su dukansu biyun dagowa suka kalleta ta kafe idanuwanta Akan Ayanah da sauti me cire tsoron hadarin da zasu iya shiga su dukan tace
‘Kinada alfarmar fiddo Zuhrah daga kurkuku amma bakida damar ‘yanta ta sbd hakan zai iya zamowa hadari fiddota da yantata,
Kinada matsayin wishmah dazai Baki cikakkiyar daman da zaa cika miki Buri uku na rayuwarki,
A ranar da zaayi bikin sunan NUAB a ranar zaa yi taron Baki cikakken matsayinki na wishmah a kuma ranar ne zaa Baki damar fadar Buri uku da kike dasu Wanda Kina fadar su Sai an cika miki su,
Bazan fada miki abinda zaki fada ba sbd bansan burin da kike dashi ba a rai amma dai zan fada miki Abu daya idan har kinason zuhrah ta rayu rayuwa me kyau wadda ko bakwa tare zata samu rayuwar nutsuwa da kwanciyan hankali Wanda hakan shine burinki to kada ko fiddata daga kurkuku kuma ki yantata a lokaci daya dan kuwa kika yin hakan Zaki iya rasata gabaki daya dan sedai ki tashi Washe gari ki ga gawarta kwance a gabanki,
Na miki alkawarin Zuhrah zata samu rayuwa me kyau da gata tareda kwanciyan hankali amma idan zaku iya sadaukar rabuwa da rayuwa batareda juna ba har abada…..
Wasu hawaye ne masu dumin gaske suka gangaro daga idanuwan Ayanah tana kasa dauke kallanta daga tenya cikeda Wani irin yanayin dayake sassara rayuwarta zuwa matakin qarshe na qunci da radadin zuciyar datake mutuwa daga Sauran walwalan rayuwa.
Itama sakinah rintse idanuwanta tayi ahankali jikinta na sakewa wani dumi na zagaye jikinta da sarawar Kai.
Tenya tasan ba abune me sauki ba ko kadan hakan kuma qunci ne sabo da zai dasu a zuciyar Ayanah na har abada amma hakan shi kadai ne mafita dan kuwa matiqar zasu yadda ita tayi alkawarin da dubararta zata kawo sauyi da aminci a rayuwar Zuhrah duk da har abada su biyun zasu rasa rayuwarsu kenan ta walwala ko farin ciki dan kuwa zasu tabbata ne a quncin rashin juna suna ji suna gani.
Girgiza Kai Ayanah ta fara yi ahankali da karfi tana fizga kafin sakinah ta riqeta jikinta da karfi tana rungumeta tana Gyada Kai tana hawaye tana cewa
‘Indai Zuhrah zata fito zatayi rayuwa me aminci zaki iya Ayanah,Zaki iya Ayanah….’
‘Bazan iya ba,bazan iyaba shine abinda take fada da karfi tana qwacewa amma dole sakinah ta saka karfi ta riqeta harta gaji dan kanta tayi Laushi.’
Ganin tayi Laushi ya saka sakinah da tenya da kanta suka kamata zuwa toilet inda hadaddun ruwan Zafin wanka ke jiranta suna fidda hayaqi da dan qamshin wani maganin al’ada na wankan haihuwa.
Su biyun ne sukai mata gashin wanka me nutsuwa dukansu jikinsu a sanyaye kaman yanda ita kuma ta koma tamkar batada sauran hankali ko kuzari a jikinta.
Sun dauki lokaci sosai kafin suka fito sakinah ce ta tsaya tayata shiryawa tamkar yanda aka Saba gashinta ta goge mata ta busar dashi ta Kamasa sako sako sbd karya dameta ta dauko mata Kaya tana miqa mata tana sakawa kamar wadda bata gani.
Abinci da lafiyayyar dafaffiyar madarar datasha hadin Kayan qamshin da zafi sosai aka kawo mata tenya da sakinah ne suka tirsasata taci aka kwantar da ita take bacci me nauyi ya dauketa sbd akwai maganin bacci a cikin madarar.
NUAB ma sabon wanka da shiri tenya tayi masa da kanta sbd bata yadda da kowaba Akan Ayanaah da shi yanzu,
Wuni Ayanah tayi tana bacci sai yamma lis ya farka aka sake hada mata ruwan Zafin da aka kuma gasata da kyau ta shirya ta zauna a daki ita kadai sakinah ta saka mata NUAB a hannunta San shayar dashi,
A lokacin data masa shayarwar farko Jin tayi wani abu ya ratsata Wanda ya sakata kafesa da idanunwata da suka qanqance sbd kukan baqin cikin rayuwarta da baya qarewa,
Addua ta bude bakinta a sanyaye ta fara jero masa tana fatar rayuwarsa ta haskaka hasken da zai haskaka rayuwar duk wainda basada gata ko yanci a rayuwar nan.
Dan qanqamesa tayi ahankali da hannuwanta tanajin tamkar ruhinta yana zame wa yabar jikinta na rabuwa da zatai da Zuhrah wannan Karan da gaske kenan har abada sbd hakan shine kadai zai bawa kowannensu rayuwar da ba ita suka so ba,
Indai Zuhrah zata rayu ta samu kwanciyan hankali nutsuwa da walwala tabbas zata zabi rayuwa da gurbin da babu me cikesa idan ba Zuhrah din ba har abada,zata zabi rayuwa babu digon farin ciki bare walwala har abada indai Akan samun rayuwar Zuhrah ne dan haka a yanzu NUAB ne kadai jininta dayake rage mata a rayuwanta da batada komai sai qunci a cikinta,
NUAB shine gata,rayuwa,ruhi,zuciya da hasken idaniyar daya rage mata Wanda kuma zata ci gaba da rayuwa sbd shi.
Da wannan tinanin da quncin ta kwana da ‘danta a jikinta datake Jin tsananin sonsa fiyeda rubabbiyar rayuwarta.
Washe gari haka akaita hidima a masarautar ta farin ciki da murnar jarumai biyu da aka samu,
A bangaren Haile kuwa kwance take rigis hawan jini da ciwon zuciya yana mata karfi dole aka aika mata kwararrin likitocin da zasu tsayu a lafiyarta,
Tenya kuwa sosai ta sake kafewa Akan kiyaye komai na bangaren ayanah sbd abubuwan daya fara gani.
******* babban bangare daya dayake komai iri daya dana HAILE da MARAKI a