NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 8 of 146

an mijinta gareta Wanda zuwa yanzu tasan azaba ta dade da sauyasa zuwa wata mummunan halittar amma tanason abinda a hakan. Shedan da zuciyarta dake rufewa idan abin ya taso mata Wanda yake tamkar tabin kwakwalwa batareda sanin kowaba suka saka zuciyarta rufewa tafara taku daya na biyun ta saki gabaki daya Kayan hannunta a jikin Abaas Wanda wuqar ta yanki gefen qafarsa take jini ya fara fito wa Wanda ya saka dukkaninsu miqewa cikin tsananin tashin hankali da damuwa Asamah ma cikin tashin hankalin da tsoro me tsanani ta zube gabansa tareda rigan kowa saka hannunta a kafarsa tana wani irin rawar jiki da kukan dayake fito wa daga qasan ranta tana basa hakuri cikin kulawa sbd a qasan ranta tasan kofar wata rayuwar ce zata bude wa duk Wanda yake garin ANJOM wadda bata San wace iri bace dan kuwa a gefen rigar jikinta ta goga jinin me yawa daga qafar Abaas batareda lurar kowa ba. Cikin sauri sakon fitar jini a jikin GHAZ Abaas ya isarwa Abaa dinsu wanda ba bata lokaci ya iso gurin Wanda ya saka duk Sauran bayin dake zagaye da gurin na kowannensu dake rumfar ja baya sosai cikin girmamawa. Wuqar da jininsa ya taba ya fara bada umarnin a karba hakama take aka kawo ruwa masu yawa a babbar tasa me kyau aka saka Asamah wanke duka hannuwanta da jinin Abaas ya taba kafin take GHAZ Ali din da Kansa yasa aka kawo magani ya karba yana kallan Abaas din Wanda hankalinsa yake son tashi sbd fitar jininsu tamkar hadari ne ga dukkanin ANJOM gabaki daya sbd da jininsu ne kadai ake iya karya komai dake ANJOM dan haka Sam baa taba yadda da kowa ba game da duk wani digon jinin GHAZ. Amma ganin Asamah ce ta raunanasa bada ganganba kuma tamkar ahali take sai hakan na hana zuciyarsa shiga tashin hankali da tsoro sosai. Kukan da Asamah ke yi ya saka Ayanah rarrashinta tareda Zuhrah Nurat da Amma kuwa suna jikin Abaas din cikeda damuwa suna kallan yanda GHAZ ya saka masa garin maganin da take jininsa ya tsaya ya Dena zuba. Ajiyan zuciya GHAZ ya sauke yana dagowa ya kalli Abaas din cikeda kulawa da qara tabbatar masa da tsananin mahimmancin jinin dayake yawo a jikinsu. Cikin nutsuwar mulkin dayake yawo jikinsa da kulawa tareda tabbatarda kiyayewa GHAZ ya bude baki yace ‘GHAZ Abaas ya koma dakinsa a tabbatarda an kiyaye danyen yankan kafarsa ta warke da kyau batareda ya sake fitowa ba’ Gyada Kai kowa yayi suna amsa wa da cewa ‘Angama’ Juya wa yayi ya bar gurin kowa yayi tsit cikeda damuwa da alhini har saida ya fice kwata kwata kafin Abaas din ya dago ya kalli Asamah kaman zai yi magana sai bai ce komaiba ya maida idanuwansa Akan Ammansa dake miqewa tabar gurin tana bin Bayan GHAZ Ayanah kuma hannu ta miqa masa ya Kama ya miqe suka nufi hanyar dakinsa tana cewa ‘Yankan qaramar wuqar cin tufa bazata girgiza jarumin anjom ba GHAZ din anjom me zuwa’ Yar dariya yayi yana kallan kafar tasa tareda cewa ‘Shekarun nawa basu Kai ba ai tukuna amma insha Allah idan nakai shekaru ashirin a duniya zan fara fita a matsayin jarumin na anjom wata ran harma na zama Garkuwa ga dukkaninku’ Har cikin ranta taji dadin abinda ya fada tana fatan hakan koda kuwa a mafarki ne. Rakasa tayi dakinsa Wanda acan suka zauna ta tayasa fira sai ga su Zuhrah da Nurat sun taho suma sbd sunsan saiya kwana biyu kafin ya fito koina sbd tsaro da dokar GHAZ din tin asali duk Wanda yake jinin GHAZ yaji rauni har jininsa ya fita to saiya kwana biyu a killace batareda fito wa koina ba sai Raunin ya qame, Hakan ne ya saka yan uwansa zuwa dan tayasa fira da debe kewa, Kayan ciye ciye da dafaffiyar madarar raqumi me dumi aka kawo aka ajiya musu sunata firarsu da hutawarsu cikin kwanciyan hankali da nishadin farin cikin kansacewa da juna, Anan suka wuni dan hatta ibadarsu anan sukayita, Da yamma ma mahaifinsu shigowa yayi cikinsu cikeda Shakuwa da kaunar juna suka cigaba da farin cikinsu anan cikinsu yayi sallah tareda iyalansa har cikin dare tukuna dukkaninsu suka watse kowa ya nufi makwancinsa. Ayanah na isa dakinta zare Kayan jikinta tayi ahankali tana rufe jikinta duka ruf da wata kakkaurar doguwar rigar wanka me Kama da alkyabba amma ita ta yadin saka me kyau. Baiwarta Sakina ce take biye da ita dauke da wutar haskawa. Gurin wankansu ta Nufa Wanda yake cike da ruwa masu tsafta da kullum ake sauyawa ta zare rigar tana zaunawa gaban ruwan tafara wanka a natse. Sakina ajiye mata hasken tayi ta koma kofa ta tsaya daga waje tana jiran fitowarta. Gama wankan tayi ta fito tana qamshin madarar flower me dadi. Dakinta ta shiga ta zauna Sakina tana tayata
🏠