NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 83 of 146

haihuwan magajin sa daga Haile datake matarsa ba imebeti ba dan kuwa a tsatsaurar dokar boyem matiqar akwai ‘da namiji daga Mata to ‘dan imebeti bazai taba zama magaji ba dan haka da confidence mai girma ta tinkaro tsakiyar fadar dauke da farin showel itama a hannunta babyn dake ciki na kwance A ciki yana bacci hankali kwance. Tenya kafe idanuwanta tayi a hannun fetto din zuciyarta na dan bugawa da tinani masu tsauri da girma Kala kala sbd idan idanunwata suna gani daidai baby ne a hannun fetto din Wanda da alama shima baa jima da haihuwansa ba, Gabaki daya wainda ke fadar tsaida idanuwansu Akan hannun fetto sukai cikeda mamaki da shiga tinanin ko yan biyu Ayanah ta haifa Sai yanzu Dayan ya fito to amma ganin jakadiyar HAILE kuma sako daga bangaren Haile akace ya saka kowa aje tinanin yan biyu aka haifa. Fetto na isowa tsakiyar fadar me girman gaske zubewa qasa tayi ahankali kanta na qasa ta daga babyn cikeda kulawa da girmamawa me girma tafara zubo masa kirari kafin daga karshe ta sanar dashi queen HAILE ta sauka awa daya da mintina arbain da tara da suka wuce Wanda sakamakon cikin datake Reno ne ya sakata karban hutun zuwa tiraka kuma tayi hakan ne sbd kebe kanta ta samu jinya da Renan ciki mai nutsuwa kuma a cikin yardar Allah ta haifo asalin magajin boyem. Da tsananin mamakin daya dakatar da komai kowa ke kallan hannun fetto din shock na kama kowa, Tenya ma wani irin dum taji kunnuwanta sunyi ta rungume LEUL da karfi kirjinta tana kasa dauke idanuwanta Akan hannuwan fetto zuciyarta na nauyi da tsananin mamaki da tashin hankalin maganar fetto din kafin ta maida idanunwata Akan sultan YASAR da shima shiru Yayi idanunwansa Akan fetto tsawon seconds kafin ya maida idanuwansa Akan babyn hannun nata ya kallesa yana mamaki mai tsananin daya dan bayyana. Tsit koina da kowa yayi Ana rasa abin fada sbd magana dai a Kai tsaye take babu wani kwana kwana kowa ya fahimci komai da fetto ta fada babu abinda kowa zaice bai ji daidai ba kokuma Neman karin bayani akai Kai tsaye itama HAILE magaji ta haifarwa Masarauta. Sultan da yayi shiru yana kallan babyn kawai suke jiran bayani daga garesa Wanda shima kai tsaye yaji komai daidai ba buqatan kowace tambaya Akan qarin bayanin komai, Mintina aka share kafin sultan ya sauke Numfashi me sanyi tareda dauke ajiyan zuciya mata sauti zuciyarsa na ratsuwa da wani sabon farin cikin samun wani hasken idanuyar da baima San dashi ba dan haka hannuwansa ya miqa a natse cikeda kulawa da soyayya mai karfi ta uba ga ‘dansa ya amshesa tareda rungumesa a jikinsa na mintina shima yana masa addua kafin yayi nasa huduba ya daga sa sama ya ambacesa da, ‘LI’ULI ASIM YASAR ALMAZZ BOYEM’ (prince Asim yasar almazz boyem) Take kowa ya maimaita sunan suna saka masa albarka tareda addua duk da baaji shauqin na ratsa jini da kwakwalwaba kaman farkon amma shima sunyi Murna sosai da kasancewansa sabon prince din boyem hakama yau rana ce mafi girma da tarihi tinda aka haifar musu jaruman babys biyu a daya rana. Kyauta da tukuici aka fara fiddawa Ana bawa fetto itama sedai kasancewan baa San da haihuwan ba bata samu kyauta irin wadda tenya ta samu ba sultan kuwa kyautarsa da tukuicin sa daidai iri daya yayi da wadda yayiwa NU’AB, Cikin karfin Hali da dake wani zuciya fetto ta karbi ASIM tareda dagasa tayi masa kikarin daya saka kowa yin tsit dan kuwa Kai tsaye da asalin magajin sarki ta kirasa bayan sultan ya riga ya Ambaci NUAB da magajin BOYEM. Dagowa sultan yayi da fararen idanuwansa da sukai wani haske da kwarjini sbd yanayin dayake ciki a yau din zai kalli fetto sbd lokacin data fada cewan an haifi ASIM ALMAZZ tabbas kenan ya riga NUAB fadowa duniya sedai kuma NUAB ne Wanda ya fara shiga hannuwansa, NUAB ne Wanda ya fara cike zuciyarsa da yanayin dabai taba shiga ba na samun magaji, NUAB ne Wanda labarin haihuwansa ya fara ratsa kunnuwansa da kunnuwan duk Wanda yake BOYEM da zagayenta, NUAB shine Wanda ya fara dagawa duniya ya ambacesa da LEUL BOYEM….. Ganin tinanin da sultan yayi shiga Akan tsakanin ‘yaya biyun waye magajin gasken ya tenya zubewa qasa da Wani irin saurin gaske tana daga NUAB da ladabin gaske ta bude Baki tace ‘Allah ya qarawa jini da ruhinka tsarki sultan me BOYEM uban LEUL BOYEM,uban magajin BOYEM,uban NUAB ALMAZZ Zakin boyem, Ayau magajinka daya ne da duniya zata sani wato Wanda ya fara haskaka zuciyarka da hasken da aka dade Ana jira, Li’ul ASIM zakinmu ne shima da babu tamkar sa, Shi din haske ne dazai haske masarautarmu da Zuwan LEUL NUAB ya fara haska mana, Jini daya ne yake gudana a jikinsu biyun Wanda yake asalin jinin boyem me tsarki da karfin iko da adalci, A tarihin boyem mai daraja data kafu Wanda ina saka ran jakadiya fetto ta manta dashi shine…….. Kaman daga sama aka rangado sanarwar isowan Queen Haile da kanta. Gabaki daya duk namijin dayake fatar qasa yayi da idanunwansa cikeda girmamawa da bin al’adar Qin sauke ido ga mace me daraja a BOYEM wato uwargidan sultan YASAR BOYEM.
🏠