nensu yake hada zufa suna Kai da kawon taimaka mata gurin samun sassaucin abinda take ji,
Zufan fuskarta zuwa wuyanta ake goge mata da tsaftataccen farin towel qarami suna Jera mata Sannu da kokarin ganin ta haihu lafiya, magani kuwa haka ake kawo mata shi tana sha tana dawo da wani sbd tafara Nisan da bata iya Shan komai amma a zuciyarta ta kasa sake adduar datake yi guda daya tak wato ‘Allah ya bata ‘da namiji koma yayane kuma Allah yasa itace zata fara haihuwa’
Wannan adduar take ta maimaitawa tana kasa sakewa dan tabbacin datake dashi na Allah yana karban adduar me naquda dan haka har a tafara ficewa hayyacinta bata roqarwa kanta ko ‘yayanta komai sai wannan adduar gida biyu.
****A daidai wannan lokacin naquda sosai AYANAH GHAZ takeyi me tsanani itama Wanda ya saka itama nata bangaren da bangaren imebētis din kaf yin tsit babu ko abu daya dayake bada sauti sbd Masarautar wannan Karan tafi kowane karo yin tsit dan kuwa mamaki biyu ne yake ci da kashe kowa amma b damar magana a yanzu wato shine Wishmah data tabbata Bayan qarnika da kuma haihuwar da baa San da cikinba kuma a hakan taci gaba da zuwa shimfidar sultan,
Wannan duka wasu abu ne da suka girgiza masarautar da duk Wanda yake cikinta cikeda tsoro da mamakin dayafi Kama da firgici kowa yake,
Masu rubuta tarihin qasar BOYEM da Masarautar BOYEM kuwa a daidai wannan lokacin suna can sun fara rubuta wa a cikin kundun tarihi,
A cikin fadar sultan ma a inda ake Zaune tsit abu daya kowa ke jira wannan Karan sunfi kowace lokaci daukan tsit sbd Ana magana a tsakaninsu duk zaman jiran da akeyi amma a wannan Karan sultan YASAR babu abinda ya bude baki ya furta hankali da nutsuwar sa kaf suna ga jiran sakon haihuwan Ayanah ghaz dake saka zuciyarsa cika da Wani irin nauyi da yanayi na tsumayi dabai taba shiga b duk haihuwan da ake masa,
Sosai yakejin kowace daqiqa tana wucewa ne da bugu wan zuciyarsa mai karfin Akan haihuwar yau dayake jinta har jini da bargonsa dan haka take duk Wanda yake fadar ya dauke wuta sukai tsit suma suna shiga tsimayin jira da Jin tsananin son labarin haihuwan wishmah ta farko data sauya tarihi da dama na masarautar qasar BOYEM gabaki dayanta dan haka sai sukejin haihuwan ta jinin BOYEM wannan Karan ta daban ce a gurin sultan da wannan dalilin suka ta zama ta musamman din tinda kuwa wishmah ce zata haihu kowa yasan haihuwan soyayya ce bata saurauta ba.
Tenya data kasa ta tsare ko motsawa batai ba daga gaban Ayanah dan kuwa duk inda hannuwan likitoci suka taba a jikinta idonta na Kai sbd tsananin tsaro da rashin yadda da kowa,
Sakinah ma a wannan lokacin tana riqe da hannun Ayanah gamgam suna hada zufan tare tana Jin duk radadin da Ayanah ke ji a zuciyarta tana Jin tsananin matsuwa da son haihuwan Ayanah lafiya tana saka mata addua mai kyau a bakinta,
A bakin Ayanah din addua ce guda biyu rak take fita wato Allah ya zama gatan yan uwanta dasuke raye ya kawo sauyi a rayuwarsu sai kuma adduar Allah ya tsaya Akan kowane irin lamarin babynta da zata Haifa,Allah ya haskaka rayuwarsa ya basa kariya daga duka Sharrin duniya’
Wannan adduar itace take maimaituwa a Baki da zuciyar Ayanah da sakinah harma da tenya da ita iya babyn takewa adduar Allah ya basa kariya har qarshen rayuwa kowannensu a zuci yake adduar.
Sosai azabar tayi mata yawan data fara galabaita tsananin tausayinta na saka zuciyoyinsu sanyaya dan haka suka dage da addua da karfi da imaninsu suna Neman mata sauki a gurin ubangiji,
Sakinah jiqe take shar kaf da zufa tana tsananta adduarta a fili tana share zufan Ayanah suna sake qanqame hannun juna Ayanah na Jin kaman bazata rayuba rayuwarta zata tsaya ne daga nan sbd abinda take ji tabbas shine kowace uwa takeji yayin jeho yaya a duniya idan har ta mutu anan ta tabbatarda tayi shahada dan haka take Jin inama zata mutu anan din ta huta.
Lokuta masu tsayi suka dauka dukansu suna naquda me tsayi da rashin sauki,
Babu wadda bata Kai qarshen jigata ba a cikinsu tareda fita hayyaci,
Duk wainda suke tareda su sun sare sun shiga tsoro da fargaba tsawon wunin da babu komai cikinsa sai jiran azaba,
Karfe shida na yamma a lokacin da baby ya turo kai fitowa jikin HAILE gadan gadan take su fetto suka shirya tsaf ma tarbansa cikin tsananin matsuwa sbd suna sane da har lokacin Ayanah ghaz bata haihu ba dan akwai sautin karar da ake sakewa masarautar ta amsa gaba daya idan an haihu dan haka tinda basu ji komai ba sun San bata haihunba gashi yanzu tasu zata far haihuwa babbar matsalar shine fita a wannan lokacin batareda haihuwan Ayanah ba zuwa isar da sakon haihuwar.
Cikin azababbiyar azaba da Nishin dayake hade da ihu mai karfi Haile ta saki tana qanqame hannuwan yarta da karfin gaske ta sunbulo babyn dayake cikinta ya fado a hannun likitar dake gabanta idanuwan fetto kaman zasu fado qasa sbd jiran ganin abinda aka Haifa,
A daidai wannan lokacin itama Ayanah ta sauke wani kakkarfan nishin daya fito da nata babyn duniya itama Wanda ya fado a hannun tenya Wanda jikinta ya dauki mummu