goge jikknta harta gama ta shirya ta nufi lafiyayyan gadonta na sarauta ta haye.
Washe gari ma haka suka wuni gurin Abaas tareda iyayensu Wanda kwata kwata GHAZ ayau din bai fita koina ba yana cikin yayansa tausayin Abaas haka kawai yake shige masa zuciya sbd ganin kaman zuciyarsa tayi sanyin da bazai iya mulki ba idan ma yayi wahala zaisha sosai,
Akan ‘yayansa mata ya maida idanuwansa yana kallan yanda suke dariya suna Wasagu da juna sautin dariyarsu na shiga kunnuwansa zuciyarsa na na cikewa da tsananin kaunarsu yanajin kaman ya maidasu cikin Mahaifiyarsu sbd basu tsaro da kariya daga dukkanin wata cutar duniya da wahala.
Akan Ayanah ya tsayar da idanuwansa dariyarta na a bayyanarda asalin zallan Kyan da Allah yayi mata Wanda yasa Sam baa barinta fita daga GHAZ din itama,
Ayanah nada zuciya me sanyi da hakuri tareda juriya tareda jajircewa Akan ‘yan uwanta Wanda yasa yakejin kannenta sun dace dan kuwa tamkar uwarsu haka take kulawa dasu,
Akan Zuhrah ya maida idanuwansa yana kallan gashinta dayake sake zube a bayanta Wanda babu namijin da zai kalleta bata fizgi hankalinsa ba dan haka yake killace dukkanin wata al’aurarsu sam baya barin ko yatsar hannuwansu wani na waje na gani sbd a sujjarsa gabaki daya adduar ‘yayansa ne.
Ahankali jikinsa na mutuwa ya daga hannunsa ya miqa akan Zuhrah ya fara tattare gashinta cikin kulawa ya daure mata yana janye mayafinta me ado dayake gefenta ajiye ya rufe gashin nata.
#MAMUH
#GHAZ
#KUSRAH
#BOYEM
#ROYALTY
#BEST LOVE
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
09033181070
5
Dago Kai Zuhrah tayi ta kalli Abaa din tana Dora hannunta akanta ta taba mayafin daya rufe kanta dashi tana zubawa mahaifinta ido ta bude baki zatai magana ya Dora hannunsa daya akan bakinta ya girgiza mata Kai ya bude baki yace
‘Kanki ya kasance koda Yaushe a rufe Zuhrah ghaz’
Gyada kanta tayi batareda ta dauke idanuwanta daga Kansa ba sbd ganin wani irin kallan tsananin kaunar dayake mata.
Tsakiyar kanta ya sumbata yace
‘Albarkar Allah ta tabbata a rayuwanki Zuhrah koda yan uwanki duka’
‘Amin Abaa’ ta fada tana matsowa sosai jikinsa ta zauna.
Nurat ya maida idanuwansa ya kalla wadda take jikinta yayi sanyi sbd itace tafi kowa saurin kamuwa da yanayin da duk ya sauya,
Ta fisu saurin hawaye da zama emotional sbd tanada qawazuci sosai na iyayensu dan haka hannunsa ya miqa mata ta taso daga gefen Abaas ta dawo gefensa ta kallesa idanuwanta na raurau haka kawai.
Wani murmushi me sanyi da kyau ya dake yana Shafa fuskanta ya girgiza mata Kai yace
‘Jarumar ‘yata Nurat bata barin jikinta yayi sanyi a kowane yanayi’
Murmushi ta sake tana Kama hannunsa qamqam tace
‘Abaa ina fatan na kasance hakan daka fada koba yanzu ba’
‘Insha Allah Nurat zaki zama jajirtacciya dakakkiya bazaki taba gazawaba insha Allah’
Maganarsa ta saka Ammansu kallansa tana dan murmushi batareda tace komaiba.
Qarasa fitar da wunin sukai cikin tsananin kaunar dasuke Jin tafi ta koyaushe musamman da mahaifinsu yaketa yabonsu yana kasa dauke kallansa akansu cikeda kauna hakama Amma Jin takeyi tana sake kaunar mijinta sbd yanda ya tarbiyantar da ita da yayansu.
Da daddare Bayan sunyi sallah ishai Abinci da Kayan marmari aka kawo aka Jere musu tareda fitilun wutar ishen flower masu sanyin kamshi da aka kewaye gurin dasu suna basu haske tareda kamshi.
Dagowa GHAZ yayi ya kalli sakina baiwar Ayanah dake gefensa ya bude baki yace
‘Ina Asamah gabaki daya yau ban ganta ba’
Sunkuyar da Kai sakina tayi cikin girmamawa ta bude baki tace
‘Tin jiya bata fito ba babu Wanda ya ganta a yau sbd damuwan abinda ya faru da GHAZ Abaas’
Kallan Amma GHAZ yayi yana Neman qarin bayanin hakan
Kallansa tayi itama cikin kwantar masa da hankali tace
‘Tashiga damuwa sosai ne har dare jiya tana gurina tana kukan Neman Gafara da Afuwan abinda ya faru dan hakanne yau Kowa ya kyaleta ta dawo daidai’
Shiru yayi sbd bayason nuna damuwa ko fada a cikin iyalansa dan haka baice komaiba sbd duk tsawon shekarun nan bai taba dauke saka Idonsa da saka taka tsantsan sosai akan Asamah ba dan haka tin jiyan da jinin Abaas ya fita yake Jin rashin nutsuwa amma baya iya nunawa sbd yanzu suna cikin wani hali ne na kusrawa dake Neman kawo musu hari kowane lokaci suka samu damar hakan.
Abinci suka ci suna fira da nishadinsu har suka gama nanma suka ci gaba da firarsu har dare sosai kafin Abaa da Kansa ya raka kowacensu dakinta da Kansa kafin ya dawo ya tafi da Amma dakinsu itama tukuna ya fito ya dawo dakin Abaas sosai kafin ya fito ya shige shima.
Tsakiyar dare sosai Nurat dake kwance taba bacci cikin kwanciyan hankali da nutsuwa ta farka da karfi cikin mummunan faduwan gaba sbd mummunan mafarkin datai.
Bude idanuwanta tayi ahankali tana sauke ajiyan zuciya a sanyaye kafin ta tashi Z