukun fata shafe Sheka daya da watanni a ciki a daidai wannan lokacin Ayanah ghaz datake tsaye zuciyarta na Wani irin harbawa da Wani irin zallan kewar datake ratsa ruhi da zuciyarta kafafunta na dan rawa tanaji a jikinta Zuhrah na cikin halinda itama take tsananin son ganint su shaqar da rahamar ganinsu.
Sakinah dake tsaye gefen Ayanah din itama zuciyarta cike take da yanayi na sanyi da mutuwar jiki tareda tsananin so da kaunar ganin Zuhrah wadda shikenan wannan Karan sun rasa juna kenan da gaske har abada.
Tenya ma dake tsaye wajen kofar kurkukun zubawa Zuhrah idanuwanta tayi babu kyaftawa tana Jin tsananin tausayin Ayanah da zata iya rasa ranta idan taga Zuhrah a halinda take ciki daidai wannan lokacin.
Barin sukai da zuhran wadda bata iya Miqewa qya