ace ta ratsa kunnuwansu cikin sanyi da rikitaccen yanayin daya saka dukkaninsu Sakinta cikin mugun firgita da ficewa hayyacin dan kuwa sautine dayake fadawa BOYEM da duniya gabaki daya MAGAJI kuma ZAKIN BOYEM ya sauka a duniya tsohuwar imebeti sabuwar wishmah AYANAH GHAZ ta haifosa.
Shigar sautin kunnuwan Sultan YASAR da gabaki daya manyan masarautar boyem a lokaci daya suka zube qasa suna yiwa Allah sujjada batareda ma sun sani ba,
Haile kuwa Numfashi daya ta fitar bugun zuciyarta ya tsaya cak sakamakon sautin sakon daya ratsa kunnuwanta ya Harba cikin kwakwalwanta ta zube a gurin jaririn hannunta yana subucewa daga hannunta zuwa qasa,
Cikin wata gaggawa da tashin hankalin dayake Ninkuwa Akan mugun shock din dasuke ciki fetto ta tare babyn koina na jikinta na rawa da kakkarwa,
‘Yarta Aslam ce tayi saurin tarota jikinta itama jikin nata yana rawa sosai da firgici tareda tsananin tsoro sukai qasa har ita har mahaifiyar tata sbd batada karfin da zata iya riqeta tinda jikinta a sake yake kaman babu rai a jikinta,
Dr Kadee ce tayi saurin bin Aslam din qasa tana tayata riqe Hailen itama jikinta rawa yakeyi da firgicin yanda duk wahala da azabar da suka sha ta tashi a iska labarin haihuwan Ayanaah ghaz ya fara shiga kunnuwan sultan YASAR da qasar BOYEM harma da duniya gabaki daya.
Fetto babyn ta rungume jikinta tareda budesa sa sauri taba duba idan yana raye babu abinda ya samesa daga faduwar taga lafiyarsa kalau sedai tinda aka haifesa baya wani kuka saida ya fadin ya fasa kuka sosai Wanda ya sakasu sauke ajiyan zuciya suna tattalar HAILE din dan maidata shimfida a bata taimakon gaggawa.
***A daidai wannan lokacin kuma sautin qarar ya ratsa kunnuwan Zuhrah dake Zaune daqyar sbd azaba da rashin lafiyar da kowace gabar jikinta keyi a cikin wani irin kurkuku mara Kyan gani,
Tinda aka sanar da Masarautar kaf cewa imebeti AYANAH GHAZ na naquda ta tashi Zaunen idanuwanta dake ciwo basa gani sosai ta bude su tareda daga Kai sama ta qurawa sama ido tafara jerowa Ayanah da abinda zata haifa addua jikinta na rawa tana fadawa Allah adduarta Akan yar uwarta
Bata Dena addua da fadawa Allah ya tsayu Akan rayuwar babyn ayanah dinta ba har saida sautin ya ratsa kunnuwanta Wanda ya sakata rufe idanuwanta ahankali tana silalewa qasa kwance tareda fashewa da Wani irin kuka mai ratsa zuciya tana gode wa Allah da bai karbi ran ayanarta gurin haihuwa hakama wata irin tsananin kewarta da kaunar son ganinta a lokacin ta saka sabbin hawaye gangaro mat a tana Jin tsananin so da ganin abinda Ayanah ta haifa musu ta rungumesa a jikinta taji duminsa tareda sakawa rayuwarsa albarka da fada masa sun yafe masa ita da ‘yan uwanta da basa raye sbd kaddarar haihuwansa a jinin BOYEM ce ta lalata tasu rayuwar da babu gyara a cikinta har abada.
Rufe idanunwata tayi hawayen data manta rabon datai yi su sbd kuka ma kansa ya gujeta sai Ayau din datake Jin kewa da tsananin son Ayanah da ‘danta suna ratsata.
****A kuma wannan lokacin ne sultan YASAR ya dago daga sujjadarsa ya daga hannu sama yayiwa Allah godia yana jerowa dan nasa addua me tsananin karfi,
Danyen zinari aka fara fitowa dashi a tray mai shegen kyau aka fara kyautarsa a matsayin tukuici hakama duka manyan dake cikin farin ciki mai tsanani da annashuwa suka fara gabatar da tukuici ga AYANAH GHAZ da kyautar data ringa girgiza mutane da tabbatarda Ayau burin qasar BOYEM ya cika na shekaru,
Ko da tenya ta fito daga babban kofar fitowa bangaren Wishmah gabaki daya wasu irin securities ne da bayin da zasu rakata har zuwa fada Sbd Mai BOYEM dayake hannunta.
Gabaki daya Wani irin Juyawa tenya taji kanta na yi sbd tarin bayi da securities da suka cika hanyar dan kawai rakiyar Magajin BOYEM ga mahaifinsa.
Kafafunta sanyi sukeyi mata a duk lokacinda tayi Taku daya na tafiya zuwa fadar mai girma sultan YASAR dauke da jaririn dayafi kowane ‘da daraja a qasar BOYEM yana dunqule cikin farin lallausan bargon daya babu hannun Wanda ya shiga duniya Bayan nata saiya shiga hannun mahaifinsa kafin ma ya shiga hannun mahaifiyar data haifesa,
Kai tsaye hanyar fada suka isa babyn na rungume a jikin Tenya data ke Jin sabuwar duniya ce yake kafuwa a BOYEM daga lokacin da ‘dan nan ya gado duniya.
Isowarsu bakin kofar fadar da Wani irin tsit akai tareda wangale mata kofa Sauran securities da bayin suka tsaya daga kofa ta sako kafarta ta dama ta shigo tana Takawa cikin nutsuwa tana nufar karagar mulkin BOYEM da sultan yake Kai idanuwansa masu tsananin kyau da kwarjini suna kan hannuwanta biyu dake rungume da hasken dayake tsaya zuciya da idaniyarsa,
Dukkanin Wanda yake cikin makekiyar fadar da Taku ne me yawa kafin Ka isa karagar daga bakin kofa kowa idanuwansa Akan hannun tenya yake suna fidda silallan zinari a gabansu suna ajiye wa qasa inda duk tenya ta taka ta wuce matsayin tukuici gareta ita kanta Wanda hakan ke saka kafafun tenya rawa da farin cikin datake Jin kaman zata some tin daga lokacin da magaji ya shiga hannunta.
Ko data isa gaban sultan YA