NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 87 of 146

nne zaku dinga ganin kayana da zarar na d'ora, ngd sosai taku maman yusuf likitar mata. ************ Tenya data kasa yadda da fahimtar zancen komai a kwakwalwanta Wani irin tsoro da firgici taji tana shiga sbd abinda taji wani gagarumin sabo ma ne da zai iya daukan rayukan mutane da dama a ciki harda su dukan da ita da kunnuwanta suka Ji,rai daya ne zai tsira a cikinsu shine babyn dayake hannunta amma Bayan shi wannan mummunan masifar da kunnuwanta suka ji mata hukuncinta Kai tsaye shine sauke kan kowane me rai daga kafadarsa dayake bangaren AYANAH GHAZ gabaki dayansu sai ita da kila matsayinta na wishmah dazai ceta rayuwarta ta fita a lissafi, Idan bata manta Zuhrah Ghaz ba itace wadda ko ita ta tambaya alaqar sunan daya zo iri daya suka sake bata tabbacin ba alaqar komai ta jini sai sunan gari daya, Zuhrah itace wadda ta raunana kanta taso daukan rayuwarta Akan zama imebēti, Zuhrah itace wadda aka yankewa hukuncin qarasa rayuwa a gidan yari har abada, Wannan zuhrahn itace wadda kunnuwanta ke Jin cewa uwa daya uba daya take da wishmah, Jini daya ne yake gudana a jininsu? Jinin mahaifiyar LEUL ne yake yawo a jikinta itama, Kanwar mahaifiyar LEUL kenan?? Wani irin mummunan zufa mai Zafin gaske ne ya gangaro mata ta qaraso tsakiyar dakin kafafunta a sanyaye batada karfin jiki ko kadan idanuwanta na sauyawa jajir dan shikenan ta shiga masifar da batasan Yaushe suka qulla abar su ba, Dagowa tayi ta kalli Sakinah da duka jikinta ke tsananin rawa da fizga idonta jajir hawaye ma sun qafe mata sbd tashin hankali tana kallan tenya din da tinani Kala Kala a ranta na yanda tenya zata dauka lamarin nan me girma, Dawo da idanuwanta tayi Akan Ayanah da bata damu da rasa rayuwarta da zatai ba kuka takeyi sosai mara sauti sbd zata rasa ranta ne batareda ta ceto yar uwarta ba zata tafi ta barta a qangin bautar da kila zatai har qarshen rayuwarta. Kukan Ayanah dake saka har jikinta jijjiga ahankali ya saka tenya kasa cewa komai saima miqa mata NUAB a hankali jikinta a sanyaye yana dan rawar tashin hankali itama dan kuwa ita datake masarautar tafi su sanin girman tsantsar hadarin abinda suka aikatawa masarautar. A hannuwan Ayanah din ta Dora NUAB daka motsa ahankali cikin showel dinsa ita kuwa Ayanah tsayawa kukanta yayi cak jinsa a cikin hannuwanta ta bude idanuwanta da sukai jajir akansa ta zuba masa ido tana kallan fuskarsa me kyau da daukan Idon da babu abinda ya Bari a cikin kamanninta se gurbin mahaifinsa daya dauko, Kammanin duka yan uwanta dasuke Kama guda daya da ita da mahaifinsu ya dauko tinda komai nata irin na yan uwanta ne musamman Nurat da Abaas sunfi Kama sabanin Zuhrah da Ammansu tafi Kama da ita dan haka fuskokin yan uwanta da mahaifinta take gani suna yi mata yawo a fuskarsa zuciyarta na Wani irin shiga radadin rashinsu a tareda da ita Ayau data haifar musu ‘dan kanta, Wasu hawaye masu radadi da sanyi ne suka gangaro mata ahankali suka sauka Akan gefen fuskarsa ta rufe ido tana sake fasa sabon kuka Mara sauti tana dagosa jikinta ta saka a kirjinta ta rungume tsananin radadin rashin Abaas na dawo mata sabo a zuci da ruhi sbd shine Wanda a duniya yafi kowa fata da son ganin wannan rayuwar a rayuwarsa wato ranar da zata haifar masa ‘dan zai dauka ya rungume a matsayin nata sbd irin tsananin son dayake mata, A koyaushe ya aurar da ita ta Haifa zuriar da zata hadu da tasa shine adduarsa da fata da burinsa tin yanada qananun shekaru gashi Ayau Allah ya raba rayuwarsu da basusan ko iyaka cin rayuwar da zasuyi kenanba, Tsima zuciyarta kukanta keyi ta sake qanqame NUAB kirjinta tana adduar ‘Ya Allah kada ya dauki ranta sai ta hadu da ‘dan uwanta rabin jikinta hasken idaniyarta Abaas, Ya Allah kada ya dauki ran Abaas batareda burinsa ya cika ba na ganin zuriarta data haifa a duniya.’ Sakinah dataji adduar da Ayanah ke yi a bayyane zubewa tayi qasa kan gwiwoyinta tana fidda hawaye masu tsananin Sosa zuciya itama tana sunkuyar da kanta qasa tana Jin radadin rashin Abaas din itama yana dawo mata sabo tareda wargajewan ahalin GHAZ din da basuda burin daya wuce ganin wannan rana ta ganin jinin da Ayanah zata haifa dan Bayan Abaas Nurat ce me tsananin son ganin jinin Ayanah na farko sbd tace itace zata zama uwarsa duniya da lahira Ashe itama bazata gani ba tabar duniyar gabaki daya a cikin Hali mafi muni da har su mutu bazasu dena tinawa ba., Irin kukan da Ayanah ke yi tana sake qanqame ‘danta da yanda ke buga kanta a qasa itama tana yi da sauti me kashe jiki da tsima zuciya ya saka tenya jikinta mutuwa tsoronta da fargabanta na komawa tausayi da fatar rage radadin dayake zukatansu da babu komai a cikin rayuwarsu tin farko da kunci da damuwan da bata taba ganin ta gushe daga idanuwa da zukatansu ba. Tsawon lokaci suka dauka suna kukan qunci da ciwon rayuwarsu daya dawo musu sabo kafin sakinah ta rarrafo ahankali batareda ta dago ba kanta a qasa ta miqa hannuwanta biyu ta Dora a kafafun tenya dake tsaye a kansu ta rintse idonta dake jajir hawaye masu dumi suka g
🏠