NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 85 of 146

da girma sosai suka hada Baki suna cewa ‘Allah ya qara maka tsawon rai da lafiya tareda iko ya Abbi me BOYEM muma muna son Ayi adalci ga kowa a bawa me matsayi matsayinsa’ Tsit fadar ta dauka sbd wani girmammen lamari daya ratsa, Manyan fada kuwa kowa maganarta ta shige sa sbd abinda ta fada haka yake babu gargada babu shakka, Haile data ga maganarta ta shiga manyan fada wani Numfashi me sanyi da rashin sauti tana Jin sassaucin muguwar azabar datake ji a kirjinta na zallar baqin ciki da tashin hankali hakama abinda ya sa ta zabi maganar anan gaban manyan fada sbd sunada iko me karfi ta wannan bangaren da duk zai shafi goben Masarauta da ikonta da kaidojinta dan haka tasan dole ya yanzu basai gaba ba zaa bawa danta magajin sultan tasan shine tin yanzu me jiran gado. Sultan idanuwansa ya zubawa HAILE yana ankarewa da abinda tayi din na zuwa fada ta fada adalci take nema wa ‘danta, Bai taba tinanin zaa fara samun jayayyar matsayin magaji ba da wuri hakan Wanda fara faruwan hakan na nuni ne da zazzafan hadarin da zai biyo Bayan rayuwar mutane da yawa Akan matsayin da rayuwar magajin BOYEM koma wanenen, Masana sun sanar da duk magadan suka fara jayayyar matsayi a masarautar BOYEM fitina ce da zazzafan hadari yake tafe a cikin Neman mulkin kota yaya dan haka take yaji wani yanayi na tinanin taka tsantsan yabi komai a natse da lissafi dan bada kariya ga Wanda yasan zasu cutu a yaqin mulkin amma ita HAILE a bayyane ya gane me takeson yi na Neman matsayin wa danta ta hanyar ikon manyan fada wainda zasu iya yanke hukuncin waye magajin BOYEM, Juyar da idanuwansa yayi ga tenya Wadda idanuwanta suke a qasa amma irin riqon datai wa NUAB ba Wanda zata iya shiru bane a bakin rai take da tsayuwa Akan lamarinsa dana uwarsa da batada kowa a duniya tinda baiwa ce da aka saka kudi aka siyo. Numfashi mai nuna isa da iko ya sauke yana komawa sultan dinsa dan tabbatarda girman matsayin da tenya zata iya zuwa Akan Ayanah ghaz da ‘danta ya bude Baki batareda ya kallo kowa ba idonsa Akan ASIM yace ‘Tabbas Li’ul ASIM ALMAZ BOYEM ‘dan queen Haile Wanda……. Da karfin gaske cikin tsananin girmamawa tareda gitta rayuwarta tenya tayi saurin daga NUAB tace ‘Allah ya qara maka daraja me BOYEM ina Neman gafarar sauke kalaman da ake nemarwa Magaji na biyu adalci sbd a yanda tarihi da dokar Masarauta me karfi ta tabbatar shine matsayin Matar dake dauke da igigoyin auren sultan takeda shi to dukkanin wannan cikakken matsayin da iko wishmah tana dauke dashi hakama a doka mai kakkaifan karfi ta Masarauta idan har wishmah ce ta haihu ba imebeti ba to tabbas ‘danta nada cikakken iko da matsayin da ‘dan matar sunnah take dashi…… Cikin murya me amsa Amon mulki da iko HAAT(wazirin Sultan da shine mai riqon qasa idan sultan baya nan kuma sune masu hukunci yace ‘Ki bude bayaninki Kai tsaye Maleketenya dan kuwa cikakken bayani zai qaddamar da waye zai yi riqon magaji a cikinsu’ Da gwiwowinta ta juyo bangaren da Haat din yake ta sauke kanta qasa cikin tabbatarda son karban matsayin NUAB daga hannun kowa tace ‘Da daaham din shedar zamowanta cikakkiyar wishmah imebēti AYANAH GHAZ ta fara naqudar magaji na daya dake hannuna a yanzu Wanda hakan ya tabbatarda babu kowane iko ko jinin dayake yawo jikin mai girma ASIM dayafi na LEUL mai jiran boyem, Zamtowan mahaifiyarsa wishmah kafin ta diresa a duniya ya wanke tareda tsaftace masa kowace irin hanya data Halasta masa cikakken ikon BOYEM gabaki dayanta da zagayenta…..’ Tsit fadar ta kuma dauka mai karfin gaske wadda ta saka HAILE fara jiqe wa da wani mummunan zufan daya daga jininta ya fara hayewa take dan kuwa ta manta da Ayanah ghaz ta zama wishmah kafin fara naqudarta Wanda tabbas hakan ya halastawa ‘dan ta komai. Saukar idanuwan sultan Akan tenya yayi mata kallo daya ya maida kallansa kan haat Wanda take ya karbi NUAB daga hannun tenya ya nunosa gabansa ya ambacesa da magajin sultan YASAR ALMAZ BOYEM, Matiqar sultan yana raye shine yakeda ikon hawa mulkin BOYEM sbd ‘dan kwarkwara ce ta haifeka bakada cikakken gado dan haka idan sultan ya rasu kafin saukarsa mulki bai doraka ba to tabbas bazaka hau karagar mulki ba. Da sanin wannan sharadin ne wani mafi girman burin Dora NUAB ALMAZ Akan kujeran mulkin BOYEM ya tsiru a zuciyar sultan YASAR sbd zamowan ‘danta Akan mulkin BOYEM ko baya raye zata kasance macen datafi kowace mace power da tsaro a boyem. Tenya cikin tsananin farin cikin gaske ta ringa zuba godiyarta ta miqe ta fice dan Kai NUAB ga mahaifiyarsa da kuma yi masa wankan al’adah da baayi masa ba. ******a daidai wannan lokacin Ayanah ce riqe da hannun sakinah gam suka riqe juna sbd kukan da Ayanah keyi zuciyarta kaman zata Dena bugawa sbd tsabar gajiya da baqin ciki da damuwan da itace take yawo a kowane gaba na jini da jikinta, Duk Wanda yake masarautar ko a wane lungu me nisa kake labarin haihuwan magajin BOYEM ya isar maka tareda sunan wadda ta haifesa dan haka babu shakka tasan zuhranta taji
🏠